Dan wasan gaban Newcastle Harvey Barnes ya ji rauni a kafarsa kuma akwai yiwuwar "zai yi watanni ba makonni ba" yana jinya, kamar yadda Kocin Kungiyar Eddie Howe ya bayyana.
Dan wasan, mai shekara 25, ya fita filin wasa yana dingishi a minti na 12 bayan fara wasa a ranar Lahadi, inda Newcastle ta doke Sheffield United da ci 8-0.
Barnes ya koma Newcastle ne daga Leicester a watan Yuli a kan fam miliyan 38, an yi wa dan wasan hoto a kafa kuma yana jiran sakamako, wanda zai nuna ko akwai bukatar a yi masa aiki a kafar.
"Rauni ya samu a kafarsa a kasan babban dan yatsansa. Ina ganin babban rauni ne," in ji Kocin Newcastle.
"Ba na so na yi magana kan raunin sosai saboda ba ni da kwarewa kan haka amma kuma rauni ne irin wanda ba a saba gani ba."
Barnes, wanda ya taka wa Ingila leda sau daya ya yi wa Newcastle wasanni bakwai, kuma ya zura kwallo daya a raga.
Howe wanda kungiyarsa za ta kara da Manchester City a Kofin Carabao a ranar Laraba, ya ce ya karaya bayan wasan "saboda ya san ba rauni ne karami ba da za a yi jinyar mako daya ko biyu ba. Wannan babban abu ne."