Yumbun roba ya tashi  ya zama sananne a tsakanin masu sha'awa. Hoto: Lemlem Hussein

Daga Lemlem Hussien

A 'yan shekarun nan, ana samun cigaba a bangaren amfani da yumbun roba wajen hada kayan kwalliya.

Wannan ci-gaban bai rasa nasaba da annobar COVID-19, lokacin da mutane da dama suka koma fadada kirkira da fasasarsu domin rage damuwa da amfani da dan rage lokaci da kuma mayar da abubuwan da suke kauna zuwa hanyoyin samun kudi.

Amfani da yumbun roba ya fara samun karbuwa ne a tsakanin masu fasaha, saboda yadda kafofin sadarwa suka taimaka wajen baje-kolin fasahar da kuma sayar da kayayyakin.

Kayayyakin suna samun karbuwa ne saboda karkonsu da sauki da rashin nauyi, wanda hakan ya sa masu hadawa suke ta kafa ninkaya a sabon fagen na kirkire-kirkire.

Me ake nufi da yumbun roba?

Wasu kayayyakin ado ne da ake hadawa da yumbun da aka sana'anta daga sinadarin polymer polyvinyl chloride (PVC). Irin wannan yumbun, za a iya sarrafa shi yadda ake so, a dafa shi sannan a hada duk abin da ake so.

Idan na ce za a iya hada komai, ina nufin duk wani kayan ado na da ake sakawa a jiki irin marjani da sarkoki da sauransu da kuma sassake irin mutum -mutumi da gilasai da fenti da sauran kayayyakin ado da sauran abubuwa masu yawan gaske.

Asali, ba a cika damuwa da fasahar yumbun na roba ba, inda sai da ya dauki gomman shekaru kafin aka fara mayar da hankali zuwa kansu.

Nau'in yumbun nan na zuwa a kala daban-daban. Ba sa bukatar wasu manyan kayan aiki wajen hada kayayyaki da su. Za ka iya fara amfani da kayan da kake da su a gida, sannan ka hada kayayyaki masu ban sha'awa.

Yadda ya faro kamar wasa

Asali, ba a cika damuwa da fasahar yumbun na roba ba, inda sai da ya dauki gomman shekaru kafin aka fara mayar da hankali zuwa kansu.

Fitacciyar mai hada 'yar tsanar nan ta kasar Jamus, Kathe Kruse ce ta fara gano fasahar a karshe-karshen shekarun 1930s a cikin ababen da aka samar wajen tace man fetur.

Tana gwaje-gwaje ne domin gano wasu hanyoyin kirkirar 'yar tsanarta, amma sai ta yi watsi da gwajin saboda bai mata yadda take so ba.

Bayan wasu 'yan shekaru, sai diyar Kruse, mai suna Sofie Rehbinder ta sake lalubo aikin, wanda mahaifiyarta ta watsar ta sake bibiyar shi tare da kara sinadarin plasticiser da kala.

Ta hakan ne ta samu nasarar samar da yumbun na roba da za ta iya aiki da shi, inda ta sa wa kamfaninta suna, "Fimoik" ta hanyar hada sunan da ake kiranta da shi 'Fifi' da kalmar talla.

ana kuma hada wadannan kayayyakin kirkirar a wasu wuraren a Amurka domin ana ganinsu a tarukan baje-kolin fasaha na duniya.

Da farko an fara sayar da kayayyakin ne a shagunan sayar da 'yar tsana, amma a shekarar 1964 sai wani kamfanin ya saya fasahar, ya canja masa suna zuwa 'FIMO', sannan daga baya kamfanin Staedtker ya saye shi a shekarar 1978.

Yanzu FIMO ya zama sanannen suna idan ana maganar kayayyakin da aka sana'anta da yumbun roba.

Bayan haka, ana kuma hada wadannan kayayyakin kirkirar a wasu wuraren a Amurka domin ana ganinsu a tarukan baje-kolin fasaha na duniya.

Wani masani a bangaren Chemistry a Amurka ne ya fara gwada amfani da yumbu wajen tatso zafi daga tsasonsa, sai dai bai samu nasara ba daga baya, sannan fasahar ba ta samu karbuwa ba.

Daga baya kuma wata diyar daraktan, wadda take zuwa dakin gwajinsa, ta ci karo da yumbun, sai ta hada gida da shi.

Wannan ya sa aka samu nasarar kirkirar sinadarin Sculpey a shekarar 1967 domin amfani da shi musamman ga kananan yara wajen samar da kayayyakin wasa.

Wani masani a bangaren Chemistry a Amurka ne ya fara gwada amfani da yumbu wajen tatso zafi daga tsasonsa.

Amma duk da haka, sai a tsakankanin shekarun 1980s masu fasaha suka fara lura da yiwuwar amfani da yumbun wajen tsara abubuwa masu ban sha'awa.

Me ya sa ake amfani da shi?

Shekara biyu da suka gabata ne aka fara nuna min yadda ake amfani da yumbun roba wajen hada kayan ado. Amma daga baya na gano cewa tun ina karama na san su.

Sai nake tuna lokacin da nake dawowa gida da wasu robobi daga makaranta, in yi amfani da su wajen hada wasu abubuwa kamar dabbobi da sauran kayan wasan yara.

Nakan tuna yadda kalolinsu sukan bata min fararen kayan makaranta da hannayena.

Ba su da wahalar sarrafawa kuma ba sa bukatar manyan kayan aiki domin fara amfani da su.

Haka kuma da kudi kadan ake sayansu, ba kamar kayan hada tukwane na dauri ba, wanda ke bukatar a dade ana dafawa, shi wannan yumbun ko kadan aka dafa shi a cikin gida za a iya sana'anta shi.

Za ka iya fara hada kayayyaki da yumbu ta hanyar sayo shi a shaguna ko ta intanet, sannan ka yi amfani da wasu kayayyakin dafa abinci na gida irin su injin taliya da wuka da sauransu ka hada abin da kake so.

Duk mai sha'awa, ko yaro ko babba zai iya hada duk abin da yake so, da kowane irin na'urar zafafa abu yake da ita, kuma za a iya hada kayayyaki a ranar farko da ka fara koyo.

Wanda yake sha'awar sana'ar zai iya kara bincike domin gano wasu hanyoyin fadada fasahar.

Sannan da yanayin cigaban kimiyya a yanzu, za ka iya farawa da kwarewa a wannan bangaren a tashar YouTube da sauran hanyoyin kara ilimi a intanet.

Saukin illarsa ga muhalli

Ina sha'awar aiki da yumbun roba, amma kamar kowane irin kayan roba, ba zai rasa illa ga muhalli ba, wanda hakan ya sa akwai bukatar a kula da kyau.

Kasancewar shi sinadarin PVC da ake amfani da shi wajen hada yumbun, roba ce da aka hada da wasu sinadarai, dole zai ja wasu kwayoyin da suke yawo a cikin iska a lokacin da ake hadawa.

Don haka, dole akwai abin lura musamman sinadarin carbon. A daya gefen kuma, kayayyakin da aka hada da PVC din za a iya dadewa ana amfani da su, sannan za iya a sake amfani da su ba sau daya ba, ba sau biyu ba, inda a wasu lokutan ma baki daya ba a zubar da komai a ciki.

A wani bangaren za a iya kallon yumbun robar a matsayin masu taimakawa wajen gyara muhalli idan ana zubar da su da kyau.

Haka kuma idan ana amfani da shi, ba ya bukatar zafi sosai, zai iya dafuwa ya yi karfi a kasa da minti 20. Sannan sauran kayayyakin da suka rage bayan an kammala, za a iya sake amfani da su maimakon a zubar a bola.

Dadin dadawa kuma, duk da cewa yumbun roba ba ya narkewa a cikin kasa, za a iya amfani da ragowar shi bayan an kammala aiki wajen hada wasu kayayyakin ba tare da ya gurbata muhalli ba.

Idan ka taba kona yumbun roba, ka tabbatar iska yana gudana sosai a wajen sannan a wanke ko kuma a goge na'urar da aka yi amfani da ita sosai saboda yana sako wasu sinadarai da suke da illa ga lafiya.

Wannan yana cikin matsalolin yumbun. Amma duk da haka, idan ka bi dokokin aikin da shi da kyau, sannan ba ka saka wuta sosai ba, hakan ba zai faru ba.

Yara da manya za su iya amfani da shi saboda ba shi da wata illa. Sai dai ana ba da shawarar a rika kula da ka'idojin amfani da shi kafin fara amfani da duk wani abu da aka sana'anta.

A takaice, idan aka kwatanta su da sauran kayayyakin da sana'antawa ake yi irin su roba da karafa, za a iya cewa suna da saukin illa ga muhalli. Wannan ya sa suka zama zabi mafi inganci idan ana batun kayayyakin da aka sana'anta masu karko da kyau da saukin amfani da kuna saukin illa ga muhalli.

Damar kasuwanci a Afirka

Yanzu haka kayayyakin da aka sana'anta da yumbun roba din suna ta kara samun karbuwa a kasuwannin duniya, amma baa su yi fice ba sosai wasu yankunan Afirka. Akwai damarmaki ga masu sana'ar hannu da 'yan kasuwa masu dimbin yawa.

Lura da yanayin Afirka, idan ka dauki yumbun roba da suke da kaloli da yawa, masu zane za su iya amfani da su wajen hada kayayyakin ado.

Akwai damarmaki da daman gaske ga masu fasahar Afrika wadanda suke sha'awar bunkasa ayyukansu na hada kayayyakin ado masu ja hankali.

Masu dinki za su iya amfani da shi wajen hada zannuwan gado da botura da sauransu, makera za su iya amfani da shi a madadin karfe da sauransu.

Masu hada 'yar tsana da dama da masu sassaka da masu zane da masu fenti da masu kayan ado duk za su iya amfani da fasahar.

Bayan haka, akwai dama babba ga masu sana'ar da masu kasuwancinsu domin kayayyakin da aka sana'anta da hannu suna kara samun karbuwa a bangaren ado da kwalliya.

Yanzu yumbun roba ya zama babban kayan aiki ga masu hada kayan kwalliya. Yana taimakawa wajen hada kayan kwalliya masu kyau da rahusa.

Marubuciyar, Lemlem Hussien, masaniyar kimiyyar ba da magunguna ce 'yar kasar Eritrea, sannan ma'abociyar ayyukan fasaha. Haka kuma marubuciyar sa kai ce kuma 'yar kasuwa.

Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubuciyar ya zama daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.

TRT Afrika