The Ubuntu Connect invites Africans to appreciate their ancestors' shared struggles and triumphs. Photo:  Nana Dwomoh-Doyen

Kalmar Ubuntu ta samo asali ne daga harshen Zulu wadda take nufin "Ni ne saboda kai ne" – wannan shirin yana kokarin cike gibin da ke tsakanin Afirka da 'yan Afirka da ke zama a kasashen ketare, inda yake kokarin karfafa hulda tsakaninmu ba.

Shirin Ubuntu Connect wani shiri ne don karfafa asalin 'yan Afirka a zukatansu da zukatan 'yan uwansu maza da mata a fadin duniya.

Abu muhimmi game da shirin Ubuntu shi ne fahimtar cewa kowane dan Adam yana da alaka da dan uwansa, ba kawai mutanen da ke yankinsa ba, amma hatta asalinsa.

Ta hanyar rungumar shirin Ubuntu mun gano cewa muna da alaka, kuma ya dace mu karfafawa juna gwiwa kuma mu tallafa wa juna, ba tare da la'akari da iyakokin kasashe ba.

Bangaren farko na shirin Ubuntu Connect ya mayar da hankali kan muhimman abubuwa ci gaba da suka faru a bangaren ilimi da bincike don gano manyan abubuwa da samar da daidaito.

Wannan ya hada da jerin tarukan kan tarihin Afirka kafin zuwan Turawan mulkin mallaka, da tasirin cinikin bayi da aka yi daga Afirka zuwa Amurka ta take, kyawawan al'adun Afirka da dokoki da kuma addinai.

Mahalarta taron za su fahimci asalinsu wanda hakan zai ba su kwarin gwiwa da kuma samar musu da hadin kai.

Manyan kamanceceniya

Ta hanyar ziyarar gani da ido, shirin Ubuntu Connect zai kai mahalarta taron wuraren tarihi, inda za su taka sahun kakanninsu, kuma hakan zai tuno musu hukubar da bayi suka shiga lokacin cinikin daga Afirka zuwa Amurka ta tekun Atlantic.

Tafiyar ba kawai yawon bude ido ba ce, tafiya mai sosa rai kuma mai tasiri wadda za ta kawo waraka da kawo maslaha da kuma fahimtat tarihi.

An shirya shirin ne don dalibai masu nazari a fannin tarihi don su ga addinan Afirka da al'adu kai-tsaye da kuma ganin kamanceceniya da kuma bambance-bambancen da ake samu a fadin Afirka.

Yayin da suka tsaya a wuri daya da kakanninsu suka taba tsayawa, sun fahimci muhimmancin asalinsu iri daya kuma amfanin da suke iya samu daga bambance-bambancensu.

Taken shirin "The Re-Africanisation of the Diaspora and Africans" wani take ne na kai wa ga 'yan Afirka da suke zama a kasashen duniya.

Mpango wa Ubuntu Connect unatarajia kuongeza ufahamu zaidi wa historia na tamaduni za Kiafrika. Picha: Nyingine

Ana katafaren shirin ne da hadin gwiwar cibiyar African Chamber of Content Producers tare da African University College of Communication da Ife Studies a Fadar Ooni a Nijeriya da wasu sarakunan gargajiya a Afirka.

Alakar cude ni, in cude ka

Don tabbatar da karewa da alkinta tarihin Afirka da al'adunta, za a samar da tsarin nazarin tarihi da al'adun gargajiya a kowace fada da ke Afirka.

Wannan ba kawai zai ba 'yan baya ilimi da basira ba ne amma hatta kare martabar shirin Ubuntu ga daruwan shekaru masu zuwa.

Shirin Ubuntu Connect ya jawo tattaunawa tsakanin masu kaunarsa daga Liberia da Chadi da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Uganda da Cape Verde da Nijeriya da Ghana da Zambiya da kuma 'yan Afirka da ke zaune a ketare.

Wannan yana nuna muhimmancin aiki tare da cimma buri daya. An bukaci wadanda suke zaune a kasashen ketare da su taimaka da kwarewarsu da gogewarsu wajen gina kasarsu ta asali.

Wannan alaka ta cude ni, in cude ka za ta taimaka wajen kawo ci gaba a Afirka, wadda take taimaka wajen cin gajiyar al'ummomi daban-daban.

Idan ana maganar Afirka ba ana magana ta fadin kasa ba ne kawai, ana magana ne kan wata kasa da ke cikin zukatan miliyoyin mutane da ke sassan duniya daban-daban.

Nasarar da kakanninmu suka samu

Shirin Ubuntu Connect yana kokarin dawo da martabar mutunta juna da kaunar juna da ke tsakanin 'yan Afirka, inda za su taimaka wajen bayar da gudunmuwa kan bunkasa da ci gaban kasarsu ta haihuwa.

Shirin ya kasance wani kira ga 'yan Afirka, a gida da kuma waje, da su hada kai a karkashin shirin Ubuntu da kuma su hada gwiwa wajen ci gaban Afirka.

Ubuntu Connect Africa - Photo Credit. Nana Benjamin

Shirin Ubuntu Connect yana gayyatar 'yan Afirka da su fahimci fafutikarsu da nasarorin kakanninsu wanda suke kunshi cikin tarihi.

A zamanin da alkinta al'adu da asali suna da muhimmanci fiye da kowane lokaci, shirin Ubuntu Connect ya kasance wata fitila karfafa kwarin gwiwa da kuma hanyar karfafa asalinmu.

Karfin gwiwa

Abin a yaba ne bambance-bambancenmu, nasararmu cikin hadin kai da kuma dukufa wajen karfafawa juna gwiwa don samun nasara.

Yayin da duniya ta zuba ido kan Afirka dangane da makomar nahiyar, shirin Ubuntu Connect yana ishara ga sabuwar Afirka da kuma 'yan Afirka wadanda ba sa zaune a nahiya.

Labari ne na warkarwa da sulhu da kuma ci gaba. Wannan babbar manuniya ce ga jajircewarmu da dorewar kaunar shirin Ubuntu da ke jinin jikinmu gaba daya.

“Saboda kaunar Ubuntu, ya kamata ku hada hannu wuri daya don mu yi wannan tafiyar kawo sauyi tare. Idan muka hada gwiwa za mu iya sake rubuta tarihinmu da komawa ga asalinmu da dasa harsashin gina kyakkyawar nahiyar Afirka mai cike da hadin kai – Afirka ba kawai ta amince da tarihinta ba amma kuma ta rungumi makomarta da hannu biyu-biyu. Saboda za ka iya kuma ni ma zan iya," kamar yadda cibiyar Chamber ta bayyana.

TRT Afrika