Daga makamashin hasken rana a hamadar Sahara, zuwa iska mai karfi a kan teku, Afirka tana da damar fitar da green hydrogen /Hoto: Reuters

Daga Jonathan Fenton-Harvey

Yayin da ake da kyakkyawan fata ga nahiyar Afirka, dole gwamnatoci da kamfanoni su tabbata al’ummominsu suna da hanyoyin samun makamashi daban-daban.

Tattaunawa kan matsalar yanayi tana yawan siffanta nahiyar Afirka a matsayin wadda ke tasirantuwa, wanda hakan ne.

Sannan ana siffanta ta a matsayin ‘yar ba ruwanmu, musamman saboda kasa da kashi 4% na gas mai cutar da muhalli take fitarwa.

Duk da haka, lokacin da duniya ke fafutukar samo hanyoyin samar da makamashi mai tsafta, yana dada yin wahala a dauke kai daga muhimmancin Afirka wajen taimakawa da samar da makamashi mai tsafta.

Daga makamashin hasken rana a hamadar Sahara, zuwa iska mai karfi a kan teku, Afirka tana da damar fitar da green hydrogen.

Manazarta yanayi sun bayyana cewa shi ne waraka wajen samar da makamashi mai tsafta.

A lokaci guda kuma, akwai kalubale kan ko kasashen Afirka za su iya morar wannan dama ta makamashi, don amfanar mutanensu, da kuma ko ayyukan cigaba za su kasance don fitar da makamashin ne kawai.

Bukatar duba batun green hydrogen

Ana kallon green hydrogen a matsayin sabon makamashin da zai iya warware matsalar yanayi, saboda saukinsa, da saukin ajiya, da karancin fitar da gas mai gurbata muhalli.

Ana ganin zai iya maye gurbin kwal, da man fetur da gas a duka inda ake amfani da su, zai ninka samar da motoci da samar da dizal, wanda ke fitar da tururi kadai.

Hydrogen shi ne sinadari mafi saukin samu a duniya, kuma tuntuniana amfani da shi a abubuwa da yawa, kamar man mota, sarrafa karfe, da samar datakin zamani da kuma abinci.

A duniyarmu, ana bukatar makamashi don fitar da hydrogen a mafi tsaftar yanayinsa.

Ana kiran fasahar da electrolysis, wanda ta ita ne ake aika karfin lantarki cikin tankin ruwa, do rarrabe shi zuwa sinadarai biyu (hydrogen and oxygen).

Idan lantarki ya samu ne daga makamashi mai tsafta kamar hasken rana ko iska, samar da hydrogen ta hanyar eltrolyses ba ya janyo fitar da hayaki mai cutarwa, wanda shi ne silar zaman hydrogen mai sauyuwa.

Haka nan, ganin yawan albarkatun hasken rana da makamashin iska, nahiyar tana da ingantacciyar damar samar da green hydrogen.

Tabbas, Hukumar Makamashi ta Duniya, (IE) ta ce a wani rahotonta kan Damar Afirka na Samar da Makamashi a 2022, cewa arzikin makamashi mai tsafta a Afirka yana da muhimmanci wajen fara morar wannan dama.

Sakamakon wannan kyakkyawan fata, nahiyar za ta iya samar da megaton 5,000 na hydrogen duk shekara, a kasa da dala biyu duk kilogram.

Wannan shi ne daidai da jimillar abin da duniya take samarwa, in ji rahoton.

Rahoton na IEA ya kuma ce nan da zuwa shekarar 2030, Afirka za ta iya samar da kashi 80 na makamashin da take bukata, daga hasken rana, da ruwa, da sauran makamashi mai tsafta.

Cigaba a matakin nahiya

Shirye-shirye da yawa don samarwa da fitar da green hydrogen suna kan gaba a wadannan shekarun.

Ana sa ran Afirka ta Kudu za ta zamo kan gaba a nahiyar wajen samar da makamashin green hydrogen, saboda albakatun wadataccen hasken rana da iska da karafa masu daraja.

A watan Fabrairun 2022, Afirka ta Kudu ta sanar da gina bututun shirin green hydrogen, wanda ya kai na kimanin dala biliyan 17.8 zuwa 2030.

A 27 ga watan Nuwamba kasar ta hada taron koli kan green hydrogen a Cape Town, a inda Shugaba Cyril Ramaphosa ya karbi bakuncin shugabannin duniya da jakadojin kasashen waje.

Ramaphosa ya ambata cewa “Afirka ta Kudu ta shirya zama jagora a duniya wajen harkar green hydrogen”.

A lokaci guda kuma, ya fadi kiyasin cewa kasar tana da damar samar da “tan miliyan 6 zuwa 13 na green hydrogen da sauran kayayyakinsa nan da 2050”

Sanarwar ta shugaban Afirka ta Kudu ta zo bayan kamfanin sinadarai na Sasol, da kuma kamfanin karafa na ArcelorMittal suka sanar da shirin hako green hydrogen daga yankin North Cape.

A Satumba, Sasol ya sanar da hadin gwiwa da kamfanin Japan, Itochu, don hako green hydrogen don fitarwa da rarrabawa a kasar. Ichonu ya yi alkawarin bayar da tallafi ga wannan shirin.

Haka nan kasar tana kokarin samar wa ga kasuwannin Turai. A watan Janairu na 2022, ta rattaba hannu kan yarjejeniya, karkashin shirin Port Rotterdam da zai yi aiki a matsayin “mai tattaro green hydrogen a Turai”.

Sauran kasashen Turai kamar Jamus suna burin hada kai da Afirka ta Kudu a wannan harkar.

Zuba jari zai yi tasiri sosai, yayin da Afirka ta ce tana bukatar kusan dala biliyan 250 zuwa 2050, don cimma muradunta na samar da green hydrogen.

Sauran kasashe kamar su Masar, da Nijeriya da Kenya, duka suna kan mabambantan matakai na gina wannan shiri, wanda ke da burin fara aiki nan da shekara goma.

A shekarar 2021, Namibia da Botswana su ma sun sanya hannu a yarjejeniyar niyya tare da USAID don gina gagarumar tashar makamashin hasken rana don samar da green gydrogen.

Kasashen arewacin Afirka su ma suna yunkurin amfana da hasken rana a nahiyar ta Afirka.

A taron COP27 na Nuwambar 2022, kamfanin Masdar, na Hadaddiyar Daular Larabawa UEA, ya bayyana a wani rahoto cewa Afirka za ta iya daukar har kashi 10 na kasuwar green hydrogen na duniya nan da 2050.

Rahoton ya yaba wa kasar Moroko da cewa kasar da ke arewacin Afirka tana sa ran samar da green hydrogen a kasa da dala biyu, duk kilogiram daya a shekarar 2030, da kuma kasa da dala daya duk kilogiram a 2050.

Kari kan haka, rahoton ya ce masana’antar green hydrogen ta Moroko za ta iya samar da kusan ayyukan-yi miliyan hudu, da kuma karin dala biliyan 60 zuwa 120 ga ma'aunin tattalin arziki, GDP na nahiyar nan da 2050.

Wannan zai zamo gagarumin aiki, ganin cewa GDP a shekarar 2021da kadan ya wuce biliyan $132.

Yayin da Moroko ta kafa shirinta na samar da green hydrogen a Satumbar 2022, Hukumar International Renewable Energy Agency (IRENA), ta wallafa wani rahoto da ke bayyana cewa ana hasashen Moroko ta samar da green hydrogen na uku a araha, zuwa 2050.

Kamfanin Burtaniya ya yi alkawarin zuba jarin dala biliyan 1.5 a Tunisiya, da nufin bai wa kasar karfin samar da hasken rana don fitarwa.

Wannan wani babban zuba jari ne ganin cewa GDP din kasar a yanzu ya kai dala biliyan 40.

Kamar kasar Moroko, Tunisiya ta bayyana cewa tana nufin habakawa nata shirin na green hydrogen na 2022 nan da 2024.

Kasar Mauritaniya ta hada gwiwa da kamfanin Chariot Energy don mayar da hankali kan Shirin Project Nour.

Shirin yana da niyyar amfana da damar Mauritaniya ta samun iska da hasken rana don makamashi, don bai wa kasar damar samun makamashi mafi sauki na Afirka a duniya.

Kalubalen dubawa

Wadannan su ne kadan daga cikin ayyukan da ke faruwa a Afirka. Duk da cewa akwai damuwa kan wasu dalilan kamar tarnakin gudanarwa a gwamnatance, wanda ke iya janyo jinkiri.

Sannan zuba jarin ba lallai an yi shi da niyyar taimakon al’umma ba ne.

A wasu kasashen, samun lantarki ya yi kasa sosai, inda kasashe 24 suke da kasa da kashi 50 cikin 100 na lantarki.

Kenan, gwamnatoci da masu zuba jari suna bukatar inganta ababen more rayuwa don tabbatar da cewa mutane a nahiyar sun iya morar wannan sauyin na amfani da makamashi.

Bugu da kari, kamar yadda IEA ta lura, a farko Afrika tana da kashi 60 na hasken rana mafi inganci a duniya. Amma kashi daya ne kacal na hasken ranar Afirka ake mora don makamashi.

Ana gina layin bututun jigilar iskar gas daga yammaci zuwa arewacin Afirka, zuwa Turai, musamman Aljeriya tana samar da gas na hakowa. Amma ana iya sauya amfani da bututun don jigilar hydrogen.

Wasu masu sa ido sun nuna damuwa game da ayyukan da ke mayar da hankali kan hakowa, wato don yin amfani da albarkatun Afirka a kasuwannin duniya da ke wajen nahiyar, a mance da na cikin nahiyar.

Har ila yau, akwai tara dumbin bashi kan gwamnatocin Afirka ta dalilin wadannan ayyukan.

Amma tabbas akwai kyawawan abubuwa, duk da zuba jari na da muhimmanci, masu ruwa da tsaki dole su inganta gina kasa don jama’a su ci gajiyar kasancewa matsalar yanayi da ke shafar su.

Idan aka yi shi cikin lura, zai iya haifar da habakar tattalin arzikin Afirka da duniya, kuma ya tallafa wajen inganta cigaban arzikin nahiyar.

Togaciya: ra’ayoyin da marubucin ya bayyana a nan ba dole ne a ce sun dace da ra’ayi, mahanga, ko tsarin editocin TRT World ba.

TRT Afrika