Giwaye a dazukan Afirka / Hoto: AP

Daga Thomas Breuer

A lokacin da na fara aiki a Tafkin Kongo shekara 25 baya, ina tuna yadda ake da dazuka masu duhu da kuma samun ruwan sama sosai, da ma giwaye masu dumbin yawa.

A wancan lokacin dazukan na da fadi da kuma cunkushewa waje guda, ta yadda mutane ma ba za su iya haduwa da giwayen ba, hakan ya sanya da wahala a samu wata arangama tsakanin giwaye da dan adam.

A yau al'amarin ya sha bam-bam. Farautar hauren giwa da yawaitar kai komon mutane da cinye dazuka ana gine-gine da fitar da gonaki da tarwatsa dabbobin da arangamar su da mutane ya janyo karewar giwayen da ke dazukan Afirka.

Giwar daji da ake kira da (Loxodonta cyclotis) a kimiyyance, na daya daga cikin giwaye samfurin Afirka da suka rage, dayar ita ce giwar savannah (Loxodonta africana).

Tarihi ya bayyana wannan giwa na zaune a kurmunzun dajin yammaci da tsakiyar Afirka, amma wani nazari da aka yi a 2021 ya bayyana adadin giwayen ya ragu da kaso 86 cikin dari a cikin shekara 31 da ta wuce.

Tare da kusan giwaye 150,000 da suka yi saura a dazukan, a yanzu an bayyana su a matsayin dabbobin dawa da ke fuskantar hatsari.

Abu da babu irin sa

Dabbobin daji sun fita daban, suna da halaye da dabi'u da suka bambanta su da 'yan uwansu na yankunan savannah.

Su 'yan kanana ne, haurensu mikakke ne kuma siriri da yake kallon kasa. Suna da zagayayyun kunnuwa amma manya, hancinsu na da tsayi sosai, wanda ake ba su damar sarrafa abubuwa yadda suke so.

Wadannan abubuwa na da muhimmanci ga rayuwarsu a wadannan dazuka masu ruwan sama da duhu.

Wani nazari da aka gudanar a 2016 ya bayyana cewa wani babban bambanci shi ne su giwayen daji na haihuwa kadan ne, kuma suna daukar shekaru 31 kafin su haihu, wanda lokacin ya fi na giwayen savannah tsayi.

Giwayen daji na fara haihuwa a makare, sannan suna bayar da tazara sosai tsakanin haihuwa, sama da sauran nau'in giwaye, wanda hakan ke sanya da wahala a ce adadinsu ya dawo yadda yake a baya.

Yanayin Tafkin Kongo

Ci gaba da wanzuwar masu rayuwa a dazukan Afirka ya ta'allaka ga wanzuwar giwayen.

A matsayinsu na injiniyoyin rayuwa a dazukan, suna taimaka wa wajen gyara rayuwar mazauna dazukan ta hanyar baza taki da taimaka wa dajin wajen sake hayayyafa.

Giwayen dazukan Afirka na cin ganyayyaki da ciyayi da kayan marmari da jijiyoyi da sassaken bishiyoyi. Suna bude hanyar samun cimaka ga sauran halittu.

Tsawon shekaru, wadannan hanyoyi sun habaka zuwa manyan tituna, wanda ya janyo aka tafiyar da manyan dazuka suka koma yankunan da ke samar da albarkatun kasa da ruwa da kayan lambu da a baya ba a samun su a wannan daji.

Giwayen dazuka na taka rawa sosai wajen samar da iskar carbon mara kyau da ke yawo a cikin dajin, inda suke nasu aikin na rage lalacewar yanayi.

Ta hanyar cinye gajerun bishiyoyi da suke girma da wuri kuma suke daukar iskar carbon kadan, suna tatse dajin su raba shi da kananan bishiyoyi, wanda hakan ke bai wa manyan bishiyoyi damar girma sosai, hakan na taimakawa wajen yaduwar iskar carbon a cikin muhallai.

Suna kuma taimaka wa wajen tabbatar da samun sinadaran da suke habaka albarkatun noma ga jama'ar da suke rayuwa a kewayen dazukan.

Rauni

Duk da muhimmancin giwayen dazuka, suna fuskantar kalubale babba, sama da takwarorinsu na dazukan savannah.

Saboda yadda ba za haihuwa da wuri, an fi samun damar kai musu hari da kashe su, saboda ba sa dawo wa da sauri bayan karar da su da ake yi.

Baya ga barazanar kasuwar kasa da kasa ta hauren giwa da kuma yadda ba sa haihuwa su maye guraben wadanda suka mutu da wuri, karuwar barazana ga giwayen daji, zai ci gaba da janyo samun karancin kayan marmari a cikin dazukan.

Wani bincike da aka fitar a watan Satumban 2020 daga Filin Shakatawa na Lope da ke Tsakiyar Gabon ya bayyana kaso 81 na sauyin yanayi na afkuwa ne saboda rashin kayan marmari a dazuka a shekaru 30 da suka gabata tsakanin 1986 da 2018.

Giwayen dazuka na taka rawa sosai wajen samar da iskar carbon mara kyau da ke yawo a cikin dajin, inda suke nasu aikin na rage lalacewar yanayi. Hoto: WWF

Wannan kuma ya janyo raguwar giwaje da kaso 11 a tsakanin 2008 da 2018.

A yayin da mazauna dazukan suka takura kuma ga yaduwar mutane a yankunansu, sai ya zamana mutane da giwaye suna cudanya da juna.

Sai ya zama giwaye na zuwa iyakar gonaki, su lalata amfanin gona, sai kauyukansu su zama wajen da suka yi sabo da su.

Wannan na yawan janyo arangama da ma rasa rayukan mutane da lalata jin dadin zamantakewarsu, sannan yana kawo mutuwar giwaye.

Farauta ta addabi giwaye inda mafarauta ke harar manyan maza da mata. Yadda suke ganin ana kashe 'yan uwansu, kananan giwaye na firgita da samun dimautar kwakwalwa, kuma akwai wata karin magana da ake fada ta cewa "Giwaye ba sa mantuwa".

Ba a makara ba

A lokacin da giwayen daji suke fama don kubutar da rayuwarsu, Asusun Kiyaye Yanayi na Duniya (WWF) na aiki tare da gwamnatoci da shugabannin yankuna da kasashe kawaye don ganin an magance barazanar da ake wa wadannan giwaye.

Giwayen daji na bukatar yawo da keta duhun bishiyoyi manya don su tsira da rayukansu, amma kuma hanyoyin gudun hijirar na koma wa gonakin noma ko wuraren samar da kayan more rayuwa ga 'yan adam da samar da masana'antu da sauran wuraren ayyuka da kai komon mutane.

Muna bukatar gyara wadannan abubuwa ta hanyar mayar da hankali wajen tsare dazukan da giwaye ke rayuwa a cikinsu.

Fadan dan adam da giwaye abu ne da yake da wahalar sha'ani da shawo kai, wanda ya kan janyo asarar rayuka a lokuta da dama, yana bata rayuwa da sanya tsoro da bakin ciki da janyo kashe giwayen.

Dole ne mu nemi hanyoyin janye hankula, zirga-zirda da motsin mutane daga wadannan wurare don magance rikici, a mayar da hankulansu da wasu abubuwan da za su amfani mutane, giwaye da sanya su ji dadin rayuwarsu gaba daya.

Yana da muhimmanci a ce an dauki matakin kasa da kasa don hana fataucin hauren giwa daga wani yanki zuwa wani, daga masamarsu a dazukan Afirka zuwa inda ake sayar da su, musamman a Asiya.

Game da wannan, za a rage bukatarsu idan aka rage bukatar kayan alatu da ake samarwa da su musamman a kasashen da suka ci gaba wadanda suka sanya barazana ga halittu masu rauni.

Giwayen dazukan Afirka, tare da tsarin halitta da rayuwarsu na musamman, yanayin zamantakewa da babbar rawar da suke taka wa wajen tabbatar da wanzuwar dazukan, sun zama manyan misalan bayarwa wajen bayyana me ake nufi da dabi'ar yanayi da rayuwa.

Ta hanyar ayyukan tabbatar da kariya da kiyaye wa a ko yaushe, wayar da kan jama'a, da ayyukan yau da kullum ne za a kawar da wannan barazana ga giwayen tare da ci gaba da tsaftace yanayin rayuwarsu da ke amfanar dazuka da 'yan adam.

Dr. Thomas Breuer, shi ne Jami'in Ofishin Kula da Giwaye a Dazukan Afirka wand ake karkashin Asusun Kare Yanayi a Fadin Duniya. (WWF)

TRT Afrika