Harshen Hausa na Nijeriya yana kama da Swahili, fiye da sauran harsunan kasar sakamakon alakar Hausar da Larabci/Photo AA

Daga Umma Aliyu Musa

Ranar Hausa tana zaman ranar bikin harshen da ya fi yawan jama’a a Yammacin Afirka, wanda sama da mutum miliyan 100 suke magana da shi a fadin duniya. Harshen Hausa ya samu ne daga ajin harsunan Afirka-Asiya.

Harshen Hausa ya fi yaduwa ne a yankunan Nijeriya, da Nijar, da Ghana, da Chadi, da Benin, da Kamaru, da Togo, da Gabon, da Jumhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Wannan ya faru ne sakamakon daruruwan shekaru na tafiye-tafiye cikin yankunan kudancin Sahara, wanda mahajjata da ‘yan ci-rani suka yi don neman arziki da wadata.

A yau, harshen Hausa, ya zama harshen gama-gari, inda miliyoyin mutane suke mu’amala da harshen a gidajensu, da makwabtansu, da sauran mutanen duniya.

Hausa ya zama wata mahada tsakanin masu amfani da harsuna daban-daban a fadin Afirka. Amurka da sauran kasashen Turai ma ba a bar su a baya ba wajen amfani da Hausa.

Tasirin Hausa a kafafen sadarwa

Tasirin Hausa a fili yake a kafafen sadarwar yammacin Afirka. Akwai tarin gidajen rediya da talabijin da jaridu da dandalin intanet masu amfani da harshen hausa.

Wadannan kafofi sun isar da sakonni ga masu jin Hausa, da nishadantar da su, da ilmantar da su kan labarun duniya. Amfani da Hausa yana daukaka al’adu da hadin-kai, da sanin makomar Hausawa.

A fagen sadarwa a duniya, akwai tashoshi da sashen Hausa kamar su VOA Hausa ta Amurka, da BBC Hausa ta Birtaniya, da FRI Hausa ta Faransa, da CRI Hausa ta China, da DW Hausa ta Jamus, da Radio Iran Hausa, da kuma TRT Afrika Hausa. Dukansu suna gabatar da shirye-shirye cikin harshen Hausa.

Bayan zuwan intanet da shafukan sada zumunta na zamani, an samu karin yaduwar adabin Hausa, da fina-finai da kade-kade da suke taimakawa wajen alkinta harshen, da janyo masa karin mabiya da masoya.

Hausa a Amurka da Turai

Muhimmancin Hausa ya haura iyakokin Afirka, inda ya samu karbuwa a yammacin duniya. Cikin sama da shekaru 100, masana da manazarta sun taimaka matuka wajen koyar da harshen Hausa.

Tun kafin a fara koyar da Hausa a jami’o’i a Amurka, wasu kasashen Turai sun dade da fara koyar da shi. Turawa ‘yan yawon duniya kamar Eduard Vogel, da Karl Moritz von Beurmann, da kuma Gerhard Rolfs sun taba ziyartar kasar Hausa a gabanin nan.

Rubuce-rubucen James Frederick Schön (1802–1889) kan nahawun Hausa ya kafa ginshikin martaba harshen Hausa a fadin duniya, har harshen ya dauki hankalin manazarta harshe da masana masu sha’awar harsunan Afirka.

Jami’o’i da dama a Turai da Amurka da Asiya suna koyar da Hausa a matsayin kwas. Wannan dalilin ya sa dalibai daga fadin duniya suna tafiya yankunan Hausawa, kamar Arewacin Nijeriya da Jumhuriyar Nijar don koyon Hausa a jami’o’i, kuma su rayu tare da Hausawan asali.

A Turai ga misali, kuma, jin masu amfanin da harshen Hausa a tashar Hamburg Central Station ya fara zama ruwan dare.

An san Hausawa da zumunci, da ladabi, inda suke ziyartar ‘yan uwa da abokan arziki, da taimakon dangi, da sauran al’umma.

Hausa ya samu shuhura a biranen Turai da dama, inda masu amfani da Hausa suke taron bikin aure, da bikin suna, da na saurauta da addini.

Baya ga Sarkin Hausawa da ake da shi a Turai, wanda yake da fada a birnin Paris, akwai karin masu sarautun Hausa a fadin nahiyar Turai.

A irin wadannan bukukuwa, ana ganin kwalliya da tufafi, da abinci, da ke nuna yalwar arzikin Hausawa. Hakanan kuma, akwai kwararrun Hausawa ‘yan Nijeriya da ke rayuwa, suna taimakawa wajen cigaban kasashen da suke zama.

Yawancin wadannan kwararrun, sun hadu sun kafa kungiyoyi, kamar Arewa Global Ambassadors wadda ke dandalin WhatsApp, inda ake tattaunawa donmin cigaban Hausawa ‘yan arewacin Nijeriya, da tallafawa wadanda aka baro a gida Nijeriya.

Babbar nasarar kungiyar ita ce assasa shirin Arewa Youth Mentoring Programme, wanda ake gani a shafukan YouTube da Telegram, wanda yake samar da horo ga matasa a fannonin ilimi, da gurbin karatu, da fasahar zamani, da wayarwa kan cibiyoyin duniya, don shiga a dama da su a lamuran duniya.

Bugu da kari, Hausawan da ke Amurka da Turai sun taka rawa wajen alkinta harshe da al’adun Hausa.

Al’ummomin Hausa a wadannan yankuna suna shirya azuzuwan koyar da Hausa, da bukukuwan al’adu kamar na Ranar Hausa, don daukaka tarihinsu, saboda yara masu tasowa ku san asalinsu da martabarsu.

Alfanun Ranar Hausa ta Duniya

Manufar Ranar Hausa ta Duniya ita ce zaburar da mutane game da bukatar kare harshen Hausa da al’adunsu. Ana gudanar da nune-nune, da wasannin dandali, da wakoki, da bukuwan kara wa juna sani.

Wannan yunkuri yana da alfanu wajen kare martabar harshen Hausa da kiyaye amfani da shi, wanda ta haka ne za a kauce wa matsalar batan harshe, ganin yadda manyan harsunan duniya suke danne kanana.

Ranar Hausa biki ne na nuna dumbin al’adun Hausawa. Bikin yana karfafa al’adu da dabi’u da kida da rawa da adabi, inda ake nuna tasirinsu kan Afirka da ma duniya. Mutane daga bangarorin rayuwa daban-daban suna haduwa don murnar Ranar Hausa.

Ranar Hausa ba a bukukuwan da ake yi a Afirka kawai ta tsaya ba, ranar tana taimaka wa wajen hada kai tsakanin al’adu da kuma girmama juna. Sakamakon yawan jama'a, da farin jini a gidajen jarida, da kuma martabar da ya samu a kasashen duniya, Hausa yana da muhimmanci wajen daukaka dajarar nahiyar Afirka.

Wannan ya sa Ranar Hausa take taka rawa wajen tsare tarihin Hausawa a duniya, da alkintawa da martaba basira da al’adun Hausawa.

Marubuciyar wannan makala, Dr Umma Aliyu, Malamar Hausa ce a Jami'ar Hamburg da ke Jamus.

A kula: Wannan makala ta kunshi ra'ayin marubuciyar ne ba na TRT Afrika ba.

TRT Afrika