Wannan ɓata lokacin da aka mayar da shi jiki yana hana ci gaba kuma yana daƙile ƙwazo da ganin an yi komai bisa tsari " Photo: Reuters.

Daga Ambassador Dwomoh-Doyen Benjamin

Girmama lokaci, wanda wani amintaccen ginshiƙi ne na al'ummomi da yawa, da alama yana rasa darajarasa a sassa da yawa na Afirka.

African-time, kamar yadda aka saba kiransa, ya kasance wani batu mai ban mamaki da ake yawan magana a kansa a fadin nahiyar tsawon shekaru.

Tsananta bincike da kuma tattaunawa da mutane daga kasashen Afirka daban-daban sun yi ƙarin haske kan yadda wannan matsalar ke da muhimmanci. Rashin girmama lokaci na hana ci gaba da rushe tsare-tsare da kuma yana lalata ƙimar lokaci.

Kazalika, ta hanyar fahimtar tushen wannan hasashe da kuma rungumar sabbin hanyoyin warware matsalar, Afirka za ta iya tsallake matsalar rashin girmama lokaci tare da komawa kan turbar mutunta shi.

Dokta Kemi Wale-Olaitan, shugabar makarantar koyar da fasaha da zamantakewar al'umma a Kwalejin Sadarwa ta Jami'ar Afirka (AUCC), tana ba da kyakkyawar fahimta game da halin 'yan Afirka na makara, wato African-time.

A cikin bayanin nata, ta yi tsokaci kan yadda ake gayyatar manyan baƙi da dama zuwa tarukan da aka shirya fara su da ƙarfe 12:00 na rana, amma ba za a fara ba sai an ɓata lokaci sosai.

Wannan ɓata lokacin da aka mayar da shi jiki yana hana ci gaba kuma yana daƙile ƙwazo da ganin an yi komai bisa tsari.

A cewar Dr Kemi, African-time ya samo asali ne daga hadaddiyar mu'amalar bambancin al'adu da tarihi, da ababen more rayuwa.

"A al'adance, al'ummomin Afirka sun ba da fifiko ga kammala ayyuka a cikin ƙayyadajjen lokaci maimakon bin ƙayyadajjen jadawali.

"Wannan tsarin ya dace sosai da salon manoma, inda lokaci yakan tafi ne da alamun yanayi kamar tsayuwar rana ko carar zakara. Wannan fassarar al'ada ta haifar da kalmomi kamar "African time" da "Black man time."

Kazalika, a wannan zamanin, inda jadawali da ƙayyadajjen lokaci ke da muhimmanci don samun nasara, wannan hanyar tafiyar da lokaci ta African-time na iya hana ci gaba.

Yadda African-time ya zama jiki

Da aka zurfafa cikin batun, sai aka gane cewa halayyar African-time matsala ce da ta ba a nahiyar kawai ta tsaya ba, ta tsallake har zuwa wasu nahiyoyin.

Matsalar sufuri na daga cikin abubuwan da ke jawo African-time. 

Dr. Bishop Murphy Jackson, masani kuma babban malamin coci a Laberiya, ya yi tsokaci kan tsananin lamarin a cocinsa.

A Laberiya, ana kiran halayyar yin latti da sunan "Liberia time." Wannan jinkiri na yau da kullun yana rushe shirye-shiryen da aka tsara, yana lalata al'amura, kuma yana hana haɓaka da tasirin cocinsa.

Fitaccen jarumi kuma furodusa mazaunin Uganda, Mista Raymond Rushabiro, ya tabbatar da wannan ra'ayi, yana mai nuni da yadda ba a iya sarrafa lokaci a Uganda inda ake kiran hakan da "Uganda time."

Ya kuma jaddada yadda wannan al’amari ke tasiri a kasafin kudin shirya fina-finai da kuma yin illa ga harkar fim, inda ya ƙara da cewa a duk lokacin da suke son a samu lokacin yin kiran waya, sai su rage ainihin lokacin da sa’a daya ko fiye da haka, don su samu mutane su isa a lokacin da aka tsara.

A cewar Ambasada George Egeh, rashin sarrafa lokaci lamari ne mai matukar damuwa a Ghana, wanda ya haifar da kalmar "Ghana Man Time" na GMT, inda za a ga taron da aka shirya farawa da karfe 8 mahalarta ba sa fara zuwa sai bayan awa daya ko fiye.

Wasu mutanen kamar su Mista Phil Efe Benard, wani gogaggen mai shirya fina-finai daga Nijeriya, da Mista Shimekit Legese Nageenya, fitaccen dan jarida a Habasha, da Mista Tegha King, wani mai sharhi kan al’umma daga Kamaru, duk sun bayyana cewa a kasashensu ma ba a daukar lokaci da muhimmanci.

Mista Tafadzwa Charles Ziwa, wani masanin kimiyya da ke Zimbabwe, shi ma ya yadda ake ƙin darajta lokaci a Zimbabwe. Mista Jeromy Mumba, fitaccen dan wasan kwaikwayo a kasar Zambia ya tabbatar da cewa ko a kasarsa ma akwai kalubalen kiyaye lokaci inda har ake kira sarar da "Zambian time."

Nyokabi Macharia, wata 'yar kasuwa, 'yar fim, kuma furodusa a Kenya ta ce a ƙasarta ma abin bai sauya zane ba, ina ta ƙara da cewa ya zama al'ada, duk kuwa da irin ƙoƙarin da cibiyoyi da ƴan kasuwa ke yi don kawo sauyi.

Rafilwe Maitisa daga Afirka ta Kudu ta bayyana cewa duk da cewa rashin girmama lokaci bai karaɗe duka yankunan Afirka ta Kudu ba, amma har yanzu ƙalubale ne a tsakanin wasu 'yan kasar a Afirka ta Kudu.

Ganin yadda mutane da dama daga sassan nahiyar suka bayyana yadda rashin darajta lokaci ya zama ruwan dare a yankunansu - ya nuna tabarbarewar lamarin da nuna yadda ya zama wajibi a magance matsalar.

Darajar lokaci

A matsayina na ɗan Afirka mai sadaukarwa don nemo cikakkiyar mafita ga matsalolin da suka addabi nahiyar, na yi nazari sosai kan wannan matsala ta fuskoki da yawa.

Bukatar sake daidaita wannan tunanin ya fito a matsayin wani muhimmin mataki na raya al'adar kiyaye lokaci.

Ɗaya daga cikin abubuwan farko da ke ba da gudunmawa ga rashin darajta lokaci na Afirka ya ta'allaka ne a cikin fahimtar lokaci da ƙimarsa

A wasu al'ummomi da ke wajen Afirka, ana biyan mutane da yawa albashi a kowace sa'a ta aiki, suna ba da takamaimiyar hanyar auna ƙimar lokacinsu. Wannan tsarin yana haɓaka fahimtar lokaci kuma yana sauƙaƙe sarrafa lokaci mai tasiri.

Sabanin haka, a Afirka, albashin wata-wata ya zama al'ada, ya rabu da manufar samun sa'o'i. Sakamakon haka, talakawan Afirka suna fuskantar ƙalubale wajen fahimtar ƙimar lokaci ta hanyar kuɗi, wanda ke haifar da rashin sadaukar da kai kan lokaci.

Yi la'akari da wannan: fahimtar ƙarin lokaci da ƙimarsa ya zama ruwan dare a sauran al'ummomi musamman a Yammacin Duniya. Kowace ƙarin sa'a da aka yi aiki tana daidai da lada mai ma'ana.

Sabanin haka, babu irin wannan fahimtar a wasu wurare da dama na Afirka, lamarin da ke haifar da rashin sanin ƙimar lokaci.

Bukatar sake daidaita wannan tunanin ya fito a matsayin wani muhimmin mataki na raya al'adar kiyaye lokaci.

Kalubalen kayan more rayuwa

Kalubalen rashin kayan more rayuwa a Afirka na bayar da gudunmawa wajen yin African-time a nahiyar.

Rashin kyawun hanyoyi da yawaitar hadurra a kan hanyoyinmu da cunkuson ababen hawa da ba a tsammata ba na sanyawa da wahala a yi wani tsari na lokaci sannan a cimma wannan tsarin.

Wannan rashin tabbacin ne ka iya zuwa ya komo na yawan janyo a saduda, inda mutane suke hakura su amince da makara sakamakon rashin ingantaccen sufuri.

Haka kuma, tsarin aiki na awanni takwas a kasashen Afirka da dama na iya janyo nuna halayyar ko in kula ga lokaci a wani bangare na ranaku.

Kudirce cewar za a iya cimma wani sakamako ko yaya yake a wani dan lokaci, na iya janyo jinkiri da rashin yin abu a kan lokacinsa.

Magance matsalar

Domin magance matsalar African-time, yana da muhimmanci a tunkari matsalar gadan-gadan. Tsoron kar a ce mutum ya zaƙe da yawa ko yana nuna ya fi kowa iyawa, ya sanya an gaza neman hanyar magance matsalar.

Magance matsalar African-time na bukatar amfani da dabaru daban-daban na al’adu da samar da kayan more rayuwa a lokaci guda.

Kalubale ne da ke bukatar hada hannu waje guda tsakanin gwamnatoci da kungiyoyin farar hula da ‘yan kasuwa da sauran jama’a don magance shi.

Sabuwar fahimta kan ma’anar lokaci

Sauyi zuwa ga tsarin aiki da biyan kudi na awa-awa ko yawan aikin da mutum ya yin a iya sanya wa ma’aikatan Afirka dabi’ar girmama lokaci.

Wannan sauyi zai tilasta a sake nazari kan ayyukan kwaado da alakar dan kwadago da ubangidansa don tabbatar da biyan hakki bisa adalci da tsarin kasuwanci mai dorewa.

Tare da dabbaka wannan hadi tsakanin lokaci da daraja, ‘yan Afirka za su iya girmama lokacinsu da ganin darajarsa, su kuma habaka dabaru na tilas don aiki da lokaci yadda ya kamata.

Samar da kayan more rayuwa yadda ya kamata, musamman ma tsarin sufuri, na da muhimmanci wajen rage lokacin da ake dauka yayin tafiya zuwa wani waje kuma yana kara inganta hasashe. Wannan ya hada da gyara hanyoyi, kara yawan ababan hawa na haya, da aiwatar da tsarin sufuri na zamani da yadda za a kula da shi.

Komawa ga tsarin aiki na awanni 24 zai samar da sabbin damarmakin cigaban tattalin arziki a inganta sakamakon da za a samu. Wannan na bukatar sauya dabi’a, sabawa da awannin aiki, da tabbatar da kayan more rayuwa don taimakawa ayyuka.

Sauke nauyin da ke kan kowa

Ta hanyar kalubalantar al’adu da kuma karfafar tattaunawa a bayyane, za mu iya halayyar game da cika alkawarin lokaci a Afirka. Bayyana matsalar African-time yadda take – mai hana samar da cigaba – za mu iya hada hannu wajen aiki don magance ta.

Hadin kai tsakanin gwamnatoci, kungiyoyin farar hula, da daidaikun mutane na d amuhimmanci wajen tabbatar da sauyi na gaskiya.

Daidaikun mutane na da rawar taka wa sosai wajen magance matsalar African-time.

Idan kowa ya ji cewa yana da alhakin girmama lokaci da ba shi muhimmanci, yana aiki da lokutan da aka saka don gudanar da wani abu da girmama ayyukan da wasu ke da shin a da muhimmanci wajen samar da jama’a me gudanar da aiki a kan lokaci.

Matsalar African-time ta dade tana damun nahiyar, tana inganci da hana kawo cigaba. Sai dai kuma, ta hanyar fahimtar lamarin ta fuskar tarihi, magance yadda aka dauki darajar lokaci, magance kalubalen kayan more rayuwa, da duba yiwuwar habaka tattalin arziki a awanni 24,

Afirka na iya samar da aiki a kan lokacin da aka tsara da sakamako mai kyau. Mu dage mu rabu da dabi’ar lalaci, mu rungumi makoma da ake girmama lokaci da aiki da shi yadda ya kamata.

Lokaci ya yi da Afirka za ta sake yin duba da fayyace alakarta da lokaci, ta rabu da matsalar African-time tare da rugumar sabon zamanin aiki da lokaci. Sai hakan ta tabbata ne za mu iya amfana da dukkan damarmakin a ke nahiyar, wadanda za su kai mu hahun gaba a fagen kasa da kasa.

Marubucin, Jakada Dwomoh-Doyen Benjamin, Daraktan Zartarwa ne na Kungiyar Masu Samar da Kayayyaki ta Afirka.

Togaciya: Ba dole ba ne ra’ayin marubucin ya zo daidaida ra’ayi ko ka’idojin aikin jaridar TRT Afrika.

TRT Afrika