Kasashen yammacin duniya na bukatar lura da batun yawan al’umma

Daga Edward Paice

“Wannan shi ne karnin Afirka,” haka shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya shelanta a watan Satumban 2019. Idan shugaban yana nuni ne da yawan al’umma, to ikirarin nasa ba zai zama abin tababa ba.

Tabbas wannan batu na yawan al’umma yana bukatar kasashen yammacin duniya su lura da shi. Haka nan, ya kamata mafi yawan gwamnatocin Afirka su dauki matakin daidaita shi a kan lokaci. Muna fuskantar wani sabon zamani.

Tun bayan samun ‘yancin kai Afirka ba ta taba samun karuwar yawan al’umma cikin gaggawa kamar wannan lokacin ba”, kamar yadda wani masanin kididdigar al’umma ya fada.

A shekarar 1950, yawan al’ummar nahiyar bai wuce kashi 10 cikin 100 na jumullar al’ummar duniya ba. Zuwa shekarar 2050, kaso daya cikin hudu na al’ummar duniya za su kasance haifaffun nahiyar Afirka.

Sabanin haka, ana sa ran cikin irin wannan lokacin, yawan al’umma a Turai zai ragu daga kashi 20 zuwa kashi 10 cikin 100 na jumullar al’ummar da ke rayuwa a can, a halin yanzu.

Afirka za ta samar da fiye da rabin yawan al’ummar da za su karu a duniya cikin shekara 30 masu zuwa.

Cikin sabon zamani guda, yawan al’ummar Nijeriya za su haura na Amurka, sannan yawan al’ummar Gabashi da Yammacin Afirka za su karu su wuce na Turai ko yankin Latin Amurka.

Afirka ce nahiya ta biyu mafi yawan al’umma a duniya/AA

Zuwa karshen karnin, an yi hasashen ‘yan Afirka za su kai kashi 30 zuwa 40 na al’ummar duniya.

Wannan ba ‘tumbatsar’ al’umma ba ce, kamar yadda ake yawan ambatawa. Maimakon haka ana iya cewa wani gagarumin kari ne, da kuma muhimmin sauyi na yawan jama’ar.

Afirka ce za ta kasance a kan gaba a lokacin da yawan al’ummar duniya zai kai kololuwa, wanda hakan zai nuna muhimmin tasirinta ga hasashen sauyin yanayi, da wadatuwar samar da abinci, da wasu batutuwan daban.

Nahiya mafi yawan matasa

Me ya kawo saurin karuwar yawan al’umma? Akwai manyan abubuwa biyu da ke haifar da hakan.

A shekarar 1950, hasashen tsawon rai a Afirka bai wuce shekara 40 ba. A yau ya kai sama da shekaru 60, yayin da ake sa ran ya kai shekara 70 zuwa nan da tsakiyar wannan karnin.

A daidai wannan lokaci, jumullar yawan haihuwa, wato matsakaicin adadin haihuwar yara masu rai da kowace mace take yi, ya haura hudu. Zai ci gaba da kasancewa sama da uku a shekarar 2050.

A lokacin nan, yawan al’umma a cikin kasashe kamar 60 a fadin duniya zai zama yana raguwa.

Alal misali, yawan al’ummar wasu kasashe kamar Italiya da Koriya ta Kudu zai ragu zuwa rabin yawansu na yanzu a cikin wannan karnin na 21, matukar yawan haihuwa bai wuce yawan masu mutuwa a cikin al’ummarsu ba.

Abin da ya fi daukar hankali game da karuwar yawan al’ummar Afirka – na abin da ke jawowa da kuma sakamakon karuwar, shi ne yawan matasan da al’ummar ke da shi.

Matsakaitan shekarun mutanen Afirka cikin shekarar 2020 ya kasance shekara 18.6, wato shekara 24.4 a Arewacin Afirka da kuma shekara 17.5 a kudu da Hamadar Saharar Afirka.

Wannan ma ya yi kasa da matsakaicin shekaru na 27.9, da ake samu a kasashen da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana a matsayin marasa “cigaba”. Haka abin yake a Afirka yankin kudancin Sahara.

Abin da ya fi daukar hankali game da karuwar yawan al’ummar Afirka shi ne yawan matasanta/Photo AA

Cikin shekara 30, tsaka-tsakin shekaru zai haura zuwa 23.9, amma wannan zai ci gaba da zama kasa sosai da matsakaicin shekaru na 35.9, kuma kasa da rabin adadin a Gabashin Asiya.

‘Yan kasa da shekara 18 ne suka fi yawa a daya cikin uku na kasashen Afirka. Kusan kasashe 12 suna da mutane masu matsakaicin shekaru 16, ciki har da Jamhuriyyar Dimukradiyyar Congo, wadda take daya daga cikin kasashe mafiya yawan al’umma.

A Chadi da Nijar, matsakaicin shekarun mutane ya tsaya ne a kasa da 15. Zuwa shekarar 2050, kashi 40 cikin 100 na al’ummar duniya ‘yan kasa da shekara 18, za su kasance ‘yan Afirka ne.

Duba da yawan matasa da kuma yawan haihuwa a cikin al’ummar, Afirka za ta samu bunkasar yawan jama’a sama da kashi biyu cikin 100 har na tsawon akalla shekara 10 masu zuwa.

Kasashe 12 masu yawan al’umma sama da miliyan 10 suna ci gaba da samun habaka da sama da kashi 2.5 cikin 100 duk shekara.

Zuwa shekarar 2050 za a haifi jarirai sama da biliyan 1.5 a Afirka. A wannan lokacin, kusan kashi 40 cikin 100 na duka yaran da za a haifa a kowace shekara a fadin duniya, za su zama ‘yan Afirka ne.

A tarihi, wannan wani misali ne mai ban al’ajabi na tasirin haihuwa, wanda aka gani a wani yanki na duniya.

Yayin rubuta littafin “Youthquake – Why African Demography Matters”, wanda ya yi magana kan batun muhimmancin tumbatsar matasa, bambancin al’ummomin na kabilu da addinai da jinsi ne ya fi daukar hankalina fiye da karancin shekarun mafi yawan mutanen.

Bambance-bambancen sun yi yawan da za a ce Afirka al’umma guda daya ce.

Matsakaitan shekarun mutanen Afirka cikin shekarar 2020 ya kasance shekara 18.6/Photo AA

Jumullar yawan haihuwa a Afirka ta Kudu, da Moroko, da Libiya, da Tunisiya yana “matakin sauyawa”, wato kimanin haihuwa biyu ga kowace mace. Amma mata a Nijar kuwa, suna haihuwar yara bakwai ne.

Ko da a wuraren da yawan haihuwa yake da daidaito, yawan al’ummar Afirka ya sha bamban matuka da yadda ya kasance a lokutan baya.

A yawancin yankunan duniya, inganta damar samun ilimi ga mata yana da alaka da raguwar yawan haihuwa. Haka ma yake a kasashen Afirka da dama.

Amma a Nijeriya, jumullar yawan haihuwa ya kai kusan haihuwa 4.5 ga kowace mace, ko da a cikin matan da suka kammala karatun sakandare.

A tsakanin mata masu ilimin matakin sakandare da ke Jamhuriyyar Dimukradiyyar Congo, jumullar yawan haihuwar ya kai kusan haihuwa shida.

A Ghana kuwa, wadda a Afirka a ke wa ganin jagora ce a fannin ilimin mata a matakin sakandare, kuma jagora wajen amfani da dabarun hana haihuwa.

Yawan haihuwa yana kan matakin haihuwa kusan hudu, wato an samu ragin haihuwa daya kacal, idan aka kwatanta da shekarun 1990.

Haka ma a Malawi, duk da yawan amfani da dabarun hana haihuwa na zamani, ba a samu raguwar haihuwa kasa da hudu ba.

Mata masu wadata da wayewa da masu rayuwa a birane, yawanci sun fi son haifar yara kadan.

Sai dai kuma kashi daya cikin biyar na matan Angola masu rayuwa cikin wadata, suna haihuwar yara hudu a matsakaicin lissafi.

A Jamhuriyyar Dimukradiyyar Congo, mata masu wadata suna haihuwar kimanin yara shida, yayin da a Uganda da Nijeriya suke haihuwar kusan hudu.

A birnin Addis Ababa na Habasha, a matsakaicin lissafi mata sukan haifi kasa da yara biyu. Amma wannan ya sabawa yadda aka saba gani a tarihi game da matan da ke rayuwa a biranen Habasha, sannan da ma biranen Nijeriya, inda yawan haihuwa ya kai 4.5.

A fadin Afirka, ana samun yawan wadanda suka saba wa wannan “tsarin adadi” na duniya, kamar yadda ake samun wadanda suka dace da shi.

Samun gagarumin bambanci tsakani da kuma a cikin kasashen, shi ne abin da aka saba gani.

Bunkasar Afirka

Cikin shekarar da ta gabata, manyan labarai game da yawan al’umma sun mayar da hankali kan ikirarin Elon Musk na cewa saurin raguwar yawan haihuwa a fadin duniya yana “daya daga cikin ababen da ke barazana ga cigaban duniya”.

Sai kuma batun China da ke fama da raguwar yawan mutane, da kuma kasancewar Indiya ta sha gaban China a matsayin kasa mafi yawan al’umma.

Ana haifar yara da yawa akai-akai a Afirka/Photo AA

Ga kuma batun jumullar yawan al’ummar duniya da ya kai biliyan takwas, bayan samun karin kashi daya bias uku wanda ya samu cikin shekara 20 kacal.

Ba a faye ambaton tasirin Afirka kan yawan al’ummar duniya ko kuma abin da haka zai iya haifar ga duniyar ba. Haka zancen yake a cikin Afirkar kanta da kuma kasashe da yawa, ba a jin tattaunawa kan batun yawan al’umma.

Bai kamata a ce ana kau da kai daga zancen karuwar yawan al’umma a Afirka ba.

A Yammacin duniya, hakan alama ce da ke nuni da raunin fahimtar batun sanin nahiyar Afirka.

Ana yawan ambaton Afirka a matsayin kasa daya tilo, maimakon yanki mai kasa 54, wanda adadi ne da ya kai daya cikin hudu na yawan kasashen duniya.

Tasawirorin da aka saba gani ba su yi daidai wajen zayyana fadi da girman nahiyar ba. Amurka da China,da India,da Turai,da Japan duka za su shige cikin fadin kasar da ta yi Afirka.

Duk da daruruwan shekaru na fahimtar Afirka, Kasashen Yamma ba su san nahiyar ba gaba daya, kuma har yanzu ba sa nuna damuwa wajen magance wannan jahilcin.

Dole ne a sauya hakan cikin gaggawa. Kuma babbar manufar rubuta littafin Youthquake shi ne samar da wayar da kai a ciki da wajen Afirka, game da gagarumin sauyin jama’ar da nahiyar ta samu.

Me ya sa wannan gagarumin sauyi da kuma karuwar yawan al’umma suke da muhimmanci? Wannan tambaya ce da ake yawan yi min.

Me ya sa ba a tambayata kan rashin muhimmancin hakan.

Afirka za ta samar da rabin yawan cigaban da za a samu a fannin samar da ma’aikata a duniya, cikin gomman shekaru masu zuwa.

Karuwar yawan al’umma, hade da cigaban tattalin arziki, da wadatar ma’adanai za su yi tasiri kan tsarin kasuwancin duniya.

A siyasar yanki, bunkasar girman Afirka ya taka rawa wajen janyo hankalin kasashen waje (da kuma zuba jari) daga China da Hadaddiyar Daular Larabawa da Turkiyya da Indiya.

Yanzu ba zai yiwu ba a ce hakan ya gaza bai wa Afirka damar shiga a dama da ita cikin kungiyoyin fada a-ji na duniya.

An ga hakan karara lokacin da kasashe daga bangarori biyu suka yi ta zawarcin kasashen Afirka game da yakin Rasha da Ukraine.

Afirka za ta zamo cibiyar yaki don rage illolin dumamar yanayi da kuma magance sauyin yanayi.

Tasirin Afirka da ‘yan Afirka a harkokin wasanni da kade-kade da kwalliya da addini yana ta habaka.

A takaice dai, abubuwa kadan ne ba za su tasirantu da karin yawan al’ummar Afirka ba cikin shekaru masu zuwa.

(Edward Paice Darakta ne na Cibiyar Bincike ta Afirka mai cibiya a Landan. Littafinsa na baya-bayan nan shi ne “Youthquake – Why African Demography Matters”)

TRT Afrika