Daga Peter Asare-Nuamah
Juyin mulki ba sabon abu ba ne a Afirka. Daga shekarar 1952 zuwa 2022, an yi juyin mulki guda 214, 106 daga ciki sun yi nasara yayin da 108 ba su yi nasara ba.
Ko da yake, tun shekarar 1990 yawancin kasashen Afirka sun fahimci bukatar rungumar tsarin dimokradiyya don samar da ci gaba a nahiyar.
Bayan haka ne Afirka ta rage fuskantar juyin mulki, inda tsarin dimokradiyya ya fara zama daram a wasu kasashe.
Ko da yake a baya-bayan nan nahiyar tana fuskantar dawowar juyin mulki. Tun shekarar 2020, an yi juyin mulki a kasashe bakwai a Afirka: Burkina Faso da Sudan da Chadi da Guinea da Mali da Nijar yanzu kuma Gabon.
Yawancin juyin mulkin da aka yi sun faru ne a kasashen da Faransa ta yi musu mulkin mallaka. Na baya-bayan nan na ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023, dakarun da ke tsaron fadar shugaban kasa karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tchiani sun hanbarar da Shugaba Mohamed Bazoum na Nijar.
A ranar 30 ga watan Agustan 2023, sojoji sun hanbarar da Shugaban Gabon Ali Bongo daga mulki.
Batun juyin mulkin Gabon ya biyo bayan ayyana Shugaba Bongo, wanda shi tare da mahaifinsa sun mulki Gabon tsawon shekara 53, a matsayin wanda ya lashe zaben kasar. Sojojin sun soke sakamakon zaben kuma sun yi wa shugaban daurin talala.
Rukunan dimokuradiyya
Ya kamata a sake duba batun dalilin da ke saka sojojin yin juyin mulki da kuma yadda shugabanni da 'yan Afirka za su bude sabon babin ci gaba da tabbatar da wanzuwar tsarin dimokradiyya a nahiyar.
Shakka babu, kasashe da dama na Afirka ba sa samun kyakkyawan shugabanci da tsarin dimokradiyya kuma babu tsare-tsaren da za su ciyar da nahiyar gaba tsawon shekaru.
Afirka tana daga cikin nahiyoyi mafiya talauci ko ma a ce wadda ta fi talauci ta fuskar ci gaban dan Adam a duniya.
Ko da yake abin mamakin shi ne Afirka tana daya daga cikin nahiyoyi mafiya arzikin albarkatun kasa a duniya. Wannan abin mamakin "na kasancewa mai arziki kuma mai fama da talauci" ya jawo shugabanni da 'yan Afirka matsala.
Idan aka duba batun matsin lamba daga ciki da ketare kan karfafa dimokradiyya, wasu shugabanni suna ganin dimokradiyya ta kunshi kawai yin zabuka ne.
Wannan ya sa ake kallon zabe a matsayin babban rukunin dimokradiyya ba tare da la'akari da yadda aka gudanar da su ba, ba a mayar da hankali a kan sauran muhimman rukunan dimokuradiyya.
A zahiri dimokuradiyya da shugabanci sun wuce gaban zabuka, kodayake zabuka suna share fagen tabbatuwar dimokradiyya da shugabanci nagari.
Sauran muhimman rukunan dimokradiyya da doka sun hada da damawa da 'yan kasa wajen tsare-tsare da kuma kyautata rayuwar al'umma da ci gaba.
Wadannan bangarori idan aka tsame su daga dimokradiyya da shugabanci nagari, to kasa za ta fuskanci babban kalubale.
Daga lokaci zuwa lokaci, bayan zabuka yawanci shugabanni a Afirka suna watsi da wadannan muhimman rukunai na dimokradiyya da kyakkyawar shugabanci.
Bukatar samar da ci gaba
Maimakon a mayar da hankali wajen magance manyan matsalolin Afirka kamar cin hanci da rashawa da rufa-rufa wajen tafiyar al'amura da talauci tsakanin al'umma da wagegen gibin da ke tsakanin talaka da mai shi da sauransu, wasu shugabannin Afirka sun fi mayar da hankali kan tara wa kansu da danginsu dukiya, bayan burinsu na siyasa da na samun nasara a zabe bayan zabe.
Irin wadannan matsaloli suna danne hakkin talakawa yayin da 'yan siyasa suke kara kudancewa. Ba abin mamaki ba ne yadda wasu suke kallon siyasa a matsayin hanyar samun makudan kudi dare daya a kasashen Afirka da dama.
Karuwar yawan matasa da karuwar rashin aikin yi a nahiyar ya jawo rashin daidaito a siyasance a Afirka, ko juyin mulki ko kuma rikicin ta'addanci idan ba a magance su ba.
Lokaci ya yi da zababbun shugabannin Afirka za su yi aiki fiye da 'zaben shugabanni' wajen saukar da nauyin da ya rataya a wuyansu. Ya kamata shugabannin Afirka su yi wa jama'arsu aiki wajen bai wa bukatar mutanensu fifiko fiye da bukatun kansu.
Dimbin mutane sun fito kan tituna don nuna goyo bayan ga jagororin juyin mulki a Nijar da Gabon, ya kamata wannan ya sa shugabannin Afirka su farka su mayar da hankali kan bukatu da ci gaban jama'arsu.
Ya zama wajibi shugabanni su dukufa wajen canja salon yadda suke shugabanci da tafiyar da dimokradiyya don ci gaban nahiyar, kamar yadda ake fata a Muradu Masu Dorewa na Majalisar Dinkin Duniya (SDGs) da kuma muradun Tarayyar Afirka wanda ta yi wa take Agenda 2063.
Marubucin Dokta Peter Asare-Nuamah malami ne a Jami'ar Environment and Sustainable Development a kasar Ghana, kuma babban mai nazari ne a Cibiyar Bincike kan Ci gaba a Jami'ar Bonn da ke kasar Jamus.
A kula: Wannan makala ta kunshi ra'ayin marubucin ne amma ba ra'ayin TRT Afrika ba.