Daga Toby Green
Duk da cewa jaridun duniya ba su daukar labarin ba, kasar Guinea-Bissau da ke Yammacin Afirka tana ta fama da babbar matsalar abinci cikin watannin baya-bayan nan.
Hankalin gidajen labarai ya karkata ne kan zaben majalisar dokokin da ya gabata a watan Yuni, wanda 'yan adawar Shugaba Umaro Sissoco Embalo suka yi rinjaye.
Kudin da aka saba biyan manoman kashu a kasar ya koma rabi idan an kwatanta da 2022.
Kashu shi ne babban abin da kasar ke fitarwa, kuma tana samun kudin-shiga da ya kai kashi 95% na jimillar kayayyakin da kasar ke fitarwa. Wannan ya sa manoma a karkara suna fuskantar matsala.
A shekarar 2022, gwamnatin Guinea-Bissau ta sanya farashin kashu a kasuwa kan CFA 375, duk kilo (kusan dala $0.07).
A lokacin da Jaime Boles, shugaban kungiyar Tarayyar Manoma Kashu na kasar, kuma shugaban Kungiyar Manoma, ya ce wannan farashi ne madaidaici, a kasar da da a cewar Majalisar Dinkin Duniya, mutum ɗaya cikin biyar ba ya samun isasshen abin da zai ci.
Sai dai kuma, a watan Afrilun wannan shekara labari ya fara yaɗuwa na cewa farashin da manyan 'yan kasuwan da ke sayen kashu suke bayarwa, ya fara sauka sosai.
Boles ya ankarar da cewa farashin da ake biyan manoma na cikin gona tuni ya yi kasa da CFA 375, wanda gwamnati ta saka. Sai dai a zahiri farashin yana tsayawa ne tsakanin CFA 200 da 250. Boles ya shawarci gwamnati ta rage kudin harajin da take cajin masu saya, don taimaka musu su biya cikakken farashin.
Gwamnatin ta dogara ne sosai kan haraji daga harkokin kashu, don cika alkawuran biyan bashin kasashen duniya. Wannan ya sa gwamnatin ta dage wajen cajin kudi da yawa a matsayin haraji.
Cinikin ban-gishiri...
Masu sayen kashu din sun ki sauya farashi. Wasu rahotanni suna cewan sun kafa wata gamayya, ta amfani da guruf din WhatsApp don hada yankunan karkara da babban birnin Bissau, don tsayar da daidaitaccen farashin kilo, kasa sosai da farashin da gwamnati ta saka.
Zuwa karshen watan Afrilu, yankuna da dama a kasar sun shiga takura: suna da tarin 'ya'yan kashu jibge a gida suna dako, amma babu masu sayen da suke iya biyan farashin da gwamnati ta saka.
Manoman karkara a yankin Tombalí – wanda ba shi da tazara daga birnin Bissau, sun koma yin musayen ban-gishiri na ba ka manda, tsakanin kashu da shinkafa da magani.
A sauran yankunan, manoma sun koma kasuwancin bayan fage, suna karbar kasa da farashin gwamnati saboda suna cikin matukar bukatar kudi.
A irin wannan yanayi manoma suke ribatar farashin kwayan masarufi kamar man girki da shinkafa.
Kasuwar kashu ta zamo wani batu a zaben kasar. Yayin da kashi 80% na 'yan kasar Guinean-Bissau suka dogara kan kashu wajen samu kudin-shiga. Tabarbarewar farashin da ake sayen kashu yana lahani kan wadatuwar abinci.
Gadon mulkin mallaka
Makonni biyu kafin zaben 'yan majalisu, shugaban Jam'iyyar African National Congress, Ibrahim Dialló, ya yi ikirarin cewa gwamnati ba ta yi komai kan ceto manoma kashu ba. Kuma ta bar manoman cikin “yunwa da matsanancin talauci da mutuwa”.
Bayan zaben, 'yan adawa sun karbe iko da Majalisar Dokokin Guinea-Bissau, Sai dai duk da haka, a cewar wani rahoto taruwar kashu da ba a siya ba ya haifar da matsananciyar yunwa a yankuna da dama.
Jaime Boles ya ce: “Kananan manoma sun sayar da duka girbinsu, [a kasa da farashin gwamnati] saboda ba su da abin siyan abinci; kuma ba su da abinc da za su ci”. Ya kira wannan yanayi da tsagwaron zalunci.
Kenan, me ne sanadin wannan babban bala'i a wannan matalauciyar kasa? Lokacin da Guinea-Bissau ta samu 'yancin-kai daga Portugal a 1974, turawan sun bar masana'anta daya tilo a kasar (ta yin giya) bayan shekaru 80 na mulkin mallaka.
Bayan nan, sabuwar kasar ba ta da wani zabi face bin tsarin cigaban tattalin arziki mai dogara kan kayan gona guda, da ya faro lokacin mulkin mallaka.
Wannan ya zamo babban abin damuwa: kashiu 90% na kayayyakin da kasar ke fitarwa kan abu daya ne. Shi ya sa tattalin arzikin ya ke saurin tasirirantuwa.
Neman mafita
Baya ga wadannan manyan batutuwa, wani dalilin kai-tsaye da ke haifar da matsalar shi ne masu sayen kaya, wadanda ke kai kayan kasar Brazil, da China da Indiya, wadanda kuma suka kafa gamayya don karya farashin da suke biya kan kashu.
Amma wannan ya biyo bayan sauyin tattalin arzikin duniya: ta yadda masu sayen kaya suke fuskantar karin kashe kudi sakamakon hauhawar farashi a duniya, bayan annobar COVID-19 da yakin Ukraine.
Bugu da kari, masanin tattalin arziki Santos Fernendes ya ba da misalin karyewar darajar CFA wajen canji da dalar Amurka, a matsayin wani dalili.
A halin yanzu, 'yan kasar Guinea-Bissau dole su fara neman mafita. Amma ba abu ne mai sauki ba a kasar da noman kashu yake da muhimmanci wajen tara kudin biyan bashi, da kuma ciyar da 'yan kasa.
Fernendes ya ayyana tasirin wannan matsala kan harkokin samun kudin gwamnati, duk da dai a watan jiya, Asusun Lamuni na Duniya ya amince da ba wa kasar karin bashi.
Akwai barazanar fuskantar zamani mai tsanani, da zai dauki tsawon lokaci a kasar, kafin a ce an dauki hanyar magance matsalar ana tsaka da tarin matsalolin duniya da suka sha kan kasar.
Toby Green, Farfesa ne a kan nazarin tarihin Afirka a Jami'ar King’s College London.
Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana a ba sa wakiltar mahanga ko tsarin editocin TRT Afrika.