Daga Staff reporter
Shiga ko kuma rashin shiga tsere na ɓera, tambaya ce da dan'adam ya daɗe yana neman amsa akai.
A garin Morogoro da ke kasar Tanzaniya, mafi yawan lokuta shiga tseren ɓeraye yana nufin kutsa kai cikin romon kasuwancin kiwon ɓeraye zabiya.
Leah Pangapanga ta tsunduma cikin wannan sana'ar wacce ba kasafai ake yi ba sama da shekaru biyar da suka wuce, bayan samun ƙwarin gwiwa daga buƙatu na neman ɓeraye zabiya daga cibiyoyin bincike da ɗakunan gwaje-gwaje.
Leah ta samu kejin kiwon ɓeraye zabiya10 daga wata ƙawarta, daga nan adadinsu ya yi ta ƙaruwa, tun daga lokacin ta yi ta samun ci gaba.
"Iri na ɓeraye zabiya suna hayayyafa sosai. Lokacin daukar cikinsu yana tsakanin kwanaki 28 ne, kuma suna haihuwar ya'ya 12 a lokaci guda. wani abun burgewa shine uwar berayen ba ta dadewa take daukar wani ciki.'' lead ta shaida TRT Afirka.
Bunkasar Kasuwa
Duk da cewa kasuwar ɓerayen zabiya tana sama tana kasa amma ribar da ake samu ya toshe duk wani abu.
Ana biyan masu kiwon berayen kudin Tanzaniya akalla shilling 5,000, ko kwatankwacin dalar Amurka biyu a kan kowanne ɓera zabiya, kasancewar ana saya da yawa kasuwancin yana samar da riba sosai.
"Kostoma daya na iya sayen ɓeraye 200 zuwa 300 a lokaci guda," in ji Leah.
Kwalejoji da makarantun sakandare sun fi son ɓerayen zabiya don gwaje-gwajen halittu saboda su irin dabbobi ne masu kama da halittar dan'adam.
Kiwon ɓerayen ba shi da wani wahala a mafi yawan lokuta.
Abincinsu da ake ba su da farko shine cakudannan dusa na musamman dake dauke da isassun abubuwan gina jiki da zai su yi girma cikin saurin girma.
Masu kiwo da dama sun fi son hada dusar da abincin ruwa da nau'in sinadaren abinci na bitamin da madarar foda don taimaka wa ɓareyen wajen shayarwa da daukar ciki.
Kawar da rashin fahimta
Daya daga cikin kalubalen da masu kiwon ɓera suke fuskanta a Tanzaniya shi ne yaƙi da tunanin al'umma kan cewa ɓeraye halitta ne da ke yaɗa cututtuka, musamman la'akari da cewa ana alakantasu da annoba.
Ilimin kimiyya ya nuna cewa ɓerayen zabiya sun bambanta sosai da sauran ɓeraye da suka mamaye gidaje da filayen wadanda suke haifar da barna.
A lokacin da Leah ta fara kiwon berayen zabiya, mutane da dama daga yankinta sun yi tunanin ta na jefa lafiyarta cikin a hadari kan wani abu da ba shi da wani daraja.
"Sun dauka cewe ba ni da hankali kuma a rude nake, saboda na yi fice a harkar kiwon kaji, mutane da dama sun gaza fahimtar dalilan da suka sa na mai da hankalina wajen kiwon beraye, gaskiyar magana ana ita ce kiwon kaji ya na da matukar wahala," in ji Leah.
"Daga baya na daina kiwon kaji saboda kara tsadar kayayyakin abincin ciyar da su da kuma cututtuka, sabanin ɓerayen zabiya da ake bukatar a ciyar da su sau daya a rana kuma ba sa bukatar kulawa kamar kaji."
Shawarar da ta dauka ta biya ta, kamar yadda ya ke biyan sauran masu kiwon ɓeraye zabiya irinta.
Baya ga dakunan gwaje-gwaje na kimiyya, akwai wata sabuwar kasuwa da take tasowa a Tanzaniya na ɓerayen zabiya, sannan gidajen namun daji a wasu lokutan a kasar suna amfani da wadannan ɓerayen da ake siyarewa a kasuwa a matsayin abinci wa macizai, yanayin da ke ƙara bunƙasa kasuwar.
Ire-iren wadannan bukatu ke sanya leah kasa iya cika bukatun duka kwastomominta.
Ta dade tana ƙoƙarin shawo kan wasu daga cikin al'ummarta, musamman mata, su yi kiwon berayen zabiya don suma su ci amfani.
"Ina son iyaye mata sosai. Don haka, idan na samu wata dama, nake kokarin ganin suma sun amfana," a cewar Leah a hirar da TRT Afrika ta yi da ita.
"Kadan daga cikin masu kiwo da ake da su a yanzu ba za su iya biyan yawan bukatun da ake samu ba, ana kara samun sabbin makarantu, sannan gwaje-gwajen kimiya na kara ƙaruwa. Ina ganin kasuwar tana kara samun ci gaba."
Cibiyar SUGECO da daliban da suka kammala karatu a Jami’ar Aikin Gona ta Sokoine suka kafa, ta na iya bakin kokarinta wajen kawar da rashin fahimta da ake samu game da kiwon berayen zabiya.
"Kiwon farin ɓeraye baya haifar da haɗari ga lafiyar masu kiwonsu ko muhalli saboda ana yin komai a wurin da aka keɓe wanda ake da iko da shi," in ji ta.
"Kawai mai kiwo na bukatar ya tabbatar da tsabta a kowane lokaci kuma ya ba da magungunan berayen kamar na kashe tsutsotsin ciki da na ƙwari a daidai lokacin da aka tsara.''