Bayan rushewar gwamnatin Habre a karshen shekarun 1990, gwamnatin soji ta wannan lokacin ta nuna bukatar dake akwai na hada kan dukkan al’umar Chadi kan manufa daya, domin a sake zayyana taswirar makomarsu da za ta hada dukkan ‘yan kasar a harkokin jagoranci.
Hakan ya sanya a 1993, aka shirya babban taron mulkin kasa, inda aka tattauna dukkan batutuwa tare da samun wakilcin kowanne bangare. A karshen wannan babban taro, an rubuta sabon kundin tsarin mulki.A lokacin, dukkan ‘yan siyasar Chadi da suka gudu zuwa kasashen waje sun halarta tare da bayar da gudunmowa ga taron.
A zamanin mulkin tsohon Shugaban Kasar Chadi Idriss Deby Itno (wanda aka kashe a fagen daga a watan Afrilun 2021 sakamkon harin kungiyar ‘yan tawaye ta FACT), ‘yan adawa sun sake neman irin wannan abu. Amma maimakon a zauna a yi sulhu, sai aka samar da wasu kwamitoci a 2018 da 2020. Amma sai ‘yan adawa suka ki halartar tarukan kwamitin guda biyu.
Bayan shudewar Idriss Deby sai maganar sulhu ta sake dawowa kan tebur.
Domin tabbatar da an shigar da kowa wannan sulhu da tattaunawa, sai wani abu na wajibi ya bulla. Shi ne batun samar da gwamnatin hadaka tsakanin ‘yan siyasa da farar hula. Wannan ne ya haifar da tattaunawar Doha.
Taron Doha na ‘Yan kasar Chadi ne,
Shudewar Idriss Deby ta sake dawo da tambayar zama a teburin Sulhu.
Domin ganin wannan zama na Sulhu ya tafi da kowa, wani abu na dole ya bijiro. Shi ne batun cakuduwar sojojida ‘yan siyasa a sha’anin gudanarwa. Wannan ne ya haifar da tattaunawar Doha.
Doha ta ‘yan kasar Chadi ce, babbar jigon nasarar “sulhun kasa da ya hada da kowa”.
Tun ranar 13 ga Maris aka samar da ita, amma sai a ranar Litinin 8 ga Agusta aka sanya hannu kan yarjejeniya tsakanin ‘yan siyasar soji da gwamnatin rikon kwarya a gaban Shugaban Rundunar Soji Janaral Mahamat Idriss Deby Itno, Shugaban gwamnatin rikon kwarya ta soji.
Daga cikin kungiyoyin gwagwarmaya 52 da aka raba zuwa gida uku (Rukunin Rome, Rukunin Doha da Rukunin Qatar), kungiyoyi 43 sun sanya hannu kan takardun yarjejeniyar da aka kulla mai taken “yarjejeniyar zaman lafiya”. Sauran kungiyoyi 19 suna da ra’ayin cewa ba a cika sharuddan da aka zayyana ba. Suna son a nan gaba su ga Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya ta Soji ya nuna ya damu da aiki da yarjejeniyar tare da mika mulki ga farar hula, ya kawo karshen tasa gwamnatin ta riko, kuma kar ya tsaya takarar neman shugabancin kasar.
A gefe guda kuma, ‘yan adawa na ta daga muryoyi suna cewa wannan tambayar ta shafi kowa, a saboda haka a adana ta sai ranar yanke hukunci.
Bayan dawowar Mahamat Idris Deby Itno daga Doha, an tarbe shi da kade-kade da raye-raye, saboda a wajen mutane da dama, wannan matakin babban abu ne ga makomar Chadi, kuma ana jiran tafiya tare da sauran ‘yan adawa da ba su saka hannu kan yarjejeniyar ba.