Tunanin hadin kan Afirka ya ta’allaka kacokan kan ingancin hanyar da ake bi don tabbatar da hakan  / Photo: AA

Daga Yohannes Habteselassie Adhanom

A 1997 Mwalimu Julius Nyerere a Babban Dakin Taro na Gundumar Asmara babban birnin Eritiriya ya bayyana cewa kasashen Afirka na da junansu ne kawai don hada kai wajen tsira da ci gaba.

Ya bayyana hakan ne bayan yin bayani kan yadda kasashen Yamma da Gabas suke da manufofi da Afirka ta kasa tsinkayen su.

Ya bayyana bukatar lallai ‘yan Afirka su hada kai waje guda wanda wannan kadai zabin da ya rage musu.

Tunanin hadin kan Afirka ya ta’allaka kacokan kan ingancin hanyar da ake bi don tabbatar da hakan.

Hadin kan Afirka zai tabbata ne idan har idan kasashen nahiyar 54 suka bai wa masu jefa kuri’a a nahiyar su bayar da gudunmowa wajen kawo cigaban kowacce kasa.

Sannan ne kasashen Afirka za su iya aikin samar da hadin kai da zai amfani juna, wanda zai karfafa kowanne bangare, kuma mai bayar da gudunmowa ga manufar zaman lafiya a duniya.

Akwai wasu hanyoyi na somin tabi a bangarorin alakar tattalin arziki da wasu kawancen tsaro na yankuna da za su iya taimaka wa wajen cimma wannan manufa.

Amma babban abun da zai kawo hadin kan shi ne idan kowacce kasa ta Afirka ta bayar da fifiko wajen yin aikin kawo cigaba a cikin dukkan kashen nahiyar.

Manufar hadin kan Afirka da hanyar da za a tabbatar da hakan na da matukar muhimmanci ga ‘yan Afirka baki daya.

Bukatar shugabanni

Amma bai kamata bukatar shugabanni ta zama ita ce kadai jigon neman hadin kan nahiyar Afirka ba. Ya zama dole ‘yan Afirka su fahimta tare da amince wa da wannan.

Ya fi kyau a mutu don kare ‘yancin alummar Afirka kamar yadda Patrice Lumumba Thomas Sankara da Hamid Idris Awate suka yi/Hoto AP

Ya zama dole a yada manufa da hanyar tabbatar da ita a dukkan kasashen Afirka.

Dole a yi muhawara tare da fahimtar su ta yadda za su fahimci mene ya kamata su yi a kasashensu ton tabbatar da wannan manufa.

Tarayyar Turai za ta iya zama abun misali. Kungiyar da ta kunshi kasashe ‘yan jari hujja wanda har yanzu suna da sauran aiki don inganta tsarin.

An dauki shekaru ana gwagwarmaya kuma ana bukatar aiki tukuru don dorewa da inganta gwagwarmayar.

Mafi yawan kasashen Afirka na fama da matsalolin siyasa da tattalin arziki. Siyasarsu na yin tasiri kan tattalin arzikinsu da kuma walwalar jama’arsu.

Hukumomin gudanarwa da kungiyoyin farar hula na da rauni ko ma a wasu wuraren babu su gaba daya. Babban abun tambayar shi ne me ya sa wadannan matsaloli suke ci gaba da wanzuwa.

Amsar na iya bambanta idan aka dauki kowacce kasa ita kadai. Amma babbar matsalar da ta ke a ko ina ita ce ta rashin samun jagororin da suke da kishin bautawa mutane da saka bukatun al’umma a gaba da nasu.

Shugaban masu fifita bukatar mutane sama da tasu na iya zama abun misali, ta hanyar yadda suke bai wa al’umma damar amfana da arzikin da suke da shi inda za su bai wa dukka jama’a damar a dama da su a dukkan bangarorin kawo ci gaba sannan a bayar da fifiko ga ilimi da lafiya da jin dadin jama’a.

Zaman lafiyar da Nyerere ya gani ya wanzu a kasar da ke yankin da ake kira kahon Afirka bayan shekaru 30 da kawo karshen yakin kwatar ‘yancin kai daga Itopiya ne yake karfafa masa gwiwa game da zaman lafiyar Afirka.

Wata gaba da take da muhimmanci da tabo a Asmara a 1977 ita ce cewa zaman sa a kan mulkin Tanzaniya tsawon shekeru 27 ba dai dai ba ne.

Nyerere na jaddada cewa lallai bai dace shugabanni su zauna a kan mulki tsawon lokaci haka ba. Daya daga cikin matsalolin shugabannin a Afirka wanda hakan ya janyo tsaiko a cikas wajen cigaban kasashensu.

Rayuwa da gwamnatoci da dukkan komai sun ta’allaka ne ga sauyin da ake samu, amma ba dukkan shuganannin Afirka ne suke tunanin akwai wasu irin su da suke da tunani, tsarin kawo cigaba da dabarun jagoranci sama da nasu ba.

Shugabanni da dama sun yi kira ga hadin kan Afirka a shekarun da suka gabata, amma wannan batu ya dinga tafiyar hawainiya.

Kamar dai Tarayyar Afirka ta zama mafarin hakan, abun takaici sai ya zama ba ta da wani abun nunawa saboda kowacce kasa taki sauke nauyin da aka dora mata.

To mece ce babbar rashin nasarar kasashen Afirka? Rashin kyakkyawan shugabanci. Kasashen Afirka sun rasa shugabannin da za su samar da ingantattun hukumomi da dokoki.

Kasashen Yamma suna kiran dokokin Afirka da aka samar kafin mulkin mallaka da sunan ‘Customary laws’ (Dokokin Al’ada) domin nuna su a matsayin kaskantattu ko marasa daraja idan aka kwatanta su da nasu dokokin, Amma doka, doka ce.

Dokokin da suka assasa tushen shari’a da jagoranci da suka wanzu daga karni na 13 zuwa na 19 a Eritiriya sun zama abun misali.

A yankin arewacin Eritiriya, al’ummar Sebderat na da tsarin jagoranci da zai iya zama mai daraja da inganci kuma ya wakilcin dukkan Afirka a yau.

Jama’a ne kadai suke iya cire masu bayar da shawara ga zababben shugaba.

Tsari mai taimakon jama'a

Tsarin na taimakawa mutane wajen juya shugabansu, saboda shugaban bai isa ya kori wani mai ba shi shawara ba.

Wannan na hana shugaban samun ‘yan amshin shata a tare da shi da kuma gudanar da kama-karya.

Ya wajaba matasan Afirka su yi kokarin taka rawar a zo a gani da kafa tarihi a kasashensu a wannan zamani na sadarwa/Hoto AP

Misalan da za su iya taimaka wa wajen samar da dokoki da suka dace da Afirka na nan a dukkan yankunan nahiyar.

Sanin ilimin yankunan da amfani da yarukan kasashen na asali don fahimtar dokoki da ka’idojin jagoranci za su yi amfani sosai.

Bukatar karfafa ilimin jama’a game da jagoranci da tsaffin dokoki na kaka da kakanni na sanya a fahimci dokikin cikin sauki, a kiyaye su tare da ci gaba da gina su. Amma hakan ba ya nufin koyon wasu yarukan ba shi da muhimmanci.

Babban dalilin da ya sanya yaren asali yake da muhimmanci shi ne yadda mutane suka riga suka san falsafa, dokoki da yanayin zamantakewarsu da yarensu na asali sama da yaren da suka koya daga baya.

Tabbas gaskiya ne Afirka na tafiyar hawainiya wajen ci gaba, duk da akwai hanyoyi da arzikin da za a yi amfani da su don kawo cigaban cikin sauri.

Wajabta samun ingantaccen ilimi da tabbatar da kafafen yada labarai masu ‘yanci da kula da lafiyar jama’a zai iya kubutar da kasashen Afirka daga rushewa.

Sannan a samu kariya daga taimakon kasashen waje da kulle-kullensu, kamar yadda aka gani ba da jimawa ba. A koyaushe dan kasa mai ilimi zai dinga tabbatar da an samu zaman lafiyar kasa.

Ya fi kyau a mutu don kare ‘yancin alummar Afirka kamar yadda Patrice Lumumba Thomas Sankara da Hamid Idris Awate suka yi, sama da a mutu ana yaudara da zabgawa al’umma karya da alkawuran da ba a cika musu.

Ya wajaba matasan Afirka su yi kokarin taka rawar a zo a gani da kafa tarihi a kasashensu a wannan zamani na sadarwa, wanda ake runguma a matsayin ‘Sanya idanu Kan Jari Hujja’.

Ya kamata su yi aikin gina al’ummunsu bisa doron inganta hanyoyoin kula da lafiya da faranta rai da cigaban muhalli don ingantuwar Afirka.

TRT Afrika