Daga Mpoki Thomson
A shekarar 2019, na halarci taron bitar koyar da kwarewa kan sanya hannun jari, wanda kamfanin Sahara Ventures suka shirya. Wannan kamfani da ke Dar es Salam a Tanzania, ya kware ne kan kirkira da fasaha, da kuma sana’a.
Babban bako mai jawabi a wajen ba wani ba ne illa sanannen mai zuba jarin nan dan Afirka ta Kudu, wato Vusi Thembekwayo. Duk da cewa taken taron shi ne “Fikirar Cigaba da kuma Sana’a”, taron ya bar ni ne da tambayoyi masu yawa ba tare da samun amsoshi ba.
Vusi ya yi bayani cikin hikima kan yanayin da ke shafar sabbin kamfanoni a Afirka, da kuma irin nisan da muka yi a fannin ya zuwa yau.
Ya tabo wasu batutuwa masu sarkakiya da suke hana cigaban sabbin kamfanoni. Sannan ya bayar da misalai kan darassun da za a koya daga gazawa da kuma cigaba.
Sai dai wani abu da ya ja hankali a maganganunsa shi ne fahimtarsa ga matasa masu shiga sana’a a fannin fasaha, wadanda suka zo daga yankin Gabashin Afirka.
Ra’ayinsa shi ne ba a bukatar kamfanonin da ke Afirka su yi tunanin za su iya kwafar tsarin zuba jari irin na cibiyar fasahar nan ta Silicon Valley da ke Amurka.
Wani abu kuma da ya tabo, wanda yake yi wa mutane kaikayi shi ne yalwar fahimtarsa kan yadda kamfanonin Afirka suke neman kwaikwayar tsarin zuba jari na kasashen Yamma.
Wannan batu ya kasance dadadde, kuma ana ganin yana faruwa ba wai kawai a fannin kamfanoni masu shiga sabuwar harka ba, har ma ya watsu a fannonin tattalin arziki daban-daban.
Afirka na kokarin nacewa salo da tsarin kasashen Yamma, wadanda a zahiri ba su kamaci nahiyar ba.
Cigaban da Afirka ta cimma cikin shekarun nan a harkar fasaha da sauran fannonin cigaba zai zama ba a girmama su ba, idan muka bar al’adun da suka sabawa namu suka zama su ne alkiblarmu wajen fayyace mene ne cigaba.
Sai dai kash, wannan dogaro kan al’adun kasashen Yamma ya yi kama da abin da aka saba gani a duk harkokin zuba jari. A shekarar 2022, sabbin kamfanoni sun samu zuba jari na dala biliyan 500, wanda kaso mafi tsoka ya tafi ga harkar fasahar hada-hadar kudi.
Sai dai kuma, wani abin damuwa shi ne yawancin kudaden sun
A bayyane yake cewa masu zuba jari daga kasashen waje sun mamaye fagen masu karfin jari a nahiyar Afirka. Kuma su ke samar da tsabar kudin da ake bukata don assasa kamfanonin cikin-gida.
A cewar rahoton Bankin Cigaban Afirka na 2021, kashi 90 cikin 100 na zuba jari a harkokin fasaha a nahiyar, sun tafi ne zuwa kasashen Kenya da Nijeriya da Masar da Afrika ta Kudu.
Cikin tsawon shakaru, hamshakin kamfanin fasahar nan na Amurka wato Google, ya samar da irin jarin da ba ya bukatar kamfani ya kawo nasa, ga kamfanonin Afirka da ke matakin farkon shiga kasuwa.
Wani kundin bayanai na wata-wata kan nazari game da zuba jari a sabbin kamfanoni a Afirka, wanda aka yi wa lakabi da “Africa: The Big Deal”, ya bayyana cewa a shekarar 2022 kawai, Google ya zuba jarin dala miliyan hudu cikin sabbin kamfanoni 60, ta hanyar Gidauniyar Bakake Masu Kafa Kamfani.
Abin da ke ci gaba da takure matsayin Afirka wajen kokarin kwaikwayon tsarin kasashen Yamma a harkokin kasuwanci shi ne, shida cikin manyan masu zuba jari a sabbin kamfanonin Afirka 10, kamfanonin kasar waje ne.
Neman zuba jari daga kasashen waje ya ma zarce kamfanoni masu zaman kansu. Gwamnatoci da cibiyoyin gwamnati su ma sun rungumi tagomashin cigaban da sabbin kamfanonin Afirka suke da shi.
Idan muka koma kan abin da Vusi ya fada game da abubuwan da ke mayar da sabbin kamfanonin Afirka baya, wani babban musabbabi shi ne burin girma cikin sauri ta hanyar samo masu zuba jari.
Wannan kwararren mai zuba jari wanda ya san gaba da bayan wannan harka, ya yi imanin cewa mafita ga matsalolin zuba jari da kasuwanci a Afirka ya dogara ne kan ko Afirka ta shirya bude kofofinta na kasuwanci.
Shi yana goyon bayan Afirka ta zamo maras shingaye, ta yadda kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar zai kasance ba ya samun cikas a zahiri daga kalubalen haraji ko wadanda ba na haraji ba.
Idan za mu sanya wannan batu kan sikelin sabuwar Afirka mai fayyace makomarta, wannan zai bude wata muhawara kan me ya sa nahiyar ta kasa nemar wa kanta ‘yanci daga kasashen da suka garkame ta a baya.
Har zuwa yau, Afirka na ci gaba da bin akalar manyan kasashen Yamma ne. Idan aka duba mahangar siyasar duniya da ta tattalin arziki, muna ci gaba da dogaro kan wasu daga waje, yayin da muke yunkurin daukar mataki kan abin da zai kawo mana cigaban makomarmu.
Kenan, a sanda masanin kasuwanci ya fadi fahimtarsa, wadda take bayyana kashin gaskiyar matsalar Afirka ta dogaro kan tallafi da jin kai daga kasashen waje, hakan na kara zuzuta dadadden kalubalen nan na cewa: “Afirka na bukatar mallakar makomarta.”
Kamfanonin duniya irinsu Google za su ci gaba da sanya idanunsu kan neman riba daga Afirka.
A irin tsarin duniya na yau, masu karfi su suke ci gaba da kara karfi. Shin mun shirya sauya salon rayuwarmu da tunaninmu na ganin sai sun dace da akidar kasashen waje?
Wannan batu a kashin kansa, wani salon dunkufarwa ne da ya hana maza da matan Afirka sanin matsayinsu a duniya.
Za mu ci gaba da cutar da kanmu, matukar ba mu fara kallon Afirka a matsayin nahiyar da ta bambanta da sauran sassan duniya ba. Akwai hikima kan cewa a yau ana kallon Afirka a matsayin inda makomar cigaban duniya zai kasance.
Tabbas akwai hikima game da yadda sauran nahiyoyi suke tururuwa zuwa Afirka don kokarin inganta makomarsu.
Da zarar mun fahimci cewa matsalar guda ce, za mu rungumi bambance-bambancenmu wanda yake ci gaba da fayyace ainihin su wane mu, da kuma damarmakinmu.
(Mpoki Thomson dan jarida ne mazaunin birnin Dar es Salaam)