FIFA ta yi iƙirarin cewa ba ta son shiga cikin lamuran siyasa - amma wannan dalili ne? Siyasa tana shafar kowane fanni na rayuwa, har da wasanni.

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya ta sake jinkirta yanke hukunci kan ƙorafin Falasdinawan na haramta wa Isra'ila shiga wasannin duniya saboda mummunan yaƙin da take yi a Gaza.

Sai dai a wani ɗan rangwame, ta buƙaci a gudanar da bincike na ladabtarwa kan yiwuwar nuna wariya da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Falasdinu (PFA) ta yi zargin an yi mata.

FIFA ta yi iƙirarin cewa ba ta son shiga cikin lamuran siyasa - amma wannan dalili ne? Siyasa tana shafar kowane fanni na rayuwa, har da wasanni. Kasancewar kungiyoyin wasa na Isra'ila a matakin duniya da na ƙasa na aikewa da sako mai karfi cewa tashe-tashen hankula na ƙasashe abu ne na al'ada kuma ana iya yin watsi da su. Wannan ba abin yarda ba ne.

A yayin wani taron majalisa a Zurich, jami'an FIFA a ranar Alhamis sun nuna cewa ba su cim ma matsaya ba kan bukatar Palasdinawa na dakatar da Isra'ila daga hukumar. Sanarwar ta gamu da takaici da fushi da yawa daga cikin al'ummar wasanni.

A lokacin da yake zantawa da TRT World, Abubaker Abed, matashin dan jarida kuma mai sharhi kan harkokin wasanni na Falasdinu daga Gaza, ya ce, "Ta hanyar ɗage matakin da ta dauka, FIFA ta sake amincewa da ƙa'idoji biyu da munafunci. An lalata dukkanin kayayyakin wasanni kuma an kashe 'yan wasan kwallon kafa sama da 305, FIFA ba za ta iya daukar tsayuwar daka ba ta haramtawa Isra'ila."

Ya kara da cewa amma a kan batun Rasha, cikin kwana uku kacal hukumar ta FIFA ta dauki matakin ƙaƙaba wa Rasha takunkumi bayan ta mamaye Ukraine a shekarar 2022.

"Dagewar da FIFA ta yi na iya gaya mana cewa duk fargafagandar da ake yadawa da sunan 'daidaito' faɗa ne kawai."

Tausayin da ƙasashen duniya suka nuna wa Ukraine idan aka kwatanta da shirun da suke yi a kan lamarin Falasdinu na nuna cewa munafunci ne zalla da fuska biyu daga FIFA.

Yanzu ya zama wajibi a tambayi jami'ai a FIFA da UEFA da hukumomin kwallon kafa na kasashe da sauran kungiyoyi cewa ina suka ɓuya a lokacin da ake batun daukar ƙwararan matakai kan Isra'ila kan laifukan yaƙi da ta aikata.

Bincike

Hukumar ta PFA ta fara gabatar da shawararta ta dakatar da Isra'ila a taron FIFA da aka gudanar a watan Mayu, inda FIFA ta ba da umarnin tantance shari'a cikin gaggawa tare da yin alkawarin magance lamarin a wani taron na musamman na majalisarta a watan Yuli.

Amma a watan Yuli, FIFA ta ce a yanzu za a aika tantancewar shari'a ga majalisarta a ranar 31 ga Agusta, tana mai zargin cewa: "Bayan buƙatun neman tsawaita wa ɓangarorin biyu na gabatar da mukamansu, wanda FIFA ta ba su, ana buƙatar ƙarin lokaci don kammala wannan tsari tare da kulawar da ta dace."

Sai dai a cewar mutanen da ke da kusanci da batun, tuni aka kai rahoton ƙwararrun shari'a na FIFA ga hukumar, mako guda kafin wannan sanarwar.

Yanzu ya zama wajibi a tambayi jami'ai a FIFA da UEFA da hukumomin ƙwallon ƙafa na kasar da kungiyoyin inda suka ɓuya a lokacin da ake batun daukar kwararan matakai kan Isra'ila kan laifukan da ta aikata.

A hedkwatar kungiyar da ke Zurich a ranar Alhamis, Majalisar FIFA ta amince da shawarwari da kuma matsayar da aka cim ma a cikin nazarin shari'a.

"Kwamitin ladabtarwa na FIFA zai fara gudanar da bincike kan laifin nuna wariya da hukumar kwallon kafa ta Falasdinu ta yi," in ji FIFA a cikin wata sanarwa.

Haka kuma za a gudanar da bincike a kan halartar Gasar Ƙwallon Ƙafa ta Isra'ila na kungiyoyin Isra'ila da ake zargin suna da sansani a yankunan Falasdinawa.

Shugaban hukumar ta FIFA Gianni Infantino ya ce majalisar ta bi shawarar ƙwararru masu zaman kansu.

"Tashe-tashen hankulan da ke faruwa a yankin ya tabbatar da cewa, fiye da dukkan la'akari, kuma kamar yadda aka bayyana a taron FIFA karo na 74, muna bukatar zaman lafiya. Yayin da muke ci gaba da kaɗuwa da abin da ke faruwa, kuma zuƙatanmu suna tare da wadanda ke shan wahala, muna kira ga kowa da kowa. dukkan ɓangarori don dawo da zaman lafiya a yankin nan take,” ya ƙara da cewa.

Hukumar ta PFA ta zargi hukumar kwallon kafar Isra’ila da hada baki da gwamnatin Isra’ila wajen keta dokokin kasa da kasa ta hanyar nuna wariya ga ‘yan wasan Larabawa.

"FIFA allowed Israel FA to continue using Palestinian territory as its own, and football as an instrument of colonial expansionism. It makes FIFA complicit in human rights violations, illegal occupation and apartheid" said Katarina Pijetlovic, head of the PFA’s legal department, after FIFA deferred a ruling again.

"FIFA ta amince da hukumar FA ta Isra'ila ta ci gaba da yin amfani da yankin Falasdinu a matsayin nata, da kuma kwallon kafa a matsayin wani makami na fadada mulkin mallaka.

"Hakan ya sanya FIFA ta shiga cikin take hakkin bil'adama, mamayewa ba bisa ka'ida ba da kuma wariyar launin fata", in ji Katarina Pijetlovic, shugabar sashen shari'a ta PFA, bayan da FIFA ta sake jinkirta hukuncin.

Matsayin "tsaka-tsaki" na FIFA game da kungiyoyin ‘yan kama-wuri-zauna da ke shiga Gasar Lig ta Isra'ila ya tabbatar da jigon jagorancinta, wanda ke nuna son kai ga Isra'ila.

FIFA ta gaza bayar da jadawalin ranar Alhamis na lokacin da za a kammala sabon binciken.

MDD ta sa baki

A martanin da FIFA ta fitar, wata kungiyar kwararrun kare hakkin dan'adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce an gano akalla kungiyoyin kwallon kafa takwas da ke taka leda a matsugunan da Isra'ila ta mamaye a Yammacin Gabar Kogin Jordan.

"Irin wannan hadaka da kuma dabi'ar da ake yi a cikin hukumar ta IFA ya kai matsayin amincewa da doka kan lamarin da ya biyo bayan kasancewar Isra'ila a yankin Falasdinawa da ta mamaye. Wannan kuma ya saɓa wa dokokin kasa da kasa," in ji ƙwararrun.

Sun bukaci FIFA da ta tabbatar da aiwatar da manufofinta na rashin ɗaukar raini da nuna wariya idan ana batun Isra'ila da yankunan Falasdinawa da ta mamaye.

"Muna tunatar da FIFA cewa dokokin kare hakkin bil'adama na kasa da kasa, wadanda suka hada da 'yancin cin gashin kansu, da kuma haramta wariyar launin fata, sun shafi kungiyoyi masu zaman kansu na kasa da kasa, musamman ma wadanda ke da hurumi a duniya da kuma aiki irin su ita kanta. Sannan kuma ta cika nauyin da ya rataya a wuyanta na mutunta hakkin dan'adam,” in ji su.

Sun yi kira ga hukumar ta FIFA da ta tabbatar da cewa hukuncin da ta yanke ya yi daidai da ka'idojin dokokin kasa da kasa da ba su da tushe.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun dade suna Allah-wadai da Isra'ila saboda mamaya da kuma zaluntar al'ummar Falasdinu bisa tsarin mulkin wariyar launin fata da bai dace ba.

Gwamnatoci da hukumomin MDD da kungiyoyi masu zaman kansu sun kuma zargi Isra'ila da aiwatar da kisan kiyashi kan al'ummar Falasdinu a lokacin da take mamaya da kai hare-hare a Gaza, wanda ta fara bayan ranar 7 ga watan Oktoba.

Dabarun tsokana

Sa'o'i kadan bayan matakin da FIFA ta dauka na dakatar da Isra'ila, hukumomin Isra'ila sun tsare Firas Abu Hilal, sakatare-janar na PFA na wani dan lokaci.

"Tsarewar da aka yi wa Sakatare Janar na fiye da sa'o'i hudu wani bangare ne na cin zarafi da yawa da mamayar da ake yi wa wasannin Falasdinu," in ji PFA a cikin wata sanarwa da aka wallafa a X.

Rashin hadin kai da matakin na FIFA bai takaita ga yankin Falasdinu kadai ba.

A cikin 'yan watannin nan, mun ga yadda FIFA da UEFA suka hana 'yan wasa da sauran jama'a da ke goyon bayan Falasdinu "rikitar wasanni da siyasa" tare da kasa yin Allah wadai da cin zarafin 'yan wasan da ke goyon bayan Falasdinawa.

A farkon watan Satumba, dan wasan kwallon kafa dan kasar Chile da Falasdinu, kuma tsohon dan wasan kasar Falasdinu Yashir Islame Pinto, ya bayar da rahoton cewa dan wasan Brazil Dennis Murillo ya kira shi da "dan ta'adda" a lokacin wasan kwallon kafa a gasar ta Thailand.

Bayan da aka shigar da ƙara a hukumance, FIFA ta yanke hukuncin hukunta Murillo ta hanyar dakatar da shi na wasanni uku, inda daga baya aka rage bugun fanareti zuwa biyu – da kuma hukunta Yashir da kansa kan martanin da ya yi.

Mounting toll

A cikin shekarar da ta gabata, sama da mutum 41,000 da suka hada da kananan yara 16,000 ne sojojin Isra’ila suka kashe a Gaza, sannan sama da Falasdinawa 89,000 ne suka jikkata, yayin da ake fargabar akalla mutum fiye da 10,000 har yanzu suke binne a karkashin baraguzan gine-gine.

A cewar PFA, akalla 'yan wasan kwallon kafa 305 ne aka kashe a yakin kisan kare dangi na Isra'ila, ciki har da yara 84 da ke cikin makarantun kwallon kafa na matasa na Gaza.

An rusa kayayyakin wasanni, inda Al-Dorra ya kasance filin wasa daya tilo a Gaza, wanda yanzu ya zama mafaka ga dubban Falasdinawan da suka rasa matsugunansu. An kuma dakatar da ayyukan gasar kwallon kafa ta Gaza tun daga lokacin.

Kungiyar kwallon kafa ta kasa ba ta samu damar karbar bakuncin wasa a gida ba cikin kusan shekaru biyar - ma'ana an tilasta wa kungiyar buga wasannin share fage a kasashen ketare ba tare da magoya baya masu karsashi da murna ba, a yayin da ake fama da tashe-tashen hankula da ƙaurace wa gida da kuma raunin da ya faru a gida.

Duk da haka, tawagar kasar Falasdinu, wadda aka fi sani da Al-Fedayeen, na ci gaba da haɓaka.

A halin yanzu tana taka rawa ta tarihi a cikin shirin neman cancantar shiga Gasar Cin Kofin Duniya na 2026 na Asiya.

Ta karbi bakuncin Jordan makonni uku da suka gabata a Kuala Lumpur na kasar Malaysia, kuma za ta buga wasa a Iraki ranar 10 ga watan Oktoba, sannan za ta karbi bakuncin Kuwait bayan kwanaki biyar a Doha na Qatar.

Marubuciyar maƙalar Leyla Hamed haifaffiyar kasar Sifaniya ce kuma asalinta 'yar jarida ce a fannin ƙwallon ƙafa a Moroko, kuma ƙwararriya a fannin shari'a a Burtaniya. A halin yanzu tana aiki a matsayin edita, marubuciya, mai magana a The Athletic, wadda ke aika rahotanni a kan Gasar Premier ta Ingila.

TRT Afrika