Zoey Seboe ta tuna lokacin da take makarantar firamare da wani ɗalibi ya yaye mata ɗankwalinta, har wani daɓaɓare-daɓɓare mai kama da tabon ƙunar wuta da ke kan wuyanta har zuwa ƙasa ya bayyana.
Matashiyar mai shekara 24 ba ta iya tuna cewa ko tun daga wancan lokacin ne ta fara jin cewa gara kawai ta bar jikinta a gan shi a yadda take maimakon ta yi ta ɓoye-ɓoye saboda gudun mutane su ƙyame ce ta.
A lokacin da ta shiga ajin ƙarshe na sakandare, Zoey ta samu ƙwarin gwiwa sosai wajen ƙirƙirar wani abu na kwalliya da za ta dinga rufe kanta da shi, ta hanyar amfani da ƙarin gashi maimakon yawan kima ɗankwali da take yi “don samun sauyi.”
A lokacin da ta kai shekara 22, ta halarci Gasar Sarauniyar Kyau ta Afirka ta Kudu cikin isa da taƙama.
Labarin Zoey abin ban sha’awa ne saboda an haife ta da wata cutar fata da ake kira lamellar ichthyosis, wata cuta da ke mayar da fata tamkar wacce ta ƙone kuma ƙonanniyar fatar ba ta zubewa da wuri.
Kimiyyar lafiya ta bayyana cutar da cewa idan dabbare-dabbaren ya fito a kan fata, to akwai wasu ƙayoyin halitta da suke sa fatar ba za ta kakkaɓe don mai kyau ta sake fitowa ba.
Duk da yarda da kanta da kuma ɗaukar ƙaddararta, Zoey ta tabbatar da cewa rayuwa da wannan cuta ba abu ne mai sauƙi ba, saboda cutar na kuma rage yawan gumin da jiki ke fitarwa tare da saka shi saurin jin zafi musamman idan ana gaban wuta.
Don kare kanta daga waɗannan abubuwa, sai take yawan saka kaya masu dogon wuya da hannu da ma waɗanda za su rufe mata jikinta ruf gaba ɗaya.
Ta shaida wa TRT Afrika cewa “Wannan cutar ba ta sa ina ji na daban ba saboda ba na damun kaina da ita.”
“Wataƙila, na sha bamban da sauran mutane, amma cutar ba ta tasiri kan kasancewa ta mutum.”
Bai faye faruwa ba
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce cutar fata ta lamellar ichthyosis na shafar aƙalla mutum daya a cikin 200,000 a fadin duniya.
"Fatar mutum ce take tattarewa ta yi dabbare-dabbare kamar na ƙuna, kuma ba ta saɓewa," kamar yadda wata ƙwararriyar likitar fata a Afirka ta Kudu Dr Lerato Masemola ta faɗa.
Duk da cewa cutar ba ta da magani, yawan goge wajen da shafa masa mai na iya hana fatar yawan bushewa.
Zoey ta ce "ya danganta da yanayin da ake ciki, amma ina iya shafa mai a jikina kamar sau shida a rana a lokacin sanyi, sau takwas kuma a lokacin zafi."
"Baya ga shan magungunan da aka ba ni a asibiti, dole kuma ina amfani da mayukan kare ƙunar rana saboda kauce wa yawan jin ƙaiƙayi da kuma suɗewar fata.
Sannan kuma mutanen da ke da cutar ichthyosis n ayawan fama da zubewar gashi, inda sumar ke wahalar fitowa.
"A da can, mata da yawa a Afirka kan ɗaura ɗankwali ko su naɗa gyale a kansu a matsayin martaba kai da mutuntawa da kuma rufe sirrin gashinsu.
"Ina ɗaura ɗankwali ne saboda cutar nan ta jawo duk gashina ya zuce, Don haka sa ɗankwalin shi ne kawai yake sa na ji daidai," Zoey ta shaida wa TRT Afrika.
Rungumar ƙaddara
Duk da irin cin zali da ƙyamar da ta dinga fuskanta a makaranta, akwai abubuwan dadi sosai da Zoey ke tunawa na rayuwar makaranta.
"A lokacin da nake ajin ƙrshe a sakandare, ba na samun isasshen lokacin wanke 'yankwalayena saboda ayyukan aji. A lokacin ne na fara saka ƙarin gashi kuma sai ƙawayena suka dinga yaba kyan da ya yi min.
"Kuma ni ma sai na ga ya yi min kyau ɗin," matashiyar ta tuno.
"Ba lallai ne shi ne irin salon gyaran gashin da wasu za su so yi ba, amma dai a lokacin ni ya dace da ni."
Yayin da shekaru suka wuce, Zoey ta taso cikin kwarin gwiwa game da kamanninta. Hakan ne ma ya sa har ta yi sha’awar shiga Gasar Sarauniyar Kyau ta Africa ta Kudu, duk da cewa ba za ta iya bayyana kanta sosai a dandalin kamar sauran 'yan takara ba.
"Na samu ƙwarin gwiwar shiga gasar ne bayan da na gane cewa kowace mace na iya shiga. Sai na yi tunanin cewa "idan dai sauran mata za su iya, to ni ma zan iya," ta ce.
Ga mamakinta, sai Zoey ta ga an tantance ta a cikin masu gasar, inda sanar da hakan ya jawo mata tsananin farin ciki.
"Mutane sun yi ta martani mai kyau, inda da dama ke cewa na burge su. Sai dai marasa kirki sun ce na yi kama da maciji.
Mutane da dama sun yi tambaya cewa 'Ta yaya Afirka ta Kudu suka zaɓe ta? Me ya sa za ta yi hakan?' Abin sha'awar shi ne ganin yadda mutane suke mayar da maratani a kan abin da ba su san komai a kai ba.
Zamowarta cikin 'yan takara 30 ya ba ta ƙwarin gwiwar yin tata bajintar da irin halittarta.
"Na san cewa zai yi wahala na kai labari wajen yin nasara a ƙrshe, amma kuma na yi farin cikin cewa shiga ta gasar ma ya nuna wa al'umma cewa kowa na iya taka rawa a komai," in ji Zoey.
Fata da buri
Duk da cewa ba ta ci gasar ba, shigar ta ba ta ƙwarin gwiwar karantar shari'a da kuma fafutukar samar da al'umma da za ta tafi da kowa.
"Ina so na zama lauya, kuma na yi amanna cewa al'umma na samun sauyi cikin sauri ta hanyar karɓar mutane masu wata lalura irin tamu.
Na fi damuwa a kan yadda mutane za su kalli ɗankwalina a irin wannan tsarin na gasar sarauniyar kyau," Zoey ta faɗa da mamaki.
Mutane masu fama da cutar fata ta ichthyosis na buƙatar wani tsari na tallafi, kuma Zoey ta tabbatar da cewa ta yi sa'ar samun 'yan'uwa da ƙawaye da suke goyon bayanta a duk abin da take yi.
Abu ɗaya da take bai wa masu fama da irin cutarta shawara shi ne su guji ƙyamatar kansu.
"Kai za ka jagoranci kanka wajen zama yadda kake so har a karɓe ka a cikin al'umma. Kuma ka yarda da kanka," ta ce.