Daga MARION FERNANDO
Ta yiwu ba ku taba mayar da hankali kan dandazon tantabaru da ke taruwa a manyan gine-gine masu tsawo ko saƙo da lunguna da ke cikin biranenku ba. Amma da za ku yi hakan, za ku lura da wani abu mai matukar mamaki – wadannan tsuntsaye da ke sumumu (shiru-shiru tamkar sai yadda aka juya akalarsu) suna isar da sako kamar yadda kyanwar gida da ke hawa kan cinyarku cikin farin ciki take yi.
Tambayi kowane masanin harkokin rayuwar tsuntsaye ko mai matukar son bibiyar al’amuran tsuntsayen, za su sanar da ku yadda wadannan tsuntsayen, tamkar sauran, ke fitar da sauti da motsin jiki (cara ko kyarkyara), yayin da suka samu nutsuwa, tare da zaƙuwar son zamantakewa ko mu’amala – al’amarin da ke nuni da cewa, mafi yawan lokuta akan same su ne tari guda, tare da sauran abokan huldarsu na dangin tsuntsaye da ke baza fuka-fukai.
Masana harkokin rayuwar tsuntsaye sun yi nuni da cewa, tantabaru su ne rukunin farko na tsuntsayen da mutane suka mayar da su tsuntsayen gida, inda tun farko aka fara kiwata su a matsayin nau’ukan abinci.
A ’yan shekarun nan, kusan ko’ina a daukacin fadin biranen duniya ana ganin tantanbaru na watayawa, tun daga tituna masu kura na Kuala Lumpur zuwa kasuwanni masu dimbin tarihi da shahararrun hanyoyi a birnin Istanbul.
Sannan idan ka ziyarci wurare irin su birnin New York da dandalin shakatawa na birnin Washington ko wajen bude ido na Mumbai da ke kasar Indiya, tantabaru sun kasance wasu muhimman abubuwan da ake gani, wadanda ke ƙayatar da masu yawon shaƙatawa da bude idanu.
Shin mene ne ya sanya ba a cika kula da harkokin tantanbaru ba, duk da cewa, ana ganin tarin dandazon su a kusan ko’ina? Kuma mene ne dalilin da ya sanya wadannan tsuntsayen ke zaune a cikin birni, inda suke gudanar da rayuwarsu tamkar mazaunan birnin tare da abokan zamansu mutane?
Andrew Garn , kwararren mai daukar hoton kafafen yada labarai, kuma marubucin litattafai 12, wadanda suka hada da Tantabarun New York (The New York Pigeon,) ya bayyana wa kafar yada labarai ta Rediyo da Talabijin na Turkiyya (TRT World ) cewa: cikin kalma guda – abinci. Dimbin abincin da ake samu a birane, tare da mutanen da a ko da yaushe a shirye suke su ciyar da su shi ya sa suke a ko'ina.
“Na yi nazarin muhallai ko matsugunai a tsaunin farar kasa da ke kasar Masar, tare da tsaunukan Indiya da biranen duniya daban-daban, tun daga Benice zuwa Siberiya.
"Tantabaru na dada karuwa a birane saboda suna samun sauran abinci da mutane ke ci a rage, sannan mutane suna ba su kulawa,” a cewar masanin, dan asalin New York.
Tushensu daga tsauni guda ne, inda kakannin tantabaru suka fito, nau’ukan wadanda suka fara rayuwa a cikin daji (fera) aka fi samu a fadin duniya a yau. Irin su ba su da wata barazana, su masu jajircewa da ƙwazo ne, domin rayuwarsu da yawansu daidai yake da na tsuntsayen da ake ta’ammali da su a gida, kamar aku da kanari, wadanda rayuwarsu ba ta yi daidai da su (tantanbaru) ba, inda dimbin nazarin da aka gudanar ke nuni da sare itatuwan dazuka da gurbacewar muhalli, har ma da wayoyin tafi-da-gidanka ke bayar da haske kan yadda kananan tsuntsaye ke karewa a mafi yawan biranen duniya.
Akwai nau’uka 300 na tantabaru da aka gano, wadanda suka hada da kurcaccaki, wadanda ke bazuwa a fadin duniya, don haka yawansu ba abin mamaki ba ne, idan aka yi la’akari da yadda tarihi ya nuna irin kauna da mutane suke yi musu.
Nau’ukan Scandaroon da Archangel da Frillack - mabambantan nau’ukan tantabaru da dama sun yadu, tare da sunaye masu kayatarwa, ta hanyar la’akari da launukansu da motsin jikinsu, yayin da wasu suka fi kayatarwa, tamkar nau’ukan tantabarun Fantail ko Jacobins, wadanda ke da adon zayyanar fuka-fukai.
“Tsautsayi ne ya afka musu sanadiyyar asalin rayuwarsu. Domin da sun kasance masu wuyar sha’ani tamkar zalbe da mikiyoyi, mutane da za su shagaltu da son fahimtar tsarin gashinsu da karfin tashinsu,” kamar yadda Garn ya nuna, wanda ya fara daukar hotunan tantabaru bayan da ya kamu da son nazarin wadannan tsuntsayen tsawon shekaru 12 da suka gabata.
“Ina kaunar tantabaru, ina ganinsu kullum, kuma kusan ko da yaushe nakan ceto wadanda suka ji ciwo ko rauni.”
Tsabagen kaunar halittu masu baibaye da gashin jiki ya sanya ya shiga aikin sa-kai na samar da kyautata muhallin tsuntsayen daji da ilimantarwa a wata cibiya da ke karkashin Gidauniyar Wild Bird Fund, “farkon hoton tsuntsayen da ya dauka a can, daga bisani ya zama mai aikin sa-kai, inda ya samu izini a hukumance, wajen tsugunar da tsuntsayen da alkinta tarihi tare da zane-zane a can.”
“A ko da yaushe nakan bai wa kaina aikin dangane da abin da ya dauki hankalina. Wasu ma ba a taba wallafa su ba, wasu kuwa tuni suka zo a litattafai.
Baya ga litattafan da ya wallafa a kan tantabaru, Garn ya wallafa wasu da suka hada da, Brooklyn Arcadia, wadanda ke nuni da makarantar Green-Wood, wani wuri da ke da matukar kayatarwa a Brooklyn, tare da alkinta bayanai na zayyanar gine-gine a tsawon karni dangane da titin jirgin kasa birnin New York.
Kwakkwarar shaida
A zamanin da tantabaru sun kasance wata muhimmiyar hanya ta isar da sakonni. Wadannan tsuntsayen gida ana amfani da su ne a matsayin ’yan aiken kai sakonni a tsakanin kasashe, har ta kai ga an fahimci irin kaifin basirasu. Tamkar dabbobi masu kafafuwa hudu da muke zaune tare da su, tantabaru na iya samun horon kwarewa da kyau.
"Za a iya horar da tantabaru su gano ciwon daji a dodon hoton sassan jiki x-rays, a lokaci guda su tabbatar da abin da ake son fahimta, tamkar kwararre masanin sinadaran sarrafa hoton sassan jikin dan'adam," a cewar Garn.
Ba’Amurke, masanin dabi’un dan'dam B. Frederic Skinner ya shahara wajen koyar da tantabaru yadda za su juya akalar makamai masu linzami. Skinner ya gano cewa, wadannan tsuntsaye za a iya tarairayarsu kan yadda za su juya akalar muhimman ayyuka, wadanda suka hada da wasannin sarrafa sauti na Ping pong.
Bincike ya nuna cewa za su iya fahimtar kalmomi. “Tantabara na da kaifin gane al’amura fiye da kyanwa da kare – suna iya tantance launuka biyar, suna iya bin kadin al’amura ta hanyar sarrafa sauti, da wari ko kamshi, tare da maganadisun da ke sararin duniya,” kamar yadda Garn ya bayyana.
Ya ƙara da cewa, “Su nau’uka guda ne daga cikin halittu biyar (da suka hada da mutane) da ke iya gane kansu a cikin madubi. Karnuka da kyanwoyi ba za su iya ba.
“Tantabaru na kulla alaka da mutane ta hanyoyi daban-daban fiye da karnuka da maguna. Daga cikin al’amuran su ne, suna iya tashi, sannan suna son kasancewa a waje. Mutumin da ya mallaki tantabaru na kulla alaka ne ta hanyar kiransu yayin da suke saman rufin soro, inda za su iya tashi cikin sauki, kuma su dawo."
Suna da juriya ta tsawon lokaci, a mafi yawan lokuta har tafiye suke yi mai nisan zango a daukacin tekuna, kai sun ma kasance wasu jiga-jigai a zamanin daukacin yake-yaken duniya – wasunsu har ma lambar yabo suka samu saboda irin gudunmawar da suka bayar wajen ceton rayuwar dan'adam.
Tun daga kan isar da sakamakon wasannin Olympic a daukacin garuruwan kasar Girka to aikin taimakon matukan jiragen ruwa wajen bin hanyoyin Bahar Rum, tantabaru sun bayar da muhimmiyar gudunmawa a harkokin rayuwar yau da kullum.
Ko kun san cewa tantabaru za su iya gane fuskokin mutanen da ke ciyar da su? Kamar yadda Garn ya nuna dandazon taron tsuntsaye za su iya saukowa kasa yayin da suka gane fuskar mutumin da suka sani.
Ba ya killace tantabaru a gidansa – “A kashin kaina, ba na killace tsuntsaye don ba na jin daidai ne a ce su rayu a cikin a kurki (sai dai idan sun kasance ba za su iya zama a cikin daji ba).
Ban dai san mutanen da ke kaunar tantabaru kamar sauran dabbobin gida ba, sannan su zauna tare da su a gidajensu, don wannan lamari ne mai kayatarwa.” – Sai dai Garn yana da wajen ceton kare da ya yi wa lakabi da Possum, wato wurin da yake zuwa hawan tsauni a lokuta da dama.
Ya bayyana yadda wani tsuntsu ya aikata abin da zai dade bai manta da shi ba.
“Akwai tantabarar da ke wajen shakatawarmu (Ja da fararen farata) wadda ke sauka kasa ta biyo ni a lokacin da nake tafiya tare da karena kusan kullum har tsawon wata guda.
Sai wata rana, Garn ya ce, tsuntsawar sai ta bace, inda daga bisani ya gano ta bayan wasu watanni a kan titi mai lambar 14th Street a kan babban titin Manhattana, inda ta bayyana a cikin wani gungun tsuntsayen.
“Nakan je lokaci zuwa lokaci don in ciyar da tantabarun kwayar hatsi a lokacin huturun, saboda suna matukar bukatar abinci mai gina jiki, ta yiwu wannan jar tantabara ta gane ni tun daga lokacin,” a cewar Garn.
Kawar manomi ce a yankin Anatolia
A Turkiya can a Cappadocia, yadda tantabaru suka yi tasirin inganta Tsakiyar yankin Anatolia mai tsohon tarihi, wanda rabinsa Hamada ce, akwai akurkin tantabaru a gidaje da aka kawata duwatsu da su.
Daukacin tsaunin gabar ruwa an yi masa lakabi da Tsaunin Tantabara ko Tsaunin Gubercinlik - wanda yake a tsakanin Garuruwa biyu a Cappadocia, wato Uchisar da Gorene, inda ake yi wa tantabaru ramuka a jikin bango, masu siffar takalmin kwado ko burbushin ragowar tsauni mai aman wuta da ake samu a daukacin fadin kasar.
Kwasfan kwayaye da ake samu bayan tantanbaru sun kyankyashe, akan nike shi a yi gari don shafen kawata bangwayen majami’a. Kashin tantabaru a kan kwashe shi don alkinta bangwaye su yi nagarta a Karanlik Kilise, ko a Majami’ar Dark, wata shararriyar majai’a da ke gidan kayan tarihi na Goreme.
Mafi muhimmanci shi ne, ana gina gidajen tantanbaru a yankin don manoman da ke kusa su kwashi kashin tsuntsayen –su yi amfani da shi, haka ake yi tsawon zamani, ta yadda ake samar da taki a yankunan da tsaunuka masu wuta saboda ingancin sinadaran da ke damfare a tattare da su. Tsofaffin majami’un kogo aka kawata su don wadannan tsuntsaye su samu muhallin zama.
A da, manoma masu juriya na aikin tattara bahayar da ake kira gubercinlik ta yadda sukan yi kokarin fitar da dimbin sinadarin nitrogen da suke yin dabe da shi da lailayen bangwaye, aikin da sukan yi na tsawon shekara guda.
Da zarar an tattara, takin kashin tantabarar, duk da ba shi da kyawun gani, to abu ne dai mai kyautata rayuwar tsirrai a lambuna da gonakin hatsi, irin su alkama, domin suna da amtukar amfani ciyar da mutane a nan kusa da nesa.
Mutanen karkarar yankin sun yadda da cewa karen daji da sauran nau’ukan dabobin masu cizo da ke cin tantabaru ko ƙwayayensu sukan zame a kan farin kwan da ke suka take, al’amarin da ke haifar musu da wahala wajen shiga inda tantabarar take, al’amarin da ke bai wa tantabarar kariya a wurin.
Dangane da noma kuwa, burbushin abin da aka samu tsawon karnoni na al’adu a Turkiyya na nuni da hakan. Dimbin gidajen tantabaru da aka same su har zuwa yanzu tuni ne ga ci gaban zamani, yayin da tantanbaru ke yi wa mutane jagora a wajen tafiya, kuma ana binsu ka’in da na’in, don an yi amanna.
Amma mene ne dalilin da ya sanya tantabaru ba sa samun kulawa? Ko suna da alamar da ke nuna kiyayya ga mutane ne? Ko kuwa abokanmu ne har zuwa lokacin da ba ma bukatarsu, sai mu kyale su, su ji da kansu?
A cewar Garn, “Ba a yi watsi da tantabaru ba, ana mai kai su wasu kasashe don amfani daban-daban, al’amarin da ya hada da abincin mutane (a kan kiwata su don ciyar da mutane nama a karni na 20, kafin gonakin kiwon kaji su sha gabansu).
“Tantaaru sun gudu, sun yadu. Suna da basira, da nagarta, sannan suna da jajircewar rayuwa,” kamar yadda Garn ya yi karin bayani cewa, “Tantabara na iya rayuwa a Dandalin Times, a kewayen wajen gyaran ababen hawa ko bayan South Brond da gabar ruwan Brighton. Tsawon karnoni sun samu horon yadda za su iya rayuwa a birane, kuma suna yin hakan da kyau."
A zamanin nan, ana ci gaba kiwon tantabaru, ko da yake ba kamar yadda ake yi a da ba. Za ka iya samun akurkin tantabaru da gidan mai rufi da lambunan bayan gida a biranen Istanbul da Paris har zuwa Khartoum da Alkahira da Karachi, inda ake matukar sha’awar kiwon tantabaru ba tare da tursasawa ba.
Za a ji saukin cewa, akwai mutane irin su Garn da suka kulla abota da tantabaru.
Idan aka koma birnin New York ana yi wa wuraren shakatawa alamar tantabaru, musamman a ta’adar masu kade-kade da raye-raye, sai dai Daraktan Sadarwar Gidauniyar Tallafa wa rayuwar Tsuntsayen Daji, Catherine Quayle ta ki yarda da wannan lamarin.
“Ba za mu yarda cewa ana keta haddin tantabaru a New York ba, a cewar Quayle. “Akwai dimbin masoyan tantabaru.
"A matsayin asibitin kula da lafiyar dabbobin daji, wadanda marasa lafiyarsa sun hada da tantabaru, muna ganin dubban mutanen da ke zuwa wajenmu don ceton tantabarun daji da ke bukatar taimako. Mabiyanmu da masu ba mu gudunmawa manyan masoyan tantabaru ne.”
Gidauniya Tallafa wa rayuwar Tsuntsayen Daji da ke New York ta kula da lafiyar tsuntsaye fiye da 9,500 da kuma sauran nau;ukan dabbobi 180 a kowace shekara.
“Mutane na alakanta kazantar tituna da su, duk da cewa mutane suke baza kazantar a muhallin da suke zaune. Tantabaru, tamkar auran tsuntsaye haka suke da tsafta, kuma dole haka za su kasance, ta yadda za su iya tashi, jikinsu ya kasance da dumi, cike da koshin lafiya,” kamar yadda Quayle ta bayyana.
A cewar Quayle, tantabaru ba irin nau’ukan tsuntsaye ne da ke yin kaura ko su yi nesa da inda suke kyankyashe kwayaye ba – su tsuntsayen yanki ne, kuma suna matukar dogaro da mutane da muhallinsu, domin samun abinci da wajen kwana.
Mafi yawan mutane ba su da tarihin alakar mutane da tantabaru, wasu na ci gaba da amfani da tsuntsaye ta hanyoyi daban-daban, inda daga bisani sukan yi watsi da su da zarar bukatarsu ta biya.
Sai dai, wadannan bukatu a su hada da gudunmuwa mai dorewa ba, kamar samar da taki a shekara ko ‘yan aiken isar da sako cikin sauri; gudunmawar tantabaru ta fara gushewa, har ma ana ganin sun zama abin watsarwa.
Tamkar yadda Quayle ta nuna, “Akwai mutanen da ke ci gaba da saki ko yin watsi da tantabaru. Tantabarar gida da aka kiwata a akurki tabbas ba za ta iya rayuwa a daji ba, don haka sakin su su tashi a wajen bikin aure ko jana’izar mamaci ko wasu sauran nau’ukan bukukuwa karshe dai da yawa daga cikinsu mutuwa za su yi – ko saboda yunwa ko farmakin masu cinye su. Mun so wannan lamari da kakkausar murya.”
Akwai ranar tsira ta Duniya, wato 20 ga maris. Akwai ranar Aku ta duniya, wato ranar 31 ga Mayu. Ko da yake babu ranar Tantabara ta Duniya, akwai ranar martabawa da yaba wa tantabara, wadda ta yi daidai da 13 ga Yuni.
Masu kaunar tsuntsaye da dama, wadanda ke jin dadin kukansu ko kwaikwayon mutane da suke yi da abokan aku sun fahimci cewa, tantabara da ke sumumu ita ce kawarsu ta gari a gidajensu, duk da ganin yadda aka san aku da jajircewa.
“Akwai dimbin nau'ukan tantabarun dawa da ke bukatar a zaunar da su, ta yadda za su zama abokan mu’amalar zamantakewa da mutane,” a cewar Quayle.
"Ko da yake wadannnan tsuntsaye da ake ganin tamkar ba su da wayo, sukan iya zamowa abokan zaman gida fiye da aku, abin da ya fi kamata a lura, shi ne, tantabaru har yanzu suna bukatar cikakkiyar matukar kulawa, al’amarin da ya hada da “isasshen wuri da lokacin da babu wata takurawar da za ta hana su tashi.”
“Suna da natsuwa da nuna kauna tamkar abokan zama da sukan tara da juna a tsawon rayuwa (ko da yake rayuwar nau’ukan tantabarun dawa ba ta cika yin tsawo ba).” Kamar yadda Quayle ya nuna.
Nau’ukan tantabaru daji sukan rayu ne na tsawon shekaru uku zuwa shida. Ana killace su a matsayin tsuntsayen gida, ko da yake irin wadannan tsuntsayen na iya yin rayuwar tsawon shekaru 10 – ko ma fiye da haka.
Yayin da maguna da karnuka ke zaune lafiya kalau a muhallin da aka tsugunar da su, Kuale ya soki lamirin killace babbar tsuntsuwar daji da ta saba rayuwar a waje tana watayawa a kan titi, a ce an kebe ta a cikin dakinku, domin za ta girma ne cikin takura da taraddadin tsarewa.
“Jinjirar tantabara za a iya kiwata ta cikin kyakkyawar rayuwa a cikin daki, amma ba al’amarin da ya dace ba ne a dauko tantabarar dawa, matukar dai ba rashin lafiya ne ya kamata ba, ko rauni ko rashin iyaye, sannan a irin wadannan halaye, kamata ya yi a samu mai kula da namun daji ya kawo mata dauki, kamar yadda Quayle ya bayyana.
Karshe dai, tantabaru nau’ukan halittu ne da ba a cika lura da al’amuransu ba, alhali suna bukatar a ba su matukar muhimmanci fiye da yadda mutane suka dauke su, musamman bisa la’akari da irin hidindimu da gudunmuwar da suka bayar kamar yadda tarihi ya tabbatar.
Abu guda da aka fi tabbatarwa shi ne: Matukar akwai birane, wadannan kyawawan halittu babu inda za su je.