Wannan shi ne karon farko na abin da masu shirya gasar suka kira rangadin ƙasa da ƙasa na tsawon shekaru biyar a fadin nahiyar . Photo : Présidence Rwanda

Daga Charles Mgbolu

Kasar Rwanda ta karɓi baƙuncin dubban masu sha'awar waƙe-waƙe a wani shiri mai taken ''Move Afrika'', wanda ke da nufin baje kolin fitattun Afirka ga duniya ta hanyar waƙe-waƙe da kuma janyo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen waje zuwa nahiyar.

Wannan shi ne karon farko na abin da masu shirya gasar suka kira rangadin ƙasa da ƙasa na tsawon shekaru biyar a fadin nahiyar.

Taron wanda ya gudana a daren ranar Laraba a gidan BK Arena na babban birnin kasar Kigali babban birnin Rwanda, ya samu halartar fitaccen mawaƙin nan na Amurka Kendrick Lamar, wanda shi ya jagoranci taron.

Hakanan an gudanar da wasan kwaikwayo masu ban sha'awa daga mawaƙin Tanzaniya kuma marubucin waƙa Zuchu, ɗan rawar Ruwanda Sherrie Silver, da haɗin gwiwar mawaƙan Rwanda DJ Toxxyk da Ariel Wayz.

Wajen ya ruɗe da sowa a lokacin da Shugaba Paul Kagame ya hau kan dandamali inda ya yi wani jawabi mai jan hankali.

Shawo kan ƙalubale

“Akwai abubuwa da yawa da za mu iya magancewa tare. Yin aiki tare, nahiyarmu na iya tsayawa tsayin daka tare da shawo kan yawancin kalubale, " kamar yadda Kagame ya faɗa da babbar murya.

Haka kuma an samu sakonni daga kungiyoyi irin su Majalisar Dinkin Duniya a kan faifan bidiyo da aka dora, wadanda dukkansu ke kira ga matasa kan bunkasa hazaka da kuma ba da gudunmawa ga ci gaban Afirka.

“Fatan mu shi ne mutane a kowace al’umma inda Move Afrika ta ziyarta da su samu damar samun horon ƙwarewa da kuma samun damar yin aiki a masana’antar nishaɗi,” in ji masu shirya taron a cikin wata sanarwa.

Jagoran shirin Kendrick Lamar, wanda ya zo na biyu a jerin manyan mawakan rap na Billboard 50 na bana, ya yi wasa na tsawon mintuna 75, inda ya daka a daidai yana tsaka da yin waƙa don gode wa Afirka da ta karɓi baƙuncinsa.

Dare na musamman

“Wannan lamari ne na musamman a daren yau. Wannan ne karo na farko a wannan mataki a gaban mutanena. Mun zo daga Compton, California, don yin liyafa tare da ku duka, '' in ji shi, inda da ƙyar ake iya jiyo jawabin nasa saboda yadda magoya bayansa suka ruɗe da sowa da tafi.

Masu shirya taron sun ce bikin Move Afrika babban rangadin waƙe-waƙe ne na kasa da kasa na tsawon shekaru biyar wanda kasashen Afirka daban-daban za su shirya, inda tuni kasashen Nijeriya da Botswana da Kenya da Ghana, da Afirka ta Kudu za su karbi bakuncinsu.

TRT Afrika