Al'ummar ƙasar Afirka ta Kudu na ci gaba da nuna rashin jin daɗinsu game da mutuwar auren tauraron ɗan wasan zari-ruga ''Rugby'' Siya Kolisi da tsohuwar matarsa Rachel Kolisi bayan shafe tsawon shekaru takwas suna zaman aure.
Rachel ta halarci wani biki a birnin Cape Town a ranar Talata, wanda ke nuna fitowarta na farko a bainar jama'a tun bayan da ta sanar da rabuwar aurenta a watan Oktoba.
A wajen taron , Rachel Kolisi, wadda ta bayyana cikin annashuwa, ta yi shigar wata riga mara hannu wadda ta dace da bakar wando da ta saka.
Tauraron wasan Rugby Siya, ya yi ta samun saƙonnin ƙarfafa gwiwa daga masoyansa da sauran jama'a, wadanda suka kasance masu goyon bayan zamantakewar aurensa da Rachel.
Ɗan wasan ya bayyana irin soyayyar da ya samu, wadda ya ce ta kai har zuwa ƙungiyar wasansa ta ƙasa, wadda ta samu gagarumar nasara.
Shawara ta tsakanin juna
Tun daga ranar 22 ga watan Oktoban ne dai labarin rabuwar auren ma'auratan ya yaɗu, bayan da kowane daga cikinsu ya wallafa a shafinsa na Instagram, inda suka ce:
“Bayan dogon nazari da tattaunawa a tsakanin juna, mun yanke shawarar kawo ƙarshen aurenmu.
Wannan shawarar ta fito ne daga soyayya,da mutuntawa da kuma fahimtar cewa wannan ita ce hanya mafi dacewa a gare mu duka."
Rachel da Siya suna da 'ya'ya biyu da suka haifa tare - mace ɗaya da namiji ɗaya, kuma dukansu ba su wuce shekara 10 ba.
Kazalika ma’auratan sun yi renon kanwar Siya da kaninsa, wadanda suka rasa mai kula da su bayan mutuwar mahaifiyarsu a shekara ta 2009.
Siya da Rachel sun ɗauki nauyin yaran ne daga gidan marayu da aka kaisu a shekarar 2014, bayan da suka samu karfin iya biya musu bukatunsu na yau da kullum.