An gwada an yarda an kuma aminta. Wannan shi ne taken daya daga cikin wakokin da suka yi zarra na mawakin Reggae Burna Boy.
Wakar za ta iya kasancewa abin da za a rinka kiransa da ita, ganin cewa ita ce aka fi saurara ta intanet a Afirka inda take da masu sauraronta mutum miliyan 16.8 a duk wata.
Burna Boy ya kuma kasance daya daga cikin wadanda suka yi wasa a wurin wasan rufe Gasar Zakarun Nahiyar Turai wadda aka yi a birnin Santambul, inda kusan mutum miliyan 450 suka kalla a duk duniya.
Sauran mawakan da suke tashe a mahajar sauraren wakoki ta Spotify sun hada da Asake da Davido da Omay Lay wadanda dukansu 'yan Nijeriya ne.
Shi ma mawakin nan na Afirka ta Kudu DJ Black Coffee ya yi wani kayataccen wasa a dandalin Madison Square Garden a Nuwambar da ta gabata inda mutane da dama suka ce ya kafa tarihi.
Brahim el Mazned, wanda ya kirkiro bikin Visa for Music a Rabat ya shaida wa TRT Afirka cewa kan cewa wadannan mawakan su ne wadanda suka yi gwagwarmaya domin ganin wakokin Afirka sun hau dandamalin da duniya za ta kalle su. Wannan ne ya sa Recording Academy ta fitar da wani sabon gurbin kyauta ta "Wakar Afirka da ta fi zarra" a karon farko.
Za a soma bayar da wannan kyautar a yayin bikin Gasar Grammy ta 2024 inda za a mayar da hankali kan "wakokin da aka yi amfani da maganganun gida na musamman daga ko ina cikin Nahiyar Afirka waɗanda ke haskaka al'adun kaɗe-kaɗe na yanki.
Wannan rukunin ya kunshi wakokin Afirka wadanda suka shahara ko salon Afropop, amma an bar kyautar a bude ga dukanin rukunin wakoki.
The current nominees are Asake and Olamide for their song Amapiano, Burna Boy with City Boys, Davido for Unavailable, Ayra Starr with Rush and Tyla for Water.
Wadanda aka zaba a halin yanzu sun hada da Asake da Olamide kan wakar da suka yi ta Amapiano, sai Burna Boy kan wakarsa ta City Boys da Davido kan wakarsa ta Unavailabe sai kuma Ayra Starr da Rush da Tyla kan wakarsu ta Water.
Turbar kirkira
"An samu sabbin mawakan Nijeriya wadanda suka fito bayan annobar korona," kamar yadda el Mazned ya bayyana. "Akwai inganci a nan."
Yana ganin cewa abin da ya bambanta waɗannan masu fasaha na Afirka shine asalinsu. "
Sun rabu da abubuwan da aka san su da su; Ba wai kawai suna yin waƙar al'umma ba ne ko kuma wakokin da aka saba yi ba. Sun rungumi zamani”.
Mawakin nan dan kasar Ivory Coast Yann Bana yayi amanna kan cewa wakokin Afirka sun kara samun ci gaba kuma suna ci gaba da samun karbuwa domin samun matsayinsu a duniya
"Akwai 'yan Afirka da dama a yau wadanda suke cin kyatuttuka masy girma, wadanda sai a shekarun baya suka soma samun irin su," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika. "Akwai fata mai kyau. A halin yanzu ana ganin mawakan Afirka tare da na Yamma, inda suke kokarin tsayawa da su.
Bana ya yi mamaki kan cewa akwai mawakan kasa da kasa da dama wadanda suke so su hada kai da na Afirka. Daya daga cikin bidiyoyinsa na YouTube da yake kauna sun hada da wakar Davido ta Na Money wadda ake ciki akwai The Cavemen da kuma shahararriyar mawakiyar nan ta Jamhuriyar Benin wato Angelique Kidjo.
Sabon kundin wakokin da Bana ke yi na son game Afrobeats da jazz.
Iyakar hadin-kai
Ga mawakin da aka zaba domin lashe kyautar Grammy wato Amayo wanda ya girma a Nijeriya, "ana samun dama" sosai musamman a Legas da ke Nijeriya inda a nan ne ake samun sabbin mawaka
Kamar Bana, Amayo ya yi la'akari da cewa Afirka ya zuwa yanzu "tana tafiya da tsinuwar rashin hada kan al'adu".
To, shin sabon nau'in kyaututtukan da aka kirkiro zai raba kan mawakan Afirka maimakon hada kansu?
Kwararrun masana'antu suna ganin yanayin kiɗan ya zama mafi mamayewa - fiye da nau'ukan guda daya da kuma yiwuwar rarrabuwar kawuna kamar "Kida na duniya".
"Magana ake ta kabilanci kamar ɗaya daga cikin sahihanci da nau'i," kamar yadda mai sharhi kan kida Ammar Kalia a cikin makalar da ya wallafa a Guardian a 2019, "Don haka aibi da matsala: Me yasa kalmar 'waƙar duniya' ta mutu".
Wasu a yanzu suna ta tambayoyi: Shin Recording Academy ta inganta tare da daidaita sahihancin sabon rukunin kyaututtuka na Afirka?
Yayin da el Mezned da Bana ke murna da sabbin yunkurin wakar Afirka, Amayo ya damu. Ya yi amma sabon nau'in zai sa kowa ya gwada kuma ya "yi sauti kamar sauran masu fasaha".
"Muddin mutanen da suke zuba kudi a wakoki suna samun abin da suke so, hakan zai rinka taba matakin da suke dauka," kamar yadda ya nuna fargabarsa.
Bana ba ya tunanin wannan sabon sauyin a matsayin kin jinin sautin Afirka. Yana so ya tuna da tushen kidansa da gwaji. " Idan ka saurari wakokin Afirka, ka san daga Afirka suka fito," in ji shi. "Sautin da shi kansa karin sautin ya bambanta.
Za mu iya kirkirowa da gaurayawa kadan da na Yamma, ba tare da mun manta daga inda muka fito ba. Wannan shi ne abin da mawaka da dama suke yi."
Duk da cewa Amayo yana tsoron wannan sabon rukunin kyautar, yana da yakini baki daya. Sabbin abubuwa a tunaninsa wata dama ce wurin hadin-kai.