Yara suna bukatar karfafa musu tunaninsu don su jure wa munanan abubuwan da suka faru. Hoto: AA

Daga Pauline Odhiambo

Girgizar kasa mai karfin maki 6.8 ta fada wa Maroko a ranar 8 ga watan Satumba, abin da ya jawo dubban asarar rayuka da jikkatar mutane.

Girgizar kasar ta bar mummunan tabo ga mutanen da suka tsira, ciki har da dubban yara wadanda abin ya shafi tunaninsu, kamar yadda masana suka bayyana.

Akalla mutum 3,000 ne suka rasa rayukansu kuma fiye da yara 100,000 ne ta shafa, kamar yadda bayanan da Hukumar Ilimi da Raya al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) suka bayyana.

A wani kokarin taimaka musu don musu rage damuwa, sojojin Maroko suna bai wa yaran taimako ta hanyar yin wasa da su da wasu abubuwan nishadi ciki har da shafa bula a fuska.

Tattaunawar yaye musu damuwa za ta taimaka wa mutane masu kowace irin shekara ciki har da yara da suka dimauta. Hoto: AA.

Tattaunawa da nufin yaye damuwa

Har ila yau sojojin suna taimaka wa yaran da abin ya shafa ta hanyar bunkasa kaifin basirarsu wato Cognitive Behavioral Therapy (CBT), wato wata nau'in tattaunawa da nufin gyara lafiyar kwakwalwar wadanda suka damauta daga abubuwan da suka faru, ciki har da kananan yara da matasa.

Kamar yadda masana suka bayyana, CBT yana taimaka wa yara kan fassara da nazari a kan asalinsu ta hanyar rage munanan tunani da dabi'u marasa kyau.

Sanya yaran su yi dariya yana taimaka musu rage damuwa bayan ganin abubuwan da suka faru yayin girgizar kasar. Hoto: AA

Dariya

Za a iya sarrafa tunani da dabi'un yara don bunkasa kamun kai da daidaita tunani da sauransu a daidai wannan mataki da suke girma.

Abubuwan da ake yi suna sa yaran dariya da annashuwa.

Ta hanyar wasanni yaye damuwa ana iya dakile mummunan tunanin da ke bijiro musu kamar yadda masana suka bayyana. Hoto: AA

Wasa da nufin yaye damuwa

Galibin masana masu gyaran dabi'un yara suna amfani da wasanni wajen kulla hulda da yara da kuma kyautata zamantakewa da basira.

Tsarin wasanni don yaye damuwa an gina shi ne kan manyan wasanni na manyan da ke fama da dimauta.

Gano alamomin farko na fargaba a yara yana da muhimmanci wajen magance tsananin damuwa a dogon zango. Hoto: AA

Mayar da hankali

Koya wa yara mayar da hankali kan tunaninsu zai taimaka musu jure wa mummunan abubuwan da suka faru da su.

A karfafa musu gwiwa su rika bayyana damuwarsu yayin da kuma ake karfafa musu gwiwa kan su mayar da hankalinsu kan abin da ke faruwa a lokacin wanda hakan zai taimaka wajen nesanta su daga fargaba da tsananin damuwa.

Ana amfani da basira wajen yaye damuwa ciki har da ayyukan zayyane-zayyane wadanda za su iya taimaka wa yara wajen jure wa damuwa. Hoto: AA

Akalla yara miliyan 175 ne a fadin duniya suke fada wa wani hali sanadin faruwar bala'o'i a kowace shekara.

TRT Afrika