Daga Charles Mgbolu
Rungume da allon wasan surf fari, zakaran dan kasar Moroko Ramzi Boukhiam ya ja dogon numfashi kafin fafatawa a gabar tekun Cacimba mai igiyar ruwa shudi da ke tisbirin Fernando de Noronha na kasar Barazil.
Wannan a yayin gasar ISA World Surfing ta 2024 (WSG) ce, wanda ita ce wasan karshe da za a cancanci halartar gasar surfing ta Paris 2024. An gudanar da gasar WSG a tsakanin 23 a 24 ga Maris 2024.
Bayan awanni yana kan allonsa a saman tekun da ke hankoro, Moukhiam ya zo na biyu inda dan kasar Barazil Gabriel Medina ya lashe kambin zinare, sai Frenchman Kauli Vaast da ya lashe kambin tagulla a matsayi na uku.
Wannan nasara na nufin Boukhiam ya samu tikitin halartar gasar Paris 2024, wadda za a gudanar a tsakanin 24 ga Yuli da 11 ga Agusta 2024.
Wannan ne karo na biyu da Boukhiam zai halarci gasar wasannin Olypics, saboda ya halarci gasar Tokyo 2020.
Boukhiam na ta samun yabo daga 'yan kasar Morokko a shafukan saboda kokarin da ya yi sosai a gasa daban-daban da ya halarta.
A 2019 ya zama na shiga a gasar ISA World Surfing, wand ahakan ya ba shi damar alartar gasar wasannin tsalle-tsalle ta Olympics ta lokacin bazara a Afirka a 2020.
Daga baya ya fafata a gasar hawa gajeren allo a kan teku ta maza, inda Bafaranshe Michel Bourez ya yi nasara a kansa a zagaye na uku.
Dan wasan na surfing mai shekara 30 ya shaidawa manema labarai cewa yana jin dadin sakamakon da yake samu, musamman a lokacin da ya shuga wasanni da ciwon agara.
Cikin farin ciki ya fadi cewa "Ina jin karsashi sosai! Morokko, mun sake yin nasara, a karo na biyu."
Bajintar Boukhiam a gasar Oi Hang Loose Pro ta ba shi damar kara samun matsayi a duniya daga na 163 zuwa na biyu, inda yake da maki 5,375.
Ana yi masa kallon dan wasan surfing mafi kwarewa a Morokko, idan ya yi wannan nasara da yake bukata, hakan zai zama babban abin karfafa gwiwa ga Boukhiam, har ma a wasannin gaba da zai yi a gasar Olympics.