An bude gasar AFCON karo na 34 a Côte d'Ivoire a ranar Asabar 13 ga watan Janairu a filin wasa na Alassane Ouattara da ke Abidjan.
Za a ci gaba da gudanar da gasar har zuwa ranar 11 ga watan February inda ake sa ran gudanar da wasan karshe a ranar da kuma bai wa wadanda suka yi nasara kyaututtuka.
Wannan ne karo na farko da Côte d'Ivoire ke karbar bakuncin gasar AFCON tun bayan 1984. Shugaba Alassane Ouattara ya halarci bikin bude gasar.
Gwamnatin kasar ta kashe kusan dala biliyan 1.5 domin gyara kayayyaki don gudanar da wannan gasa.
Ana gudanar da wadannan wasannin a filayen kwallo shida a birane biyar a kasar da ke Yammacin Afirka.
Kasashe 24 daga fadin Afirka na halartar wannan gasa inda suke baje kolin al'adun su baya ga kwallon kafa.
An soma wannan gasa ta AFCON tun a 1957 inda ta kara habaka a tsawo shekaru.
An soma wasan farko tsakanin Côte d'Ivoire da Guinea-Bissau inda masu masaukin bakin Côte d'Ivoire suka ci 2-0.
Tun a watan Yuni da Yulin 2023 ya kamata a buga gasar ta AFCON domin guje wa cin karo da tsakiyar kaka ta gasar Turai, inda akasarin ‘yan wasan da ke buga gasar na can.
Sai dai fargabar da aka rinka yi ta saka gasar a lokacin damina shi ma ya kara sawa an daga gasar.