Wakokin Afrobeats na daga cikin wadanda aka fi ji a 2023 a nahiyar ta Afirka. / Hoto: AFP

Daga Charles Mgbolu

Shekarar 2023 ba shakka ta kasance shekara wadda abubuwa da dama suka faru a masana’antun nishadantarwa a Afirka, inda aka kafa tarihi daban-daban, da kuma gudanar da bukukuwan al’adu da kuma karbar kyaututtuka na kasa da kasa.

Haka kuma shekarar ta fuskanci kalubale daban-daban wadanda suka hada da mace-macen wasu daga cikin shahararrun mawaka.

A daidai lokacin da wannan shekara ke yin bankwana, TRT Afrika ta tattara wasu daga cikin manyan abubuwan da suka faru a 2023 ta bangaren nishadi.

Wadanda suka kafa tarihi

Ba za a ja labulen shekarar 2023 ba tare da ambato tarihin da shahararriyar mai girkin nan ba Hilda Baci ta kafa a duniya baki daya inda ta shafe sa’o’i 93 tana girki, wanda wannan shi ne lokaci mafi tsawo da wani mahaluki ya taba shafewa yana girki a duniya.

Hilda ta kafa tarihi bayan ta shafe kwana uku da rabi tana girki ba tsayawa. / Hoto: Others

Kafa tarihin da ta yi ya jawo mutane daga fadin kasar da ke Yammacin Afirka yin rige-rige domin su ma su kafa tarihi

Mawakiyar coci Oluwatobi Kufejione ta shafe sa'o'i 200 tana waka sai kuma Joy Chukwudi wadda mai sana'ar tausa ce, ta yanke jiki ta fadi bayan ta shafe sa'o'i 75 tana yi wa kwastamomi tausa.

Wani mutum mai suna Tembu Ebere ya yi yunkurin kafa tarihi ta hanyar yin kuka na mako guda wanda hakan ya sa masa makanta ta wucin-gadi, sai kuma na baya-bayan nan mai suna Enitan ya tsinci kansa a asibiti bayan ya shafe sa'o'i 50 yana wanke kaya.

Sai dai wadannan yunkurin dukansu ba a zayyana su a kundin ajiye tarihi na bajinta na Guinness World Record ba sakamakon hatsarin da ke tattare da su.

Haka kuma wasu da suka yi tafi mafi tsawo a Uganda inda mutum 926 suka yi tafi na tsawon sa'o'i uku; da kuma Tonye Solomon dan Nijeriya wanda ya hau matattakala 150 da kwallo a bisa kansa, da kuma Helen Williams 'yar Nijeriya wadda ita ce ta yi kitso mafi tsawo na daga cikin wasu 'yan Afirka da GWR ya tabbatar da su.

Lashe kyauta a gasanni da bukukuwa

An gudanar da karo na tara na bikin karrama fina-finai wanda ake yi a duk shekara na Africa Magic Viewers’ Choice Awards a ranar 20 ga watan Mayu a Legas, inda masu shirya fina-finai daga Gabashin Afirka da Yammacin Afirka da Afirka ta Kudu suka lashe kyaututtuka da dama.

Fim din Click Click Bang na mai shirya fim dan kasar Kenya Philip Karanja Njenga ne ya ci kyautar fim mafi kyau na Yammacin Afirka gasar AMVCA. / Hoto: Philip Karanja Njenga

Bukukuwan fina-finai da dama wadanda suka hada da Africa Film Festival da Marrakech International Film Festival, duka sun bayar da kyaututtuka ga masu shirya fina-finai na Afirka da Gabas ta Tsakiya.

Kungiyar hadin kan masu fina-finai ta Afirka FEPACI ta lissafa cewa fina-finan Afirka sun yi matukar karuwa a 2023, inda bangaren nishadin ya samu ci gaba da kaso 12.76 a cikin 100, wanda ake sa ran bangaren zai samu kasuwar dala miliyan 112.90 zuwa shekarar 2027.

Hukumar Kula da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta yi kiyasin cewa bangaren fina-finan ya samar da ayyukan yi miliyan 20 a 2023 da kuma samar da dala biliyan 20 a kudin shiga na nahiyar baki daya.

Bukukuwan mawaka

Kamar fina-finai, wakoki daga shahararrun mawakan Afirka na daga cikin abubuwan da aka fitarwa daga nahiyar Afirka.

Zuwa Oktobar 2023, kamfanin Spotify wanda ake sauraren wakoki ya bayar da rahoton cewa an saurari wakoki sau biliyan 15 (kuma yana ci gaba da kirgawa) wadanda akasarinsu Afrobeats ne daga Yammacin Afirka wadanda hakan ya jawo suke tasiri matuka a fagen wakoki a fadin duniya a yayin da mawakan ke ci gaba da samun kyaututtuka.

Burna Boy na daga cikin mawakan da suka fi cin kasuwa a 2023. / Hoto: Burna Boy

Burna Boy wanda dan Nijeriya ne ya lashe kyautar Mawaki wanda ya fi kwarewa a kasa da kasa a kari na hudu a gasar BET sai kuma Rema ya ci kyautar MTV Afrobeats Award kan wakar da ya yi ta 'Calm Down' tare da mawakiyar nan ta Amurka Selena Gomez a watan Satumba.

Haka kuma Rema ya kafa tarihi bayan ya kasance a saman allon Afrobeats na Amurka a tsawon shekarar.

Mawakin nan na Tanzania Diamond Platnumz shi ma ya haskaka a 2023 bayan ya sha gaban Burna Boy da Asake wadanda duka 'yan Nijeriya inda ya zama fitaccen mawaki na Afirka a gasar MTV wadda aka gudanar a watan Nuwamba.

Mawakin nan na kasar Ghana mai suna Black Sherif shi ma ya yi nasarar cin kyauta a gasar BET ta 2023.

Fasaha da tallan kayan-kawa

Fagen tallan kayan-kawa na Afirka ya yi matukar habaka a 2023, inda UNESCO ta bayar da rahoton cewa bangaren ya samar da kayayyakin fitarwa wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 100, inda ake sa ran hakan zai ninka sau uku a shekara mai zuwa.

Masu basira da fasaha sun samu damar baje kolin kayayyakinsu a bukukuwa daban-daban na kasaita wadanda aka gudanar a kasashe wadanda suka hada da Paris da London da kuma bikin tallan kayan-kawa na Afirka.

Mace-mace

A farkon shekarar ne aka samu labari mara dadi na mutuwar daya daga cikin shahararrun mawakan Afirka ta Kudu Kiernan Jarryd Forbe wanda aka fi sani da AKA a ranar 10 ga watan Fabrairu.

An harbe mawakin mai shekara 35 tare da abokinsa Tebello ‘Tibz’ Motsoane a lokacin da suke hanyar zuwa motarsu bayan sun fito daga wani wurin cin abinci a Durban.

An harbe mawakin tare da abokinsa a kusa da wani wurin cin abinci a Afirka ta Kudu. / Hoto: Others

An kama mutum biyar wadanda ake zarginsu da hannu a kashe mawakin.

A watan Maris, mawakin Afirka ta Kudu Costa Titch mai shekara 28 ya yanke jiki ya fadi a lokacin da yake wasa a yain wani bikin mawaka.

Iyalinsa a yayin wata sanarwa da suka fitar sun bayyana cewa ya mutu jim kadan bayan faruwar lamarin.

Haka kuma a watan Satumba, masoya wakokin Nijeriya sun yi jimamin mutuwar mawakin nan dan shekara 27 Ilerioluwa Oladimeji Aloba wanda aka fi sani da suna Mohbad.

Abubuwan da suka faru wadanda ke da alaka da mutuwarsa sun tayar da kura, wanda hakan ya jawo zanga-zanga inda 'yan sandan Nijeriya suka kaddamar da bincike a kan kashe mawakin har ta kai ga kama wasu, duk da cewa har yanzu ba a samu wani da laifi ba.

Wasu labaran da suka bazu

Yaran 'yan rawa Triplet Ghetto Kids daga kasar Uganda sun sake yin wata rawar a idon duniya wanda hakan ya sa suka kai mataki na karshena gasar British Got Talent a watan Yuni.

Ba wannan ne karo na farko da yaran suka yi suna ba, domin ko a 2022 sai da suka yi tallar Gasar Cin Kofin Duniya.

Duk da cewa ba su yi nasara ba, amma an yabe su kan irin jajircewar da suka nuna ganin yadda suka fito daga karkara har aka san su a duniya.

Mawakin Nijeriya Oladips ya yi mutuwar karya a watan Nuwamba a kafafen sada zumunta dangane kan dalilan da bai bayyana ba. Sai dai bayan ya bayyana a kafar sada zumunta bayan mako guda, masoyansa sun rinka yi masa martani mai zafi.

TRT Afrika