A wajen mai fasaha na Afirka ta Kudu, Jason Langa, abin da ke boye a cikin zukata na iya bayyana a cikin launin shudi. Hoto: Jason Langa

By Pauline Odhiambo

Idan da a ce abubuwan da suke zuciya za su iya bayyana a zahiri, da wace irin kala ko fuska za su bayyana? Da haske mai daukar hankali, ko mai duhu?

A wajen mai fasahar na Afirka ta Kudu Jason Langa, abubuwan da suke zuciya shudi ne - ba wai kalar shudin ba kawai, kalar shudin da ke nuna farin ciki da irin kamar a nuna cewa "ina bakin kokarina."

"Ina amfani da shudin launi a zane-zanen da nake yi ne domin isar da sako," in ji Langa a tattaunawarsa da TRT Afrika. "Sanin cewa kowane mutum akwai yadda yake kallon kowane nau'in kala ya taimaka min wajen kara fahimtar amfani da kala a aikina da kuma samun damar bai wa mutane abin da suke so."

A cewar Langa, fentin shudi a zane-zanensa na nuna yadda mutane suke fama da matsalolin rayuwa tare da kokarinsu na daidaita rayuwarsu cikin matsalolin domin ci gaba da rayuwa.

Tuna abubuwan baya

Babban karfin gwiwar Langa shi ne ganin yadda mutane ba sa yanke kauna da rayuwa, inda suke ci gaba da gudanar da rayuwarsu duk da matsalolin da suke fuskanta.

"Yanzu, tsarin yanayi yana kara karfafa min gwiwa idan aka kwatanta da yanayin rayuwa domin ina ganin suna da alaka da juna,” in ji mai fasahar dan shekara 27.

Launin shudi na taimakawa wajen isar da wani sako daga fasahar da aka kirkira zuwa ga mai kallo. Hoto: Langa

"Idan ka wayi gari a yanayi kamar na hunturu, za ka iya jin tamkar kana wata irin rayuwa ta kunci. Amma idan ka tsinci kanka a duniyar da furanni ne suke kadawa a yanayi irin na bazara, za ka ji kwanciyar hankali da nutsuwa."

Shudin layin da ke zane-zanen Langa suna nuna wani irin alaka da ke tsakanin abin da ya zana da mai kallo, wanda hakan ke sa mai kallon ya fara tunanin yadda duniyar za ta gyaru, abubuwa su koma daidai.

Langa ya kara da cewa la'akari da sauyin yanayi da kuma yadda mutane suke ci gaba da rayuwarsu a kowane irin yanayi na rayuwa na cikin abubuwan da yake son nunawa a zane-zanensa.

"Zana abubuwan da suke da alaka da kowane irin yanayi na kara tunatar da bukatar da ke akwai na more kowane yanayin da ake ciki domin shi ma din zai wuce," in ji matashin mazaunin birnin Johannesburg.

"A tsakanin shudin da nake yawaita amfani da shi a zane-zanena, nakan ratsa hotunan ganyayyaki da sauran abubuwan da suke nuna yanayin shudi masu nuna ci gaba da hakurin jure kowane irin yanayi da ake ciki."

The myriad hues of life is the relatable experience his art attempts to embody. Photo: Langa

Mutum-mutumi a matsayin abokan aiki

Kamar sauran masu fasaha, Langa tun yana karaminsa ne ya gano yana fasaha. Kasancewar ya taso bai cika son magana sosai ba, sai ya kasance ya fi son zana mutum-mutumin da yake so su zama tamkar abokan hirarsa.

"Idan yara suka ga zane-zanena, sai su fara magana a kan mutum-mutumin Ben 10 da sauran ire-irensa da suke tunanin zan iya zanawa," in ji shi, sannan ya kara da cewa, "Watarana lokacin da malamin da ke koya mana darasin zane a sakandire ya fada mana cewa ya sayar da wani zane da ya yi a kan ran 30,000 (Dalar Amurka 1,600), sai na fara daukar zane-zanen da muhimmanci sannan na dauka fasahata a matsayin sana'a."

Bayan kammala sakandire, sai Langa ya yi karatun shekara uku na kwarewa a kan zane a wata kungiya mai suna Artist Proof Studio.

Tun wancan lokacin, sai yake ta kara neman kwarewa, inda sannu a hankali ya zama gwani a sana'ar, har ya fara fadadawa tare da amfani da wasu sababbin dabarun zanen. Ya kaddamar da wajen zanensa a shekarar 2020.

Fassara abubuwan da suke cikin zuciya

"Da farko da alkalami kawai nake zane, amma da na fara kwarewa sai na fara gwada yin zane da alburushi," in ji Langa a tattaunawarsa da TRT Afrika.

Kamar sauran masu fasaha, tun Langa yana yaro ne ya gane yana da fasahar zane. Hoto: Langa

"Kasancewar ina sha'awar sauraron mutane idan suna magana, sai ya kasance irin wadannan tattaunawar sun yi tasiri a yanayin zanen da nake yi."

Yawancin zane-zanensa mutanen da suke tare da shi ne. Wasu lokutan yakan zana baki da wasu wadanda ya taba yin mu'amala da su.

"Wasu lokutan abubuwan da suka faru ko muka tattaunawa a baya sukan fado min a duk lokacin da nake zane," in ji Langa.

"Kafofin sadarwa na zamani ma sun taimaka min domin a irin kafofin ne mutane da dama suke bayyana yanayin da suke ciki na farin ciki, wanda ni kuma nake kallo in bayyana a cikin zane."

Kamar sauran masu zane, shi ma Langa yakan yi fama da daukewar basira, matsalar da yake yaka ta hanyar kallon yanayin sararin samaniya.

"Nakan fara zane ne ta hanyar fitar da tsurar zanen a jikin allo kafin na bi shi da fenti."

"Wani lokacin nakan rasa yaya zan yi in fitar da zanen, a irin wannan lokacin ne nakan fita wajen in dan sarara. Yawanci za ka ga da zarar na dawo, sai in ga zanen na fita fes."

Zanen Golden Nostalgia yana cikin zane-zanen Langa na 2024. Hoto: Langa

Samun daukaka

Zane-zanen Langa sun samu shiga Mujallar Glamour ta Afirka ta Kudu. A shekarar 2021, ya yi aiki tare da wasu masu fasaha guda 14 domin karrama marubuci, mawakin kuma jagoran fafutika Nokutela Mdima-Dube.

"Aiki ne na hadaka tare da masu fasaha 15 da suke amfani da fasahohi daban-daban wajen yin zane. Kowannenmu ya zana wata mata ta hanyar kallon wani hoto," in ji shi.

Mujallar Ighawe ma ta yi amfani hotunan zane-zanen Langa tare da hotunan wasu fitattun masu daukar hoto. Haka kuma wasu kungiyoyin duniya sun baje-kolin ayyukansa.

Yadda yake samun karbuwa a matsayin mai fasaha mai tasowa a cikin kasarsa da ma kasashen duniya ne suke kara karfafa gwiwar Langa, wanda hakan ya sa yake kara kaimi.

Zanen da ya yi a kwanan nan mai suna "Golden Nostalgia," wanda ya yi saboda yanayin hunturun Johannesburg ya kayatar kuma an baje-kolinsa a taruka biyu a birnin.

"Na fara tunanin wannan zanen ne watarana ina kan hanyar zuwa sayan kayayyakin zane. Sai na ga hasken rana irin na yanayin hunturun, wanda ya nuna cewa duk rintsi lallai akwai nasara a gaba, sannan ya tuna min lokacin da nake dan koyo a sana'ar," in ji shi a tattaunawarsa da TRT Afrika.

"Yana da kyau ka shirya fuskantar kowane irin kalubale ka samu kanka a ciki domin bayan kowace matsala akwai sauki," in ji Langa.

TRT Afrika