Tukwanen kasa na daga cikin kayayyakin da aka sha tonowa na tarihi a kan gabar teku a Gabashin Afirka wanda hakan yake nuna irin al'adun da mutanen yankin ke da su.
Wannan fasahar ta yin tukwanen kasa ta kasance wadda aka rinka koya ta kaka da kakanni inda har yanzu ana ci gaba da gudanar da ita, inda ake samun tasirinta har a Masar da kuma wasu kasashe da ke can gabashi.
A cikin birnin Mombasa na Kenya, na hadu da Time Mwinyi a yankin Jomvu Kuu a lokacin da take hanyarta ta zuwa wurin aiki, wanda ba shi da nisa da gidanta. Anan, ta haɗu da 'yan uwanta mata masu aikin tukwane na yumɓu.
Aikin hada tukwane na yumɓu har yanzu wata al'ada ce da mata ke alfahari da ita. Irin ƙwarewar da suke da ita wurin hada tukwane da tukwanen girki da sauran kayayyaki wadanda ake yi da laka na daga cikin al'adun zamani na Swahili.
Alkinta al'adu
Wata fasaha ce wadda ta ba su damar alkinta al'adarsu da kuma koyon yadda za su dogara ka kansu, kamar yadda Mwinyi ta bayyana.
"Wannan aikin ya sa mun yi nisa; ya samo asali ne daga abin da muka koya daga na gaba da mu inda muke son mu ci gaba da koya wa wadanda suke bin bayanmu. Babbar dama ce saboda ta hanyar yin tukwane, za mu iya sayar da su sannan mu samu riba har mu taimaka wa ilimin ƴaƴanmu," kamar yadda Mwinyi ta shaida wa TRT Afrika.
Matan suna aiki ne a tattare idan za su yi tukwanen. Matakin farko ya kunshi hada yumɓu da kasa ta musamman, sai a kara ruwa a kyale ta domin ta sarara. D zarar yumɓun ya daidaita sai a fara sarrafa shi.
Mataki na gaba shi ne a siffata tukunyar ta hanyar ɗaga yumɓun, kuma ana ɗaukar ɓangaren ciki don samar da siffar tukunyar. Ana amfani da kwallon bawon kwakwa domin gyara cikin tukunyar. Sai dai a hankali, ana yanka tukunyar da aka kammala a ajiye ta a kan dutse. Wannan matakin na bukatar kwarewa sosai ta yadda tukunyar ba za ta lalace ba," in ji Mwinyi.
Ana ajiye tukwanen a gefe su bushe. Haka ana amfani da irin wannan tsari don yin wasu abubuwan da yumɓu wadanda suka hada da kwanon cin abinci da kuma farantin kasa
"Bayan bushewa, an yanke sashin ƙasa na tukwane kuma an tsara su da kyau. Muna ƙara ƙananan kayan ado a sama, sannan mu gyara shi da filasta. Ana shirya tukwane kuma a tsaftace su a hankali kafin a sanya su cikin rana," kamar yadda Mwinyi ta yi bayani.
Wurin gashi na gargajiya
Bayan sun bushe, ana gasa tukwanen a cikin wurin gashi na gargajiya ta hanyar amfani da bawon kwakwa da wata ciyawa ta musamman. Ana yin haka ne domin samun zafin da ake bukata da hayaki.
"Idan muka saka tukwanenn a cikin wurin gashin na tsawon sa'o'i da dama kuma suka gasu, muna fitar da su domin su huce. Bayan wannan matakin, za a iya sayar da su," kamar yadda ta kara da cewa.
Ana samun irin wadannan tukwanen sosai a wurin 'yan kasuwa a kasuwar tukwanen kasa ta Mwembe Tayari da ke Mombasa.
Sai dai a halin yanzu an rage amfanin da tukwanen kasa na gargajiya sakamakon zuwan na karfe da sauran na zamani.
"An samu raguwa a sana'ar yin tukwane tun bayan da aka fito da kayayyakin gargajiya irin su tukwanen karfe. Shi yasa muka kara da wasu abubuwa kamar tsintisya da kwando da tabarya da sauran kayayyaki," kamar yadda Kulthum Shenga Khamis ta bayyana, wadda 'yar kasuwa ce.
Jama'ar yankin Jomvu Kuu har yanzu suna da aminci ga tukwane da kayan aikin yumɓu a kan kayan zamani. Sun yi imanin cewa suna da fa'idodi da yawa a dafa abinci da lafiya.
"Ba za ka iya kwatanta tukunyar kasa da tukunyar ƙarfe ba, sakamakon tukunyar kasa tana daɗewa abinci bai lalace a ciki ba, ba kamar ta karfe ba. Wasu abubuwa kamar marufi na iya ƙara ɗanɗano na musamman ga miya. Za a iya amfani da gwagwada kuma wasu abubuwa kamar su 'maziga' domin girki da su idan ana amfani da itace ko kuma ko kuma gawayi," kamar yadda Mwinyi ta kara jaddadawa.
Sakamakon irin kalubalen da ake fuskanta na gushewar kwarewar fasaha wurin yin tukwanen ƙasa, matan da ke yin wadannan ayyukan sun hadu domin kafa kungiya.
Kungiyar na da burin kiyaye al'adunsu ta hanyar koyar da zuri'a masu zuwa da kuma halartar bukukuwan al'adu da ake shiryawa a Mombasa da sauran yankuna.