Sunayen na daga cikin abubuwan da ake ji daga wuri mai nisa a cikin daji. Masana kimiyya na ganin cewa dabbobi da ke da iyalai masu yawa waɗanda ke rabuwa su kuma sake haɗuwa akwai yiwuwar su rinƙa kiran kawunansu da sunaye.
"Idan kana kula da iyalai masu yawa, dole ne sai ka rinƙa cewa, 'Ke Virginia, ki zo nan!" kamar yadda Stuart Pimm ya bayyana wanda masanin halittu ne ne Jami'ar Duke wanda ba ya cikin binciken da aka gudanar.
Lamari ne mai wahala ga dabbobin daji su kira junansu da sunaye. Bil'adama su ma suna da sunaye, haka karnuka na zuwa idan aka kira su da sunaye. Su ma jariran kifin dolphins na ƙirƙiro wa kansu sunaye, inda suke fito iri-iri, haka ma tsuntsun aku yana kiran sunaye.
Duka irin waɗannan dabbobin na da wata hanya ta kiran sunaye da kuma fitar da sauti iri daban-daban a tsawon rayuwarsu — wanda wannan wata baiwa ce da giwaye su ma suke da ita.
Wurin ajiye sautin giwaye
A binciken da aka gudanar, masana halittu sun yi amfani da da wata na'ura domin gano yadda giwayen ke amfani da sauti domin kiran sunaye inda aka rinƙa rikodin ɗin muryoyin giwayen a gandun dabbobi na Samburu da Amboseli da ke Kenya.
Masu binciken sun rinƙa bin giwayen a cikin motoci ƙirar jeep domin sa ido kan idan an kira sunayen giwayen yadda suke mayar da martani.
"Kamar bil'adama, su ma giwaye na amfani da sunaye, sai dai ba su furta sunayen kamar yadda bil'adama ke furtawa, ba mu da tabbacin ɗari bisa ɗari kan suna hakan," kamar yadda Mickey Pardo ya bayyana wanda shi ne jagoran binciken kuma malami a Jami'ar Cornell.
Ƙarar da wasu giwayen ke yi kunnuwan bil'adama ba su iya jin su. Masana kimayyan su ma kansu ba su da tabbaci kan wani ɓangaren maganar ne daidai.
Masana kimiyyan sun yi gwajin sakamakon nasu ta hanyar kunna wa giwayen rikodin ɗin, inda suka mayar da martani cikin shauƙi da kaɗa kunnuwa da ɗaga hancinsu, a lokacin da suke jin sautin kiran sunayensu. A wani lokacin giwayen na yin biris da sunayen da ba na su ba idan an kira.
"Giwaye suna da matuƙar son mu'amala, inda suke yawan magana da taɓa juna — wannan da alama na daga cikin abubuwan da ke ja giwayen suna magana da juna," kamar yadda abokin binciken ya bayyana George Wittemyer na Jami'ar Colorado.