Kunkuru yana daya daga cikin dabbobi da suka fi tafiya a hankali, sai dai yanzu an samu sarkin tafiya da sauri.
Kunkurun, mai suna Bertie, yana daga cikin jinsi kunkuru na leopard ya kasance kunkurun da ya fi kowane sauri a duniya, shekara tara bayan samun kambin Bajinta na Guinness World Records (GWR).
Shi ya sa aka ba shi sarauta ta sarki.
Kundin Bajinta na Guinness World Records ya sanya wa kunkurun sunan "mai gudun tsiya."
A wannan mako kundin ya taya sarkin murnar cikarsa shekara 16 a duniya, inda kuma ya ce har yanzu babu wani kunkuru wanda ya doke bajintar da Bertie ya kafa.
Kundin Bajinta na Guiness ya tabbatar dacewa Bertie ya samu nasarar ne a shekarar 2014, bayan ya yi tafiyar mita 0.28 a dakika daya (tafiyar kafa 0.92 a dakika daya), inda ya wuce bajintar da Charlie ya kafa, wato wani kunkuru da ya yi tafiyar mita 0.125 a dakika daya, wanda babu wanda ya kalubalance shi tun shekarar 1977.
Wanda ya mallaki Bertie sunansa Marco Calzini da matarsa Janine sun ce saurinsa yana da alaka da strawberries da ake sanya masa a karshen hanyarsa, wadda ke sa shi ya yi kwadayin kai wa karshen tafiyar.
Dabba mai farin jini
"Mun karbi ragamar kula da Bertie kusan shekara hudu kenan bayan da ainihin masu shi sun komawa wata kasa," kamar yadda masu kula da Bertie, Marco Calzini da matarsa Janine, suka shaida wa kundin bajinta na Guiness a lokacin.
An shirya taron tarihin ne a gidansa da ke tsaunin Adventure Valley, wani wurin shakatawa a kauyen Brasside da ke birnin Durham a arewa maso gabashin Ingila.
Tun bayan kafa tarihi a Kundin Bajinta na Duniya na Guinness, Bertie ya zama tauraro inda ake kai masa ziyara kuma manna takardar shaidar bajintarsa ta Guiness a bangon wurin da yake zama.
Bertie yana ci gaba da rike da bajintar Guinness kuma yana rayuwa ne tare da budurwarsa Shelly a wani wurin kasaita, kamar yadda masu kula da dabbobin suka bayyana.
Jinsin kunkuru na leopard suna rayuwa ne a yankin savannah mara danshi a tsakiya da kudancin Afirka. Yayin da Bertie yake ci gaba da rike kambun sarautarsa lokaci ne kawai zai iya tabbatar da ko za a iya samun wanda zai doke bajintar da ya kafa.