Mai zanen ɗan asalin Nijeriya ƙwararre ne wajen zana hotunan rayuwa a kasuwanni. / Hoto: Falope Ibrahim

Daga Pauline Odhiambo

Salon zane na Falope Ibrahim ba ya nufin kai mutum ga zayyanar duniya irin ta gaske. Wani ɓangare na labarinsa shi ne zanen wani mai talla yana talla a titi, a tsakiyar kacaniyar kasuwannin Afirka.

Idan ka ga zanen tamkar ka ɗauka zai yi magana, idan abinci ne kuma zai yi ƙamshi. Idan ka ga rana tamkar za ka ji zafinta, ko ka ji hayaniyar kan titi.

Yana ɗan shekaru 29, wannan mai zanen ɗan Nijeriya ya samu shuhura a fannin zane, saboda baiwarsa ta sawwara abu kamar gaske.

A wani zane mai suna "Sanda Rana Ke Haskakawa", an nuna wata mai talla tana kare kanta daga zafin rana tana riƙe da lema ƙarƙashinta haɓarta, sannan tana tattara 'ya'yan itace ga wani mai yin sayayya.

Falope yakan ɗauki hotunan wurare daban-daban sannan daga baya ya zana su kan ƙyalle. / Hoto: Falope

Falope ya faɗa wa TRT Afrika cewa, "Ina tafiya gefen kasuwa wata rana sai na ga wata mai talla. Abin da ya burge ni shi ne tana riƙe da lema, sannan kanta yana karkace don ya riƙe lemar".

"Bayan neman izininta, na ɗauki hotonta sannan daga baya na zana ta a ƙyalle."

Salon zane na Falope yana sawwara hoto daki-daki tamkar gaske. / Hoto: Falope

Falope ya ce, "Sanda ya zana wannan, ina tunanin yadda tunaninmu ke bambanta daga yanayin da duniya ke kallon mu".

"Ina gode wa Allah cewa jikinmu ba a buɗe yake ba, da kowa ya iya ganin abin da ke cikinmu."

Zane mai suna 'The Seekers' ya nuna matsayin yawancin matasan Afirka da ke neman aiki a ƙasashen waje. / Hoto: Falope

Falope ya bayyana cewa, "Muna da matasa a Nijeriya marasa aikin-yi. Suna da basira kuma suna da fikirori amma ba su da damarmakin amfani da fikirarsu don neman kuɗi, wannan ya sa wasunsu ke nemn aiki a ƙasashen waje".

Wani zanensa mai suna "The Tomorrow Dawn" ya nuna batun kyautata fata game da gobe. Sai kuma mai suna "The Helping Hands" wanda ke tuno da yarintarsa, lokacin da yakan taimaki mahaifiyarsa da kakarsa wajen sayar da kaya a kasuwa.

"The Helping Hands" yakan tuna masa lokacin da yake yaro yana taimakon mahaifiyarsa a kasuwa. / Hoto: Falope

Mazan jiya

Wani zane na Falope mai suna "Mama" yana ƙayatarwa kuma yana jinjinawa iyaye mata a duniya, waɗanda ke aiki ba hutu don samar wa 'ya'yansu kyawawan damarmaki.

Falope ya faɗa wa TRT Afrika cewa, "Sanda ina yaro na kasance ina ɓata littafan rubutu ina zane kansu, amma maimakon mamata ta min faɗa, sai take sayo mi ni littafin zane don na yi zane-zanena".

'Mama' wani zane ne da Falope ya bayyana jinjinarsa da godiyarsa ga matan da suka raine shi. / Hoto: Falope

Shawarar Falope ga masu son koyon zane iat ce, "Ku gwada yin zane a-kai-a-kai kuma ku shirya saka lokaci mai tsawo a zanenku. Ka da ku raina basirarku."

TRT Afrika