Daga Firmain Eric Mbadinga
Kamar sau nawa kake ji mutane na cewa muryar wani ita ce "arziƙinsu"?
A cikin jerin sana'o'i inda murya za ta kawo maka alheri, waƙa babu shakka ita ce za ta fara faɗowa rai.
Amma kuma akwai wasu ayyukan masu nasaba kamar naɗar murya inda idan mutum ya mallaki abin da ake kira "daddaɗar murya" zai iya samun alheri mai tarin yawa.
Stévy Daic Ndjalala Totolo ƙwararre ne a wannan harkar. Sakakkiyar muryarsa, wacce yake iya sarrafa ta cikin sauƙi yana yin ta ƙasa ƙasa kuma ya ɗago ta sama, ana amfani da ita a naɗi muryar jaruman finafinai da na katun cikin harsunan Afrika da na duniya daban daban.
A shekarar 2021, Stévy ya kafa Gemini Multimedia, wani kamfani da ke Rwanda da ya zarce baje baiwarsa da ke bayyane na yin amfani da muryarsa kan jarumai daban daban.
A matsayinsa na mai tafinta na ƙasa da ƙasa kuma kwararre a fannin sadarwa, Stévy ya samar da wani tsarin kasuwanci da ke da hadafin hana janye ƙwararru da kuma da kuma jawo jari wa nahiyar Afirka.
"Ni ɗan ƙasar Gabon ne kuma tawagata ta ƙunshi mutane ɗaiɗaiku masu ɗimbin basira daga faɗin Afrika.
Duk lokacin da akwai buƙatar a juya wani abu zuwa Hausa,Swahili,Yoruba ko Shona na Zimbabwe, ina bayar da kwangilar aikin wa mutanen da suka hulɗar aiki tare bisa ƙwarewarsu a harshen da ake batu, Stévy ya gaya wa TRT Afrika.
"Ina aiki da masu shirya fina-finai ƴan Faransa kuma ina aikin naɗar murya a ayyukan da aka yi da Turanci."
Tanadin samar da amo
Ana naɗan muryar ce a yanayi na walwala na cikin sutudiyon da ke tsakiyar gundumar Kagugu ta Kigali.
Gemini Sutudiyo, wanda ya yi fice saboda ingancin kayan aikinsa, an ƙawata shi da kayan aiki na zamani don tabbatar da sautin amon da ake buƙata da kuma kaucewa damun maƙwabta.
Daga wannan shimfiɗar, da kuma taimakon tarin muryoyinta a harsuna daban- daban na maza da mata, Gemini Multimedia yana samun hannun jari kasuwa a wannan ɓangaren.
"Kamfanonin ƙasashen ƙetare da yawa suna zuwa domin aiki da mu saboda muna da kayan aiki, gogaggun ma'aikata waɗanda suka san yadda za su gudanar da aikinsu says Stévy. Waɗannan kamfanin suna wajen mu ne saboda muna gogayya ne sosai.
"Farashinmu yana haifar da yanayin ciki lafiya baka lafiya. Ma'aikatanmu da waɗanda muke ba wa ayyuka za su iya gudanar da rayuwar rufin asiri da abin da suke samu."
Daga cikin abokanan hulɗa da suka aminta da kamfanin akwai wani Kamfanonin tallace-tallace da suke shirye shiryensu a harshen Ingilishi, da kuma wata ƙungiyar da ba ta gwamnati ba, waɗanda ɗan kasuwar ya sakaya sunansu saboda dalilai na ƙashin kai.
Ji ka gaskata
A fina-finan da katun da labaran majigi da kuma tallace tallace, mutanen da suke samar wa jaruman muryoyi ba labari kaɗai suke rubutawa ba.
Aikin na buƙatarsu su rikiɗe su juye su zama jaruman kamar yadda jarumai masu wasa ke yi idan aka ba su rawar da za su taka a fim.
"Kowanne wane mutum mai ilimi zai iya karanta abu, amma ba kowa ba ne zai iya yin fassara kuma ya yaɗa abin da zai sosa rai. Idan aka buƙaci ka ce "na gode" za ka iya yin hakan kara zube babu wani abun jan hankali.
Amma idan aka buƙaci ka nuna da gaske kake yi, hakan na buƙatar wani tunani na daban da kuma ƙwarewar aiwatar da hakan," Stévy ya bayyana.
"Amon da muryar da yadda za ka furta kowacce kalma dole su zo daidai da jigon da tsarin fim ɗin."
A cewar ɗan kasuwa ɗan ƙasar Gabon ɗin, harkar naɗan murya a baya bayan nan tana muradin kari Afrika, musamman ma idan wani aiki na daban yana da mutanen da musamman yake so su kalla.
Game da kuɗin da ake ganin wannan fannin zai samar, shugaban na kamfanin Gemini ya bayyana cewa a wasu ayyukan, mai yiwuwa ne mutum ya samu ladan dalar Amurka $500 a aikin naɗar muryar na daƙiƙa uku.
Abu kaɗai da mutumin da yake so ya zama mai aikin naɗar murya yake buƙata kafin ya fara aiki a wannan fagen da ke bunƙasa cikin hanzari shi ne "daddaɗar murya". Bayan wannan kuma, akwai kamfanin Stévy.