Lamine, wanda ke zaune a babban birnin Senegal na Dakar, ya riga ya yi suna a matsayin ƙwararren fasihi mai zane-zane na barkwanci.

Daga Firmain Eric Mbadinga

Lamine Dieme da Tyty Louis Essongue ba su san juna ba. Suna zaune a wurare daban-daban da ke da nisan dubban kilomitoci da juna a ƙasashe daban-daban, kowannensu cikin jin daɗin irin ƙirƙire-ƙirƙiren da suke yi da ke nuna ainihin asalinsu.

Abin da ya haɗa waɗannan 'yan Afirka biyu - ɗaya ɗan ƙasar Senegal da ɗayan kuma daga Gabon - sha'awa ce game da salon labarun barkwanci wanda ya haifar da kyan gani tare da bayyanar da nahiyar ga masu sauraro a faɗin duniya.

Lamine, wanda ke zaune a babban birnin Senegal na Dakar, ya riga ya yi suna a matsayin ƙwararren fasihi mai zane-zane na barkwanci.

Kamar shi, mazaunin Libreville Tyty sananne ne mai bayyana baƙaƙen fata a dukkan ayyukansa ta hanyara amfani da launuka masu ƙarfi da layi da siffofi don watsa wa masu sauraro a duniya.

A al'adar yawancin masu zane-zane na Afirka, dukansu biyu suna ƙoƙari don tabbatar da cewa zane-zanensu yana da tambarin nahiyar amma duk da haka ya dace da masu sauraron duniya.

Salo daban-daban

Hotunan raye-rayen Lamine galibi suna kan batutuwan zamantakewa ne kamar siyasa da yanayin tattalin arziki. Daya daga cikin fitattun ayyukansa shi ne wasan ban dariya mai suna "Patrie", wanda ke hada labarai da fassarori kan manufar ƙasar haihuwa.

Bayar da labarin ya fara ne da tarihin Afirka - wanda aka yi wa tambari da alamar bauta da tashin hankali da ƙaura - kafin a canza zuwa tarihin Senegal na baya-bayan nan, tare da abubuwan da mai zane ya samu.

Lamine ta shaida wa TRT Afrika cewa " fasahata gado ce ta mahaifina, wanda ya kasance mai zane-zane. Tun asali ni mai zanen barkwanci ne."

Yayin da aikin Lamine ke nuna abubuwan da ke faruwa a yanzu, Tyty ya fi karkata ga almara. Dan kasar Gabon mai shekaru 29, ya hada kai kan ayyuka bakwai tare da samar da wasu fina-finan barkwanci guda biyu da sunansa, "Dans l'ombre du soleil" da "Rendjegho".

Kamar takwaransa na Senegal da ke tashe, Tyty yana son zane-zane da wasan ban dariya ta hanyar yin duba kan yanayin wurin da yake rayuwa, musamman ta wurin dangi na kusa. Mahaifiyarsa, ƙwararriya ce a fannin samar da kayayyaki, ita ma ta taka muhimmiyar rawa wajen haɓakarsa a matsayinsa na mai fasaha.

"A koyaushe ina sha'awar zane-zane, galibi bayan ganin zane na mahaifiyata. Amma wata goggota ce ta fara saka ni a harkar zanen barkwanci. Ta ba ni kyautar 'The Adventures of Tintin', littafin wasan barkwanci na farko da na fara riƙwa," Tyty ya tuna.

Bayan samun ilhama kan abin da ya gani da wanda ya karanta, Tyty ya fara zane-zane, fiye da yadda mahaifinsa ke kallon lamarin, wanda da farko bai ga wani abin ƙaruwa a harkar zane ba.

Ba kamar Tyty ba, Lamine mai shekaru 40 ya sami ƙarin fahimta daga mahaifinsa fiye da mahaifiyarsa lokacin da ya yanke shawarar barin makaranta don ci gaba da zane.

Ba tare da damuwa ba, Lamine ya shiga harkar samar da wasan kwaikwayo na barkwanci a Dakar.

"Ko a makarantar firamare, nakan taimaka wa malamaina wajen zana hotuna don abubuwan da suka faru, kuma nakan taimaka wa abokan karatuna da zane-zane," in ji shi.

Tafiyar Lamine ta fara da sauƙaƙan zane-zane a cikin littafin rubutu. A tsawon lokaci, ya canza daga zane zuwa ƙirƙirar abubuwan ban dariya da koyo daga majagaba na fasaha.

Ayyukansa sun haɗa da shirin barkwanci na "Nenne Bébé Amine", wanda aka wallafa a cikin 2009 a harshen Wolof da Faransanci, "Caquette", wanda aka saki a cikin 2016, da "Lendemain Noir", wanda aka buga a cikin 2020. Na ƙarshen, wanda ya ƙunshi siyasa, da bude ido, ya sami lambar yabo a wani biki na Turai.

A halin yanzu Lamine yana aiki a kan wani shiri game da jaruman Senegal.

Lamine Dieme kuma tana gudanar da bita na ban dariya ga masu fasaha masu zuwa.

Duk batun ƙirƙira ne

Tyty ya yi imanin cewa ingantaccen aikin ƙirƙira yana buƙatar wahayi da jigo mai jan hankali, da ƙugiyar da za ta riƙe masu karatu.

Ilhamar tasa ta fito daga al'umma gaba daya. Al’amuran iyali da ilimi da al’amuran ƙasa, da rarrabuwar kawuna na nagarta da mugunta su ne sinadaran ƙirƙirarsa. Kamar yadda ya ce, manufarsa ita ce "ƙirƙirar wutar lantarki, ya danganta da halin da ake ciki" don wayar da kan jama'a game da al'amuran al'umma.

Har ila yau, wannan manufar ta bayyana a cikin wani zanen Lamine da aka buga a ranar 22 ga Afrilu, 2022, wanda ke nuna halin da mata masu juna biyu ke ciki da ake zargin ba a kula da lafiyarsu a asibitoci.

Labaran barkwanci, waɗanda aka daɗe ana ganin ba su da riba, musamman ga masu fasahar Afirka, yanzu suna samar da abin dogaro da kai.

Tyty, wanda a yanzu yana da iyali, yana iya tallafa wa iyalinsa ta hanyar aikinsa. "Da farko, abin da matuƙar wahala saboda dole ne ka tabbatar wa mutane cewa za ka iya, kuma kwangilolin ba a lokaci ɗaya suke zuwa ba duka. Amma tare da kyakkyawan tsari, yana yiwuwa," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Lamine ma, ya raba ƙafa a aikinsa, yana samar da littattafan yara na barkwanci da bidiyon kiɗa don masu fasaha, da fina-finai na hukuma. Har ila yau, lokaci-lokaci yana gudanar da bita kan barkwanci tare da wasu cibiyoyi.

Aiki mai faɗa

Dukansu Tyty da Lamine suna wakiltar ɗaruruwan mutane masu sha'awar zane da ban dariya. Sun yi imanin cewa ingantaccen tsari da ƙarin karɓuwa daga hukumomin jama'a zai bai wa masu fasaha damar samun rayuwa mai ɗorewa daga fasaharsu.

Lamine yana ba da shawarar ƙarin gidajen wallafe-wallafen da aka sadaukar don wasan barkwanci na Afirka da haɓaka hulɗa tsakanin marubutan nahiyar da masu sauraronsu.

Eric Nziengui, wani ma'aikaci ɗan ƙasar Gabon kuma mai sha'awar wasan barkwanci, ya ƙara da wannan ra'ayi. Ya yi imanin cewa wasan ban dariya sunahaɓaka harkokin sadarwa.

"Ni mai tattarawa ne, a karkashin gadona, ina da aƙalla labaran bakwanci guda 500 waɗanda nakan sake karantawa. A halin yanzu komai an mayar da shi harkar intanet, don haka za mu iya karanta wasan kwaikwayo kyauta a dandalin Facebook daban-daban ba tare da biyan kuɗi ba." " ya shaida wa TRT Afrika.

Eric na ganin makoma mai haske ga masu labaran ban dariya na Afirka, wanda ya yi imanin ya kamata ya nuna gaskiyar tarihin nahiyar.

"Wannan ita ce damar da muke da ita don nuna jarumanmu, da tsayin dakarmu a zamanin mulkin mallaka da kuma manyan daulolinmu na baya da masarautunmu daban-daban. Dole ne masu fasaha na Afirka su ƙirƙiro jaruman Afirka don matasa su gane kansu a cikin wannan tsafiya."

Don masu sha'awar littafin barkwanci irin su Eric ne masu fasaha irin su Lamine, Tyty da ɗaruruwan wasu a faɗin nahiyar ke ƙoƙarin rubuta labaran jarumai da isar da darajoji masu tushe a Afirka yayin da suke nishaɗantarwa da ilimantarwa.

TRT Afrika