Wangui Waweru ta kasance a harkar kasuwancin dodon kodi na kusan shekara biyar. Hoto: TRT Afrika

Daga Samuel Messo

TRT Afrika, Nairobi, Kenya

Watarana Wangui Waweru ta kasance a cikin bas tare da wani dan Kamaru daga Babban Birnin Uganda wato Kampala a farko-farkon shekarar 2018 a hanyarsu ta zuwa Nairobi.

Ashe wannan haduwar ta su ita ce za ta yi sanadiyar canja mata rayuwa.

A lokacin da suke tattaunawa, sai dan Kamarun ya bude kwanon abincinsa na rana, ya yi wa Wangui tayin cin abincin nasa mai dadi, sai Wangui ta ki amsa tayin, amma daga bisani ta amince ta dandana kadan.

“Kin san me kika dandana?” mutumin ya tambaye ta, kasancewar ya san ba sanannen abinci ba ne a Gabashin Afirka, sai ta amsa masa da cewa ko dai “Mutton ne”? ta sake mayar masa da tambaya.

“A’a! dodon kodi kika ci,” in ji dan Kamaru. Wangui dama ta taba cin dodon kodi a baya, wanda ake kiransa da escargot. “Ba laifi,” in ji Wangui.

Wangui ta bayyana kiwon dodon kodi a matsayin kasuwanci na “musamman.” TRT Afrika

A tsakiyar zantarwarsu, sai ta fahimci dan Kamarun kasuwancin dodon kodi yake yi, inda daga nan sai ita ma ta fara sha’awar harkar bayan ta dawo Kenya, kawai sai ta fara kiwon dodon kodin.

Wangui, wadda uwa ce da ke rayuwa a wani karamin gari da ake kira Nakuru, sai ta fara tafiye-tafiye tsakanin kasashen Uganda da Kamaru domin harkokin kasuwancinta.

“Ina jin dadin harkar kasuwancin nan na dodon kodi,” inji Wangui. Hoto: TRT Afrika

“Kiwon dodon kodi abu ne daban daban. Kai said a wasu makwabtana suka nesance ni lokacin da fara. Ka san mutane da dama a kasarmu ba sa daukar dodon kodi a matsayin abinci,” in ji a tattaunawarta da TRT Afrika a gidanta da Nakuru.

A can karshen gidan Wangui, an gina wasu kananan wuraren kiwo da kowannensu zai dauki daruruwan dodon kodi.

Ana ciyar da dodon kodinne da kayan lambu da ake nomawa a wani lambu da ke kusa da ita, sai kuma bawon kwai da ake ba su domin su samu sinadaran calcium. Ana kiran gonar Wangui da suna Golden Snail Farm.

“Kiwon dodon kodi yana da riba sosai. Misali, ina tashar sinadarin slime a cikin dodon kodi wanda nake amfani da shi wajen hada man shafawa. Akwai nau’in cavier wanda shi ne ya fi tsada,” in ji ta cikin murmushi.

Ana amfani da bawon dodon kodin wajen kwalliya a wasu garuruwa. Hoto: TRT Afrika

Wangui wadda mahaifiyar yara uku ce tana taimakon matasa a yankin da take. Sun dage wajen kiwon dodon kodin, kuma sun fara amfani da bawon kodin wajen hada kayayyakin adon mata irin su dankunne da sauran kayayyaki suna sayarwa.

Wannan ya sa matasa da dama sun samu hanyar samun cin abinci.

Tana fata wasu ’yan kasashen Afirka za su karbi harkar kiwon kodin domin habaka tattalin arzikinsu. “Ina farin cikin sosai kiwon kodi na daukar dawainiyata.

Zan so in ga mutane da dama sun fara tunanin yin wasu abubuwa daban musamman a harkokin nomad a kiwo,” inji Wangui.

TRT Afrika