Rachel Kabue na daukar maguna daga tituna da suke bukatar wajen zama da kula da lafiya. Hoto / TRT AFrika

Daga Patrick Wanjohi

Maguna da dama a waje guda. Wannan ce hanya mafi sauki da za ka siffanta kokarin Rachel Kabue.

"Muna da maguna 635," in ji Kabue yayin tattaunawa da TRT Afirka, tana rike da wata mage a hannunta.

Adadin magunan ya ragu saboda muna bayar da kyautar wasu ga wadanda suke son rike su a matsayin 'ya'ya," in ji ta.

A 2013, Rachel Kabue, 'yar shekara 51, wadda wadda ake kira da "uwar maguna" a Kenya, ta fara aikin sadaukarwa na tattara maguna daga kan tituna tana ajiye su a gida.

Ta fara tare da daukar mage guda daya amma kafin ta ankara, sai ta dinga daukar da yawa a kowacce rana.

Tana kwashe maguna daga kan tituna, amma wasu kuma na nan a gaban gidanta da ke Nairobi, babban birnin Kenya.

Wurin ajiyar na taimaka wa magunan su samu iyalan da za su dauke su kula da su da zarar su samu lafiya. Hoto / TRT Afrika

Matar mai 'ya'ya biyar na kula da cibiyar Feline da ke yankin Utawala a Nairobi, wanda ke da nisan kilomoita 20 daga tsakiyar birnin.

Ana ajje mafi yawan magunan a wani waje na katako da ta samar a gaban gidanta. Sauran kuma na wajen da ta kira asibiti, wanda shi ma wani bangare ne na gidanta.

Rachel da iyalanta na rayuwa a wannan gida kafin ta koma wani wajen don samun damar gudanar da aikin hidimtawa al'umma.

A yayin da daya daga cikin ma'aikatanta ke tsaftace dakin da magunan ke kwana, za mu iya gani da jin kai komin maguna da yawa. Miyau, gashinsu da ya zuzzube da tsalle-tsallensu ne abun da ake iya tsinkaye a wajen. Wasun su na bacci, yayin da wasu ke kallon mu.

Kowacce rana ta kai komon maguna ce

Ana baiwa magunan abinci sau biyu a kowacce rana. A kowanne mako sun cinye kilo 12 na abinci, in jita.

Rachel ta ce Rachel ta ci gaba da cewa "Suna son naman kaza sosai, a ranakun da suke cin kaji, muna ba su ne da rana, saboda suna yin kamar ma ba su ci ba."

Ciyar da magunan wani nauyi ne da ya rataya kan duk masu son kyautatawa. Hoto / TRT Afrika

Rachel na da ayyuka sosai. A cikin 'yan mintuna tana amsa kiran waya daga mutane daban-daban da ke son karbar magunan su ci gaba da kula da su, inda wsu kuma suke kiran ta don bayar da taimakon abincin magunan.

A duk bayan makonni biyu da kubutar da magunan, Rachel na baiwa kowacce mage sunan da ya dace da da halayyarta.

Sunayen da suka fi shahara sun hada da Konde, ma'ana siririya a yaren Swahili, da Chai, ma'anar shayi a harshen na Swahili. ta ce tana da wani alkawali na musamman ga duk sunan da ta baiwa kowacce kyanwa.

Ta nuna min tabon yakushi da maguna da dama suka yi mata a yayin da take kula da su.

Ta ce yakushin, ba su dame ta ba saboda an san maguna da yin yakushi a matsayin hanyar nuna kin aminta da kai yayin da ka kusance su.

Rachel ta bayyana cewa ciyar da magunan da kula da lafiyarsu na da tsada, kuma tana yawan dogaro kan 'yan kudaden da take ajiyewa da kuma masu taimaka wa.

Kula da dabbobi na da matukar wahala idan suna da yawa haka, kuma saboda yadda maguna suke haihuwar 'ya'ya uku zuwa shida, zai iya yin wuya a iya kula da wannan adadi mai yawa a nan gaba.

Rachel Kabue ta mayar da gidanta wajen kula da maguna Hoto / TRT Afrika

Suna kokarin aiki tare da likitocin dabbobi wajen fidiye maza da mata saboda a takaita haihuwar su.

"Muna samun magunan da ke zuwa da juna biyu, kuma saboda ba kisa muke yi ba, sai mu kyale su su haihu, mu kula da jariransu na makonni takwas, wannan sai mu fidiye su," in ji Rachel a yayin da take cire faratan magen da ta makale a jikin rigar sanyinta.

Za su ci gaba da zuwa

Ta ce iyalinta, musamman ma yara, na taimaka wa wannan aiki nasu, kai har ma suna bayar da taimako wajen kwaso maguna daga kan tituna. Makotanta ma na taimakawa kokarin nata ta hanyar aiko da masu karbar maguna su kula da su.

A yayin da dukkan magunan ke tare da mu, muna fama da zubar da gashi, kuka d aihun su, da kyale suna zazzaga mu a yayin da muke cikin gida, in ji Rache a yayin da take zagayawa da mu cikin gidanta da ko'ina maguna ne, kuma ta nuna damuwa kan yadda adadin ke ta kara yawa.

Karancin waje na nufin ba za a iya ajje maguna da yawa ba kamar yadda ake so ba . Hoto / TRT Afrika

Ta fada wa TRT Afirka cewa "kwanakin baya mu samu wani fili a gabar Tafkin Victoria (Nisan kilomita 354 daga Nairobi) kuma mun fara gina sabon wajen kula da maguna a can."

"Wajen na da girma sosai, ba zai zama wajen ajje maguna kawai ba, har ma da sauran dabbobi da za a kubutar."

"A yanzu da mutane ke saurin yaba wa wannan kokari, na san za su ci gaba da zuwa, karin maguna za su ci gaba da zuwa kuma ina farin ciki da karbar su tare da ajje su da ba su kulawar da suka cancanta." in ji Rachel.

A yayin da take rako ni waje daga cikin wajen kula da magunan, ta bayyana cewa yana da muhimmanci a wayar da kan jama'a sosai kan nuna so da kauna ga maguna, kuma mutane a koyaushe du dinga kai rahoton duk wata mage da suka gani a cikin mawuyacin hali.

A gaban kofar gidanta wasu mata matasa dauke da jariran maguna sun gaishe mu. ta kawo wa Rachel su, wadda ta yi farin ciki da karbar su tana cewa har ta rada musu suna.

TRT Afrika