A shekarar 2013 ne Patoranking ya yi fice tare da samun karbuwa daga masoyansa bayan fitar da wakarsa mai suna Alubarika./ Hoto:   Patoranking/Instagram  

Tauraron mawakin nan ɗan Nijeriya Patrick Nnaemeka Okorie wanda masoyansa suka fi saninsa da Patoranking ya kammala karatunsa a Harvard Business School da ke ƙasar Amurka.

Mawaƙin "My Woman, My everything" ya sanar da labarin kammala makarantar ne a shafinsa na Instagram a ranar Lahadi.

"Barka dai sabon ɗalibin '@harvardhbs Alumnus' da yardar Allah," kamar yadda ya rubuta a shafin, tare da wallafa hotuna da ya yi daga makarantar.

Bayan fitar da sanarwar, fitattun mutane ‘yan Najeriya da masoya wakoƙi sun yi ta tura sakon taya mawakin murna.

A 'yan kwanakin nan ne Patoranking ya karaɗe kafafen yada labarai bayan da gidauniyarsa tare da haɗin gwiwar cibiyar fasaha ta ALX Afirka ta sanar da shirin bayar da tallafin karatu a fannin nazarin bayanai da fasahar Cloud Computing da kuma fannin gudanarwa ga matasan Afirka.

Fitattun mutane sun taya mawakin murnar samun nasarar kammala karatunsa a Harvard Business School. Hoto: Patoranking

“Manufarmu ita ce samar wa ‘yan Afirka mutum miliyan daya ayyukan yi nan da shekaru 10 masu zuwa. Mun yi imani da ɗimbin matasan da muke da su masu hazaka da kuma kawo sauyi a Afirka sannan za mu ci gaba da ƙalubalantar rashin daidato a fannin samun kuɗi da ke hana matasan fitowa,” in ji Patoranking a wajen ƙaddamar da taron.

Matashin mawaƙin mai shekaru 33 ya yi fice ne bayan waƙarsa da ya fitar mai suna Alubarika a shekarar 2013.

Waƙar Patoranking mai suna "Daniella Whine" da "My woman, My everything" sun kasance kan gaba a rukunin wakoƙi 10 na MTV base Official Naija.

Matashin mawaƙin ya lashe lambobin yabo da dama, ciki har da Kyautar 'Sound City Viewers Choice Awards' da kuma bidyon waƙarsa ta 'Heal the World' wadda ta fi fice.

TRT Afrika