An zaɓi Burna Boy daga Nijeriya a matsayin tauraron da ya fi kowa iya rera wakoƙi kai tsaye. / Hoto: AP  

Shirin karrama taurari na BET ya sanar da sunayen mawaƙan da za a zaɓa domin samun lambar yabo a fagen salon wakoƙin Hip Hop na wannan shekara, kuma a bana taurarin Afirka ne suka mamaye rukunin matakai da dama da aka ware.

Daga cikin fitattun 'yan Afirka da aka zaɓa, akwai Burna Boy wanda ake sa ran zai lashe kyautar tauraron mawaƙi da ya fi kowa iya rera waƙa kai- tsaye.

Tauraron mawaƙin ɗan Nijeriya zai fafata da fitattun manyan mawaƙa da duniya ta san da zamansu kamar Kendrick Lamar da Nicki Minaj da Travis Scott da dai sauransu.

A fagen kyautar 'Best Flow category' a duniya ODUMODUBLVCK yana kan gaba, ɗan gambarar mawaƙin daga Nijeriya zai fafata da mawaƙan Afirka ta Kudu biyu wato Maglera Doe Boy da Blxckie, da kuma wasu daga Birtaniya Ghetts da Stefflon Don, a cikin wannan rukuni mai matukar zafi.

Kyautar BET Hip Hop ta biyo bayan nasarar da aka samu kwanan nan na lambobin yabo na BET, inda taurarun Afirka a fannin wakoƙi suka mamaye rukunai da dama.

Tyla da Makhadzi daga ƙasar Afirka ta Kudu da Tems daga Nijeriya, duk sun karbi kyautuka masu daraja.

Taron ba da kyautar BET Hip Hop na 2024 zai gudana ne a birnin Las Vegas a karon farko a ranar 15 ga Oktoba. Shugaba kuma wanda ya assasa BET Scott Mills ya nuna farin cikinsa game da kawo shirin zuwa birni wanda aka san shi da annashuwa da karsashi da kuma tarihi a fannin nishaɗi.

TRT Afrika