Sarjo Baldeh ta yi matukar alfahari da nuna kwarewarta a dandalin da ya shafi kasa da kasa. Hoto / Sarjo Baldeh  

Daga Pauline Odhiambo

Sarjo Baldeh ba 'yar jaridar da aka saba gani bace. Ta kware wajen daukar hoton wasanni sanye da hijabi kuma da wuya kamaranta ya gaza daukar duk wani kwallo da aka buga a filin wasa, sakakkun kayan jikinta suna bin iska yayin da take gudun bin 'yan wasa.

Tana ba da labarinta gaba-daya cikin madubin kamaranta kuma ba kasafai take iya barin wani abu ya wuce ta ba. Sai dai ta samu sauyi cikin kankanin lokaci sa'ilin da aka soma buga gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) na shekarar 2023, inda aka mayar da hankali kan ‘yar kasar Gambiya mai shekaru 21, wadda aka fi sani da ‘Baldezz,’ ga mabiyanta a shafukan intanet.

Ta kafa tarihi a matsayin matashiya mafi karancin shekaru kuma mai daukar hoto ta farko daga Gambiya a gasar AFCON.

"Hoton tawagar 'yan wasa a yayin soma buga wasa sun fi wahalar samu," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika cikin murmushi.

"A wannan lokacin ne kowane 'dan jarida mai daukar hoto yake kokarin samun cikakkiyar hoton tawagar."

Sakin Fuska a ko da yaushe

Fuskarta cike da annuri da yawan murmushi ta dauki hankalin masu kallo a fadin duniya yayin da take aiki da kuzahari ta kowanne gefen filin wasa - saurin daukar hoto kamararta wajen cafke duk wani da ya dauko ya hango a wasan filin da ake bugawa.

"Dole ne ka kasance a wurin da ya dace kana ka kasance cikin hanzari a kowace hanya da ka samu," a cewar Sarjo, wacce sha'awarta ta daukar hoto ya samo asali daga wani shirin makaranta yayin da take aji tara.

"Na yi kuskuren komawa baya yayin daukar hoton tawagar, kuma nan take wasu 'yan jaridu masu daukar hoto suka sha gabana cikin sauri, hakan ya hana ni ganin tawagar.''

"An yi sa'a, wajen nasarar matse kaina cikin tcunkoson masu daukaer hoto kana tsugunna kusa da wani dan jarida wanda ya ci gaba da daidaita kyamararsa a saman kaina yayin da muke daukar hotunanmu," in ji ta, tana mai kari da wasu kalubale da ta fuskanta yayin da take aiki a sana’ar da maza suka mamaye.

Daukar hoton 'ƴan wasa yayin da tsakiya buga wasan kwallonsu na daga cikin kwarewar aikin da matshiyar ta fi kware akai. Hoto / Sarjo Baldeh

Shahara ta kafofin Intanet

Daukar hoton 'yan wasan a fagen filin wasa yana da matukar sauƙi ga mai daukar hoto wacce aka ba ta kyautar kyamararta ta farko bayan kammala karatunta na sakandiri.

Ta bunkasa fasaharta a tsawon shekarun nan- tana zuwa taron bukukuwan aure da sauransu don samar da hotuna masu kyau gaske.

"Na yanke shawarar daukar hotunan wasanni ne domin ba kowa bane yake mai da hankali wajen samun kwarewa a fannin.'' in ji matashiyar mai daukar hoto.

"A mafi yawan lokuta ni kadai ce mace 'yar jarida mai daukar hoto a wasanni da da dama, kuma hakan ne ya sa mutane suke daukar hotuna na don daura wa a shafukansu na intanet."

Inda akasarin masu daukar hoto sukan sanya wando ko guntun wando don samun saukin motsawa, Sarjo ta ce ta fi samun kwanciyar hankali yayin da take sanye da rigar da ta sake jikinta – salon shiga mai kyau da ya dace da addininta na musulumci.

"Ina jin dadi a duk lokacin da na rufe kai zuwa kasa. A lokacin ne zan iya yin duk abun da zan iya ta hanyar gudu da tsalle yayin da nake sanya da irin wannan tufafin.”

A wasannin AFCON na 2023, hotunan Sarjo na daukar hotuna a filin wasa sun yi ta yaduwa a shafukan intanet.

Sai dai zuwanta wasannin AFCON bai zo sauki ba.

TRT Afrika