Daga Brian Okoth
Hukumomin Afirka ta Kudu sun bayyana cewa sarauniyar kyau Chidinma Adetshina da mahaifiyarta za su rasa takardarsu ta zama 'yan ƙasa a Afirka ta Kudu, kana za a gurfanar da su gaban ƙuliya bisa zargin mallakar takardun zama ‘yan ƙasa ba bisa ƙa’ida ba.
Darakta-Janar na Sashen Harkokin Cikin Gida na Afirka ta Kudu Tommy Makhode ne ya bayyana hakan, a yayin bayyanarsa a gaban kwamitin majalisar dokokin ƙasar kan harkokin cikin gida a ranar Talata, 29 ga watan Oktoba.
Makhode ya ƙara da cewa sashen ya nemi mahaifiyar Adetshina ta yi ƙarin haske game da yadda ta mallaki takardun shaidar zama 'yar ƙasar Afirka ta Kudu waɗanda ta yi amfani da su wajen shigar da Adetshina ƙasar a lokacin da ta haife ta a shekarar 2001.
Sai dai zuwa ranar da wa'adin da aka ƙayyade wato ranar Litinin, 28 ga watan Oktoba ya cika — Mahaifiyar Adetshina ba ta gabatar da takardun da ake buƙata ba.
Kammala bincike
Kazalika, Makhode ya ce Adetshina ba ta samar da takardun shaidar da ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar take buƙata don a gudanar da bincike a kansu ba.
Babban daraktan ya ce sai da lamarin ya kai ga hukumar binciken manyan laifuka (DPCI), wadda tuni ta kammala bincikenta kan batun da ya shafi Adetshina da iyayenta.
"Yanzu DPCI na jiran hukumar hukunta masu shigar da ƙara ta ƙasa (NPA) ta ba su shawara kan mataki na gaba," a cewar Makhode.
Haka kuma babban daraktan ya ce zuwa lokacin, Adetshina da mahaifiyarta ba su amsa takardar da ta buƙaci su bayyana ''dalilan da za su ba da damar kar a janye musu takardarsu ta 'yan ƙasa ba.''
Tuhumar laifuka
"Har ya zuwa wa'adin ranar Litinin da aka sanya, ba mu samu amsa ba, don haka ma'aikatar za ta janye takardun shaidar kamar yadda dokar Afirka ta Kudu ta tanada," in ji Makhode.
Mataimakin ministar harkokin cikin gida na Afirka ta Kudu Njabulo Nzuza ya shaida wa majalisar dokokin ƙasar a ranar Talata cewa, za su miƙa batun ga sashen da ke kula da manyan laifuka don "gurfanar da su bisa laifin."
Nzuza ya ce gwamnati ba ta da wani zaɓi da ya wuce ta gurfanar da Adetshina da mahaifiyarta sakamakon rashin ba da haɗin-kai da suka yi ''a lokacin da ya dace'' kan binciken.
Adetshina, mai shekaru 23, ta kasance ɗaya daga cikin 'yan takara 13 da suka rage a gasar sarauniyar ƙyau ta Afirka ta Kudu a shekarar 2024, amma sai ta janye kwana biyu kafin ranar ƙarshe na gasar, wadda aka gudanar a ranar 10 ga watan Agusta.
Janyewa daga gasar Sarauniyar kyau ta Afirka ta Kudu
Sarauniyar, wadda ta taso a yankin Soweto da ke Afirka ta Kudu, ta bayyana ɗaukar matakin janyewarta da "mawuyaci."
A lokacin, Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Afirka ta Kudu ta sanar da cewa ana bincike kan mahaifiyarta wadda ake zargi da satar shaidar asalin ƙasar da ta fito.
Ma’aikatar ta ce mahaifiyar Adetshina, wadda ‘yar kasar Mozambique ce, ana zarginta da sace takardar shaidar wata 'yar Afirka ta Kudu a shekarar 2001 don shigar da suna matashiyar 'yarta Adetshina.
Mahaifin Adetshina dai ɗan asalin Nijeriya ne.
A Afirka ta Kudu, gwamnati na da 'yancin ƙwace wa mutum takardar shaidar zama ɗan ƙasa idan har ''ya saba tanade-tanade'' dokar zama ɗan ƙasa.
Lashe gasar Miss Universe ta Nijeriya a 2024
Bayan janyewa da ta yi daga gasar sarauniyar kyau ta Africa ta Kudu, Adetshina ta amsa gayyatar shiga gasar Miss Universe Nigeria ta 2024.
A ranar 31 ga watan Agusta ne aka karrama ta a matsayin wadda ta lashe gasar kyau ta Miss Universe Nigeria a wani taron biki da aka gudanar a birnin kasuwanci na jihar Legas.
Adetshina za ta fafata da sarauniyar kyau ta Afirka ta Kudu a 2024 Mia le Roux da wasu mata sama da 100 a gasar Miss Universe a birnin Mexico.
A ranar 16 ga watan Nuwamba ne za a kammala gasar.