Daga Brian Okoth
A yau mawaƙi ɗan Tanzaniya, Professor Jay yana da rai cikin wani irin yanayi da mutane ke kwatantawa da warakar al'ajabi daga cutar da ta kassara shi a baya.
Tsawon kwanaki 462 — wato shekara ɗaya da wata uku, mawaƙin mai shekaru 48 ya kasance kwance a gadon asibiti, yana fama da matsananciyar cutar ƙoda.
Bayan sallamarsa daga asibiti, ya saki wata waƙa a Nuwamban 2023, yana bayyana godiyarsa ga Ubangiji saboda warakar da ya samu.
A wakar da ya yi wa laƙabi da "Kwanaki 462", Professor Jay, wanda asalin sunansa shi ne Joseph Haule, ya zayyano gwagwarmayarsa ta jinya.
Cikin waƙar da ke da tsawon minti 8, ya faɗi baituka masu cewa: "Na shiga yanayi kala-kala cikin kwanaki 462 da na yi ina yin jinya. Dole na gode wa Allah saboda bari na da rai. Kuma ina godiya ga 'yan-uwana 'yan Tanzaniya saboda addu'o'insu da gudunmawarsu."
Professor Jay ya bayyana cewa a lokacin jinyarsa, akwai lokutan da na kasance kan injin taimaka wa numfashi. Huhunsa ya kasance cike da ruwa, ƙodarsa ba ta aiki, kuma zuciyarsa tana bugawa a hankali.
A wasu lokuta, hawan jininsa ya zamo sama sosai. Kuma an yi masa tiyata a maƙogoro, yayin da ake masa wankin ƙoda.
An fara bayyana jinyar Professor Jay a farkon 2022, lokacin da matarsa Grace Mgonjo ta faɗa a wata hirar rediyo cewa an kwantar da mawaƙin a babban birnin kasuwancin Tanzania, Dar es Salaam.
Yayin da ake cikin yanayin matsin tattalin arziƙi, abokan mawaƙin sun yi shelar neman taimako don tara kuɗi a Fabrairun 2022.
A lokacin, wani abokin Professor Jay, mawaƙin AY ya ce ana kashe shiling miliyan 4 na Tanzaniya kan jinyar majinyacin, wanda ya kai kimanin dala 1,500, duk mako.
Bayan neman taimakon kuɗin, Shugabar Tanzaniya Samia Suluhu ta yi tayin biyan kuɗin jinyar Professor Jay, a cikin gida Tanzaniya da ma a wajen ƙasar.
A Mayun 2023, mawaƙin ya fitar da saƙo a shafukan sada zumunta yana godiya ga Shugaba Suluhu saboda tallafa masa.
A Satumban 2024, Professor Jay wanda ya fara murmurewa, ya fitar da faifan bidiyo da ke nuna ma'aikatan asibiti suna taimaka masa yin tafiya. A bidiyon da ya yi yawo, majinyacin yana shan wahalar takawa a keken tafiyar guragu.
Da yawa daga masoyansa sun ce wani "babban abin al'ajabi" ne cewa mawaƙin ya fito daga irin wannan jinya.
Wasu bidiyoyi da hotuna na mawaƙin sun nuna shi yana cikin ƙoshin lafiya, kuma yana godiya saboda samun wata damar rayuwa.
Professor Jay wani mawaƙin gambara ne na harshen Swahili, wanda ya samu shuhura a Tanzaniya da yawancin gabashin Afirka a ƙarshen shekarun 1990 da farkon shekarun 2000. Kuma ya lashe kyautuka da dama saboda shahararrun waƙoƙinsa kamar "Nikusaidiaje", "Zali la Mentali", "Hapo Vipi", da "Ndivyo Sivyo", da sauransu.
A 2015, Professor Jay ya yi takarar ɗan majalisa, inda ya lashe mazaɓar Mikumi. Yankin yana gundumar Morogoro a gabashin Tanzaniya.
Jay, wanda ya yi takara a Jam'iyyar CHADEMA, ya samu ƙuri'u sama da 32,000, inda ya doke ɗan takarar jam'iyya mai mulki, wanda ya samu ƙuri'u sama da 30,000.
A Oktoban 2020, ya gaza sake lashe kujerarsa a Jam'iyyar CHADEMA, inda ya sha kaye a hannun ɗan jam'iyyar CCM. Jay ya samu sama da ƙuri'u 17,000, inda abokin takararsa ya lashe zaɓen da ƙuri'u 31,000.