Masingisa: Mai shirya fim dan Tanzaniya da ke inganta rayuwar makiyayan kabilar Maasai

Masingisa: Mai shirya fim dan Tanzaniya da ke inganta rayuwar makiyayan kabilar Maasai

Masingisa dan ƙabilar makiyaya ta Maasai ya koyi shirya fim ta intanet ba tare da samun horo na musamman ba.
Broad Masingisa na samun hikimar jigon fina-finansa daga kwarewarsa kan al'adunsu na Maasai. Hoto \ TRT Afrika

Broad Masingisa ya shiga harkar fina-finai ne bayan da ya ji haushin yadda ake bayyana al'ummarsa ta Maasai, wata al'ummar makiyaya a gabashin Afirka da ke kan iyakar Kenya da Tanzaniya.

Maasai sun mamaye manyan filaye da ke maƙwabtaka da sanannen wurin shaƙatawa na gandun namun daji na Serengeti da kuma dutse mafi tsayi a Afirka, Dutsen Kilimanjaro.

Tsarin rayuwarsu ta zama a dazuka kuma suke da adon sutura, na da tasiri sosai wajen jan hankalin masu yawon bude ido na duniya ga al'adunsu.

Amma kuma mummunar fahimta ta baibaye jama'ar da alakarsu da makotansu manoma, kuma a cikin wasu fina-finai ana yawan bayyana salon rayuwar Maasai a matsayin na jahiliyya.

Masingisa, da ya fito daga yankin Morogoro na Tanzaniya, ya shaida arangamar da ake yi tsakanin manoma da makiyayan kabilar Maasai, wanda a wasu lokutan ake jikkata makusantansa.

A shekarar 2018 sai ya fara shirya fim, duk da bai samu wani horo ba game da sana'ar. Babbar manufarsa kwaya tal itace ya ilmantar da jama'arsa da makotansu kan zama lafiya tare, da kuma sauya mummunar fahimtar da aka yi wa kabilar Maasai.

Haka kuma yana fatan taimakawa jama'ar Maasai makiyaya kan su rungumi tsarin rayuwa na zamani mai amfani, ba tare da sun bar dimbin al'adunsu da suka gada ba.

Broad Masingisa ya ce da fari jama'arsa sun nuna adawa ga shigar sa harkar shirya fim. Hoto \ TRT Afrika

Ana shirya fina-finansa a yarukan Maasai da Swahili.

Wannan mai shirya fina-finai ya koyi shirya fim ta hanyar kallon wasu fina-finan, kamar yadda ya shaida wa TRT Afirka.

Ya ce "Ina yawan kallon fina-finan wasu al'ummun daga masana'antun fina-finai na cikin gida da na kasa da kasa, da manufar koyon yadda suke rubuta labaransu da yadda suke tsara fina-finan."

Masingisa ya ce zai iya kallon fim guda daya sama da sau biyar don kawai ya samu kyakkyawar fahimtar me yake dauke da shi, sannan ya kuma koyi dabarun bayar da umarni da daukar fim. rashin horo na musamman a wannan aiki mai wuyar sha'ani ya zo da kalubale.

A 2018, ya hakura da wani shirin fim saboda rashin kyawun sauti da hotuna. Ya ce fim din ba shi da cigaba sakamakon yadda shi kansa ba shi da dabarun bayar da umarni.

Broad Masingisa na fatan tasirin fim zai sauya dabi'un jama'ar Maasai. Hoto \ TRT Afrika

Rashin nasarar ya karya masa zuciya inda yake fuskantar suka daga jama'a da suke masa kallon yana bata lokacinsa wajen wannan aiki mai wuyar sha'ani ba tare da ilin yin sa ba.

Duk da ya yi asarar kudade da lokaci, amma bai karaya ba. Ya ci gaba inda ya fitar da fim mai suna Gisoi.

Jigon shirin fim din ya shafi wani mutum wanda ya ajje abun wuya a kan wata uwa mai ciki - al'adar da ke ba shi damar kama macen aure idan har wannan matar ta haifi 'ya mace.

Wannan tsohuwar ta'ada ta hana yara mata 'yancin zabar mijin aure da suke so idan sun girma.

A watan da ya gabata Gisoi ya lashe gasar fim mafi kyau a Bukin Fina-Finai na Morogoro.

Fina-finan Broad Masingisa sun lashe kambi da yawa tare da ba shi shuhura a Tanzania. Hoto \ TRT Afrika

Masingisa ya ce yana fatan ya ga sauyi a halayyar mutanesa game da shirya fim wand ayake wa kallon sana'a ce kamar kowacce.

Yana kuma so da kaunar matasan al'ummarsa su yi amfani da basirarsu wajen ilmantar da mutane ta hanyar shirya fim wand ahanya ce mai sauki ta isar da sako.

Ya kuma halarci tarukan karawa juna sani da dama, wanda Hukumar Kula da Al'adu ke shiryawa don koyar da dokokin shirya fim.

A baya-bayan nan, yana sa ran fara shirya gajerun fina-finai tare da tallafi daga wani kamfanin China da ke da manufar tallata Tanzaniya da wuraren yawon bude ido da ke kasar. Shugabar kasar Tanzaniya Samia Saluhu ma na cikin wannan aiki.

Matashin na kuma shirya casu, inda matasa suke muhawara kan al'adunsu, sannan yana shirya fina-finan gaskiya da manufar adana al'adunsu masu kyau don amfanin al'ummu masu zuwa a nan gaba.

TRT Afrika