Daga
Firmain Éric Mbadinga
Idan ana batun nishadantar da mutane, Big Row yana da salo iri-iri na fitar da amon sauti.
Mawakin gambarar mai babbar murya dan asalin kasar Gabon, wanda asalin sunansa Ivan Koumba yana amfani da salon da ke hada kade-kaden al'adun gargajiya na Gabon da na zamani, wanda hadin ke bayar da salon da yake kira da "Tradigansta Flow".
"Waiwayen baya na cikin abubuwan da nake yi, domin hakan ne zai taimaka wajen sanin asalinmu. Sannan a kasarmu, fifita al'adunmu na da matukar tasiri domin fahimtar asalina.
Salon gambarata shi ne bayyana kai na a yadda nake," inji shi a tattaunawarsa da TRT Afrika.
Idan har za a yi la'akari da yawan sauraronsa da ake yi, da kuma jawaban da ake yi a karkashin faya-fayen wakokinsa, to lallai za a iya cewa Big Row yana da masoya a fadin Afrika da ma duniya baki daya.
A karkashin wakarsa ta "LA FINITION" a YouTube, wani mai bibiyarsa mai suna @Kyoko973 ya rubuta cewa, "Gaisuwa daga Guyana! Duk da cewa akwai teku da ya raba mu, tsarin hawa da saukar muryarka da salon wakokin suna kama da wakokinmu. Wannan wakar tana taba zuciya!"
Zuwa yanzu, za a iya cewa jajircewar Big Row ce ta jawo masa nasarori da dama, ciki har da zama na biyu a bikin kalankuwar Stars Festival of African Cultural Integration Sica karo na 17 da aka yi a Kamaru, inda mawaka daga kasashen Afrika 30 suka halarta.
Sakonni
A wakokinsa na gambara da yake yi harshen Guisir na mutanen Eshira, Big Row yana yawan yin magana a kan rayuwa da al'umma, da soyayya da al'adun Afirka da kuma bayyana alfaharinsa da nahiyar.
"A takaice dai ni mai kare al'adun gargajiya na Afirka ne," inji Big Row a zantarwarsa da TRT Afrika.
"Ina tunawatarwa kuma ina karfafa gwiwa, kamar misali a wakokin “Chasser le Nguembe” da “L'étoile de la famille” sannan ina ba da shawara.
Kamar a wakar " Boy a Change" inda na yi magana a kan muhimmancin fuskantar kalubale duk runtsi," in ji mawakin, wanda yanzu haka yake cigaba da zagayen kalankuwa.
Yadda yake kaunar Afrika da al'adunta na fitowa fili a cikin wakokinsa, inda yawancin wadanda suke cikin bidiyoyin sukan sanya tufafin da aka dinka da kayayyakin dinkin Afrika.
"Burkina shi ne in zagaye duniya domin in bayyana musu al'adun mutanen kasar Gabon da na Afrika baki daya," in ji mawakin.
Ya kara da cewa, "A sanadiyar wakokin da nake yi, yanzu na fara samun kudade."
Yanzu an fara kallon mawakin, wanda ya fara a shekarar 1998 a matsayin abin koyi kuma jakadan al'adun mutanen Bantu.
Ya fara bayyana kansa ne a birnin Port-Gentil na Gabon tun yana makarantar sakandire.
Duk da yadda ya faro harkar da kafar dama, bai tsaya da karatu ba, sai da ya kammala sakandire da jami'a. Don haka sai a shekarar 2007 ce mawakin wanda ya karanci bangaren lauyanci a jami'a ya fitar da kundin wakokinsa na farko mai waka biyar mai suna Syphonie D'Afrique.
A shekarar 2013, ya samu nasarar yin hadakar waka da fitaccen mawakin Najeriya Wizkid, inda suka sabunta wakarsa ta "Ole".
A Yunin shekarar kuma, bajintar da ya nuna a taron bikin Fête de la Musique ya lara haskaka tauraronsa a Gabon, wanda hakan ya kara masa jargin gwiwar hangen nesa.
" Ni dan Afrika ne. Wani yayana yana son sauraron wakokin gambarar Farasanci da Amurka, amma ni na fi so ya zama ina da salona na daban," in ji shi.
Big Row wanda yanzu ya bude kamfanin wakarsa, shi kadai ne mawakin gambara da ke amfani da harshen yankinsa a waka a kasar ta Gabon, waddda Farasanci ne harshen gwamnati.
Amma a wasu kasashen da suke amfani da Farasanci irin su Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo da Senegal akwai wasu mawaka masu irin salon Big Row irin su Dip doudou guiss da RJ Kanelierra kuma miliyoyin mutane suke sauraronsu duk da cewa da harshensu na gida suke amfani.