Abubuwan da Ndombe ya fi mayar da hankali a kan zane-zanensa sun haɗa da tufafi masu launi. Hoto: Ndombe Sisqo

Daga Pauline Odhiambo

Kamar yadda wasu abokai suka fi saninsa da suna 'Les Noir,' mai zane-zanen DRC Ndombe Sisqo ya yi suna ne kan yadda ayyukansa ke nuna rayuwar baƙaƙen fata da kuma al'adun Afirka.

Yin zane-zane masu launuka masu haske na nuna cewa ya girma ne a babban birnin DRC, Kinshasha - wata babbar cibiyar kayan ƙawa ta Afirka, wacce kuma ta shahara wajen kyawawan kade-kade a nahiyar.

Abubuwan da Ndombe ya fi mayar da hankali a kan zane-zanensa sun haɗa da tufafi masu launi, tare da wasu zane-zane da ke nuna rediyo a jiki da rubutun "Africa Radio".

Ɗaya daga cikin zane-zanen nasa, mai taken 'All Eyes on Me,' ya haɗa da launuka kamar rawaya da ruwan hoda da kore, da fararen launuka, wanda ke haifar da tasiri mai ban sha'awa ga batun launin ruwan kasa da launin fata.

Hoto: Ndombe 

'Daukar ido'

Ndombe ya shaida wa TRT Afrika cewa "A cikin ayyukana, ina zana haruffan da ke jan hankalin mutane."

"Dukkan abubuwan da na zana su ma suna da wani yanayi da ke ɗauke da tambayoyi da yawa. Wannan yanayi yana wakiltar haƙiƙanin gaskiya da yawa na duka batutuwan, da kuma bayyana ƙalubale da rikice-rikicen da yawancin mutanen Congo suka fuskanta."

Zanen zamani yana nuna al'amura masu sarƙaƙiya da ke daidaita duniyar da ke saurin canzawa cikin sauri.

Yawancin masu fasaha na zamani suna tayar da tambayoyi masu wuya ko masu jan hankali ba tare da bayar da amsoshi masu sauƙi ba.

Daya daga cikin zane-zanen da Ndombe ya fi so, 'Cracked People', ya bayyana fatansa na samun sauyi a fagen siyasa da tattalin arzikin Afirka.

"Muna bukatar sauyi. Mutanen Afirka na bukatar sauyi na gaske, amma duk abin da muke ci gaba da samu shi ne alkawuran banza," in ji shi.

"A matsayinmu na masu fasaha, alhakinmu ne mu shiga cikin tattaunawar siyasa don cim ma sauye-sauyen zamantakewa da tattalin arziki."

Hoto: Ndombe

'Tashi'

An baje kolin zane-zane na Ndombe a cikin Mujallar Mozaik kuma an baje kolinsu a duk duniya ciki har da Turai.

Wasu zane-zane na nuna zakaru, wanda ke nuna alamar fatan gamayya na Afirka na samun kyakkyawar makoma.

"Zane-zanen da ke nuna zakaru suna cikin jerin shirye-shiryena na ' farkawa da hankaltarwa'," Ndombe ya bayyana. "Zararan kira ne a farka a don gari ya waye," in ji Ndombe, wanda ya ƙware a fannin fasaha a Kwalejin Kiwon Lafiya ta Kinshasa.

Zakarun da yake sakawa a zanensa alama ce ta 'yan Afirka su farka.Hoto: Ndombe

A tsaye ƙiƙam

Ndombe yana ƙirƙirar zane-zane da ke nuna abokantaka da alaƙa. Yawancin zane-zane na nuna abota mai ɗorewa da zamantakewar ma'aurata.

Mata sun ƙawata gashin kansu salon na Afirka sun yi kwalliya da sarƙa da ɗan kunnem yayin da maza ke tsaye tamkar masu tsaro.

Wasu zane-zane suna nuna hotunan ma'aurata jingina da babura - a matsayin sananniyar hanyar sufuri a kasashen Afirka da dama.

"Ma'auratan suna nuna hadin kai da ƙaunar juna da kuma fatan alheri ga nahiyarsu," in ji Ndombe, mai zanen wanda yake kuma da fasahar yin magana da harsuna hudu.

Ndombe kan nuna salon gyaran gashin matan Afirka a zanen da yake yi. Hoto: Ndombe

Kowane ɓangare

Duk da cewa Ndpmbe ya fi son yin zanukan da suka shafi mata, to yakan yi na mazan ma.

"Na fi son zanen da ya shafi mara, musamman mata baƙar fata, saboda kyawunsu na musamman ne," in ji shi. "Zan yi farin ciki idan mace ta zama shugabar ƙasata, saboda duniya na buƙatar mata shugabanni."

A ƙoƙarinsa na fayyace kyawun 'yan Afirka, Ndombe yana yawan sanya wa matan da ya zana kayan ado na Afrika.

Ana sayen ayyukan zanen Ndombe a kan dubban daloli a kasuwannin duniya. Hoto: Ndombe

Zane mai araha

Ndombe yana aiki da jerin shirye-shirye don samun ƙarin abokan ciniki. "Mutane da yawa suna son sayen kayana, amma ba za su iya ba," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

"Don haka, zan ƙirƙiri ƙananan nau'ikan zane da mutane da yawa za su iya saye.

Ndombe ya fara zane-zane cikin ƙwarewa a shekarar 2020 amma ya kasance mai sha'awar fasaha tun yana yaro.

Malamansa sukan sa shi ya yi zane a kan allo domin abokan karatunsa su kwafa.

Shawararsa ga masu sha'awar fasaha? "Ku kasace kuna ƙirƙirar ayyukanku da kanku ban da satar fasaha," ita ce amsar da ya bayar a kan wannan tambaya.

TRT Afrika