Daga Charles Mgbolu
Ba shakka shekarar 2023 ta zama wacce fannin nishaɗantarwa na Afirka ya ga al'amura da yawa da suka haɗa da na ban mamaki da bukukuwan al'adu masu cike da karsashi da tarukan ba da kyaututtuka na ƙasa da ƙasa da sauran su.
Sannan kuma an ga wasu al'amuran masu ɗaga hankali a shekarar, ciki har da mutuwar fitattun mutane da ma rabuwar wata ƙungiyar mawaƙa da suka daina aiki tare.
A yayin da shekarar ke ƙarewa, TRT Afrika ta tattara wasu manyan al'amura da suka faru a duniyar nishaɗantarwa da suka shiga kundin tarihin 2023.
Kafa tarihi a duniya
Ba zai yiwu a kammala tattara bayanai kan shekarar 2023 ba tare da bijiro da batun kafa tarihin da wata ƴar Nijeriya Hilda Baci ta yi ba na yin girki har tsawon awa 93 ba ƙaƙƙautawa, kamar yadda Kundin Bajinta na Guinness World Record GWR ya bayyana.
Tabbatacciyar nasarar da ta samu, ya jawo mutane da dama a fadin Afirka ta Yamma sun shiga gasar son ganin sun zarta ta don shiga kundin tarihin.
Wata mawaƙiya ƴar Nijeriya Oluwatobi Kufejione ta shafe tsawon awa 200 tana waƙa, yayin da Joy Chukwudi ta gaza har ma ta sume a ƙoƙarinta na yi wa mutane tausa ta tsawon awa 75 ba hutawa.
Shi ma wani mutum Tembu Ebere, ya yi ƙoƙarin kafa tarihin yin kuka har tsawon sati ɗaya ba tsayawa, lamarin da ya jawo masa makanta ta wucin gadi, yayin da Enitan kuwa ya samu kansa a gadon asibiti bayan shafe awa 50 yana wankin kaya don kafa tarihi.
Kundin GWR bai tabbatar da ƙoƙarin waɗannan mutanen ba, saboda ya ce yana la'akari da kare duk wani abu da ka iya zama haɗari ga mutane.
Kazalika, sauran abubuwan bajinta da aka yi ƙoƙarin kafa tarihi a kansu sun haɗa da ɗaukar tsawon lokaci ana tafi a Uganda, inda mutum 926 suka yi ta tafi har na tsawon fiye da awa uku.
Akwai kuma Tonye Solomon, wani ɗan Nijeriya da ya yi taku 150 da ƙwallo a kansa, da Helen Williams, 'yar Nijeriyar da ta kitsa gashin kanti mafi tsawo a duniya, da ma sauran wasu ƴan Afirka da GWR ta tabbatar da bajintar tasu.
Kyautar fim da bukukuwa
An yi bikin ba da kyaututtuka na fina-finai na Afirka wato (AMVCA) a ranar 20 ga watan Mayu a birnin Legas na Nijeriya, inda fitattun masu shirya fim da suke da basira daga Gabashi da Yammaci da Kudancin Afirka suka karɓi kyaututtuka a matakai daban-daban.
Kazalika an yi was bukukuwan fina-finan daban-daban, kamar bikin fina-finan Afirka da bikin fina-finai na duniya na Marrakech, da kuma bikin masu shirya fina-finai na Afirka da Gabas ta Tsakiya.
Kungiyar masu shirya fina-finai ta Pan African (FEPACI) ta yi kiyasin cewa fina-finan Afirka sun bunƙasa sosai a shekarar 2023, inda masana'antar ke samun karuwa ta shekara-shekara har ta kashi 12.76%, wanda ya haifar da hasashen kasuwar za ta kai dalar Amurka miliyan 112.90 nan da shekarar 2027.
UNESCO ta ƙiyasta cewa masana'antar ta samar da ayyukan yi sama da miliyan 20 a cikin 2023, kuma ta ba da gudunmawar dalar Amurka biliyan 20 ga ma'aunin tattalin arziki na nahiyar.
Kyaututtukan waƙoƙi
Kamar fina-finai, waƙoƙin taurarin Afirka na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ake fitarwa daga nahiyar a 2023.
Ya zuwa watan Oktoban 2023, babbar manhajar wallafa sauti ta Spotify ta ba da rahoton cewa an saurari waƙoƙi sama da sau biliyan 15 a kafarta, inda aka fi yaba wa nau'in waƙoƙin Afirka Afrobeats na Yammacin Afirka, saboda babban tasirinsu a fannin kiɗa a duk faɗin duniya, yayin da taurarinsa suka sami lambobin yabo na kiɗa.
Mawaƙin Nijeriya Burna Boy ya lashe kyautar BET Best International Act a karo na 4, yayin da Rema ya lashe lambar yabo ta MTV Afrobeats mai tarihi a bikin ba da kyaututtuka na MTV da waƙarsa ta "Calm Down" da ya yi da mawaƙiyar Amurka Selena Gomez a watan Satumba.
Rema kuma ya karya tarihi ta hanyar kasancewa a saman jadawalin waƙoƙin Afrobeats a Amurka na tsawon shekara guda.
Mawaƙin Tanzaniya Diamond Platnumz shi ma ya yi rawar gani sosai a lokacin da ya zarce manyan mawaƙan Nijeriya Burna Boy da Asake don fitowa a matsayin 'Best African Act' a MTV Europe Music Awards a watan Nuwamba.
Mawakin Ghana Black Sherif shi ma ya lashe babbar lambar yabo ta ƙasa da ƙasa ta 2023 (BET Awards).
Kwalliya da zayyana
Fannin kayan ƙawa na Afirka shi ma ya yi haɓaka ta ban mamaki a shekarar 2023, inda hukumar UNESCO ta ba da rahoton cewa an samu fiye da dala biliyan 15 daga fitar da kayayyaki duk shekara, inda ake da yiwuwar ya ƙru da ninki uku nan da shekara 10 masu zuwa.
Manyan masu tallan kayan ƙawa na Afirka masu dumbin fasaha sun samu damarmaki na baje kolinsu a tarukan ƙasa da ƙasa da suka haɗa da a Paris da London da ma wajen tarukan mako-mako na Afirka.
Mace-mace
Sai dai kamar yadda aka sani rayuwa zaƙi da maɗaci ce, an samu mace-mace har da masu ɗaga hankali kamar na kisan da aka yi wa wani mawaƙin Afirka ta Kudu Kiernan Jarryd Forbe, da aka fi sani da AKA, ranar 10 ga watan Fabrairu.
An harbi mawaƙin mai shekara 35 ne tare da budurwarsa Tebello ‘Tibz’ Motsoane, a lokacin da suke dab da shiga motarsu bayan fita daga wani kantin cin abinci a birnin Durban.
Tuni aka kama mutum biyar da ake zargin su da hannu a kisan.
A watan Maris ma wani mawaƙin gambara na Afirka ta Kudu Costa Titch mai shekara 28 ya faɗi a kan dandamali lokacin da yake waƙa a wani bikin kalankuwa.
A wata sanarwa da iyalans suka fitar, sun ce ya mutu ne jim kaɗan da faɗuwar tasa.
Sannan a watan Satumba, masoyan wani fitaccen mawaƙi Ilerioluwa Oladimeji Aloba da aka fi sani da Mohbad sun shiga tashin hankali bayan samun labarin mutuwarsa.
Yanayin yadda mawaƙin mai shekara 27 ya mutu ya janyo zanga-zanga inda har ƴn sandan Nijeriya suka ƙddamar da bincike tare da kama wasu da ake zargi da hannu, amma har yanzu ba a samu wata hujja ba.
Sauran labaran da suka watsu
Mawaƙan Uganda Triplet Ghetto Kids sun sake fitowa a idon duniya inda har suka kai mataki na ƙrshe a gasar British Got Talent da aka yi a watan Yuni.
Ba wannan ne karo na farko matasan suka yi rawar gani a idon duniya ba, saboda ko a shekarar 2022 ma sun ja hankali a lokacin bude gasar kwallon ƙafa ta duniya da aka yi a Qatar.
Duk da cewa ba su yi nasara a gasar ba, an yaba musu kan bajintar da suka nuna a salon waƙarsu da kuma yadda suka rawarsu mai burgewa ta sa suka shahara a duniya daga yaran layi.
A watan Mayu ne fitattun mawaƙan Kenya Souti Sol na Kenya suka sanar da cewa za su rabu bayan shafe shekara 18 suna waƙa tare har ma za su fara wasu waƙoƙi a tare a matsayin na bankwana a ƙrshen shekarar nan.
Nigerian rising singer Oladips faked his death in November on social media for unexplained reasons. There were angry reactions from fans who had been mourning his death when he surfaced online one week later to say he was alive.
Fitaccen mawakin Nijeriya Oladips ya yi ƙaryar mutuwarsa a watan Nuwamba a shafukan sada zumunta saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba.
Mutanen da suka yi ta jimamin mutuwar tasa sun yi ta nuna fushi a lokacin da ya shiga intanet bayan mako guda ya ce yana raye.