Oladips ya ce zai faɗi nasa ɓangaren labarin nan gaba. Hoto:  Oladips      

Daga

Charles Mgbolu

Kimanin mako ɗaya bayan labarin mutuwar tauraron mawaƙin Nijeriya Oladips ya bayyana a kafafen sada zumunta, magoya baya suna jin wani sabon labari bayan mawaƙin ya fito ya ce yana raye.

Ranar 15 ga watan Nuwamba na shekarar 2023, magoya bayan mawaƙi mai tasowa, Oladipupo Oladimeji, wanda aka sani da sunansa na waƙa Oladips, suka ci karo da wani bidiyo a kafafen sada zumunta da yake nuna wasu abokansa guda biyu suna kururuwa a kan gawarsa, kuma suna roƙonsa da ya tashi.

Daga bisani masu kula da al'amuransa sun rubuta ɗan taƙaitaccen jawabi da ke tabbatar da cewa mawaƙin, ɗan shekara 28, ya mutu.

"Muna baƙin cikin sanar da jama'a cewa Oladipupo Olabode Oladimeji wanda aka fi sani da Oladips ya mutu jiya, ranar Talata,14 ga watan Nuwamba, da misalin ƙarfe 10:14 na dare. Har yanzu muna cikin kaɗuwa.

'Kai-Tsaye'

"Mutane sun ce wannan filta ce da dai sauransu, amma kamar yadda kuke gani, wannan Oladips ne kai-tsaye," ya faɗa a bidiyon da aka tura a shafinsa na kai-tsaye a Instagram da aka gudanar da yammacin Alhamis.

Ya ƙara da cewa zai mayar da martani kan tambayoyin da yake da yaƙinin za su biyo bayan wannan lamarin idan ya ji ya samu nutsuwa ta tunani da ta zuciya.

Labarin mutuwar da ake tunanin ya yi ya jawo bayyana alhini da yawa a kafafen sada zumunta, wanda ya zo babu jimawa bayan mutuwar wani tauraron da yake tashe sosai, Mohbad, wanda ya mutu cikin wani yanayi da ya jawo ce-ce-kuce a watan Satumba.

Yanzu labarin tashi daga mutuwa da Oladips ya yi ya kawo sa'ida sosai kuma ya jawo fushi.

"Shin wannan wasan banza ne ko mene ne?" wani magoyin baya mai suna Caleb ya tambaya a shafin X.

"Akwai bayanai masu yawa da za ka yi," wani mai suna Oluwaseun ya ƙara, shi ma a X.

Yin mutuwar ƙarya

Amma kuma, masana'antar mawaƙa ta Nijeriya ba baƙuwa ba ce wajen mawaƙa masu tasowa su yi ƙaryar mutuwarsu a matsayin wata dabarar neman shahara.

A shekarar 2015, Skibii, wani mawaƙin Nijeriya, sunansa ya fara zagayawa bayan labarin mutuwarsa ya bayyana a kafafen sada zumunta.

Skibii, a kare kansa, ya ce ya suma ne sakamakon wata cuta da yake fama da ita, abin da ya sa abokansa, suka ɗauka ya mutu.

Magoya baya, sun yi imanin cewa, mawaƙa masu tasowa, musamman, suna yin irin abu ne, don sunansu ya zama maudu'in tattaunawa a kafafen sada zumunta, don shahararsu ta ƙaru.

Kundin waƙoƙin Oladips na farko, mai taken "Super Hero Adugbo", an sake shi rana ɗaya bayan labarin mutuwarsa kuma yana ta shuhura da kuma sakawa a gidajen rediyo.

Sanarwar mutuwar tasa da kuma bidiyon abokansa masu kururuwa yanzu an goge shi a kafafen sada zumunta.

TRT Afrika