An ta jinjina wa mawakan kan irin wakar da suka yi ta gasar. / Hoto: Danny Synthe

Ana ci gaba da mayar da martani kyakkyawa kan bikin bude gasar kwallon kafa ta Afirka mafi girma AFCON 2023 musamman a shafukan sada zumunta, inda shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka Patrice Motsepe yake kiran lamarin da "wani abin kallo da ya hada dukkan kasashen Afirka."

Shahararriyar mawakiyar Nijeriya Yemi Alade wadda ta yi fice a wurin bikin, ta ce mafarki ne wanda ya tabbata.

"Tun daga 2016, na yi tunanin yin wasa a filin wasa don bukukuwan kwallon kafa wanda daruruwan ƴan rawa da jama'a suka kewaye.

"Bayan shekara bakwai, ga shi ina wasa a AFCON. Ba shakka abin girmamawa ne kuma mafarkina ne ya tabbata. Yanzu aka fara," kamar yadda ta bayyana a shafin X.

Wadanda suka shirya taron sun takaita bikin kan wakoki da rawar Afirka zalla, inda suke murna da Afirka da kwallon kafa.

Yemi Alade mawakiya ce ta Nijeriya wadda ta sha lashe kyaututtuka. / Hoto: Yemi Alade Instagram

Ƙaddamar da bikin bude taron ya kuma yi tasiri sosai a shafukan sada zumunta na masu wasan, inda dan wasan kwaikwayon nan kuma mawaki na Masar Mohamed Ramadan ya sanar da cewa shafinsa na YouTube an kalle shi sau biliyan 500.

Mohamed Ramadan wanda ya yi waka tare da Yemi Alade a 'Akwaba', wadda ita ce wakar gasar, inda suka yi ta tare da mawakin nan na Congo Danny Synthe.

"Afirka ta shirya," kamar yadda ya rubuta a shafin Facebook inda ya gode wa mabiyansa kan irin kuzarinda suka nuna tsawon lokacin wakar bude gasar.

A YouTube, tuni aka kalli Akwaba sama da sau miliyan biyar.

Ramadan ya ce sanar da gasar a shafinsa na sada zumunta ta jawo masa daukaka. / Hoto: Mohamed Ramadan

A karshen watan Disamba, Universal Music Africa, wadda a nan aka saki wakar ya ce akwai wakokin AFCON da yawa.

"Don mafi kyawun CAN, mun hada da kwararrun mawakaa 15 da kwararrun makada bakwai don kawo muku dabdala mafi kyau a nahiyar, '' kamar yadda kamfanin ya rubuta a Instagram.

A watan da ya gabata, an saki wasu wakoki na AFCON shida wadanda aka cikinsu akwai mawaka irin su Serge Beynaud da Kerozen da Josey da sauransu inda aka sake su a shafukan sauraren wakoki na intanet.

TRT Afrika