Sha'awar da Chinedu Mogbo ke da ita a kan halittu tun yana da ƙananan shekaru ce ta saka shi a tafarkin ceto dabbobin dawa daga hannun mutane.
"Na kalli fina-finan dabbobi, na ziyarci wajen ajiye namun daji, kuma na kama Tururuwa na saka su a kwalba," kamar yadda Mogbo ya tuno da ƙuruciyarsa.
"Tun ina ɗan ƙaramin yaro tsuntsaye da ƙadangaru da kuma ƙwari da ke kewayena suke ba ni sha'awa," Mogbo ya bayyana.
"Ina son kula da su," kamar yadda Mogbo wanda ke zaune a Legas babban birnin kasuwanci na Nijeriya ya faɗa wa TRT Afrika.
Mogbo ya yi karatu a fannin kiwon lafiya amma muradinsa na kan kula da kare dabbobin dawa.
Yana fita ya ceto dabbobin dawa da dabbobin gata da suka yi ɓatan kai ya kai su Green Fingers Sanctuary - wani gidan kula da dabbobi da ya kafa a Legas. Har ila yau, ana amfani da gidan a matsayin wata cibiyar ilimi.
Cibiyar na kula da dabbobi aƙalla 150 masu nau'o'in dabam dabam fiye da 40 har da su ɗankunya (pangolins).
Galibin dabbobin an ceto su ne daga yanayi mai hatsari, yayin da sauran aka kawo su musamman dan dalilai na ilimi.
Mogbo ya yi imanin cewa fahimta da sanin ƙimar dabbobin dawa yana da muhimmanci wajen tabbatar da halin sanin ya kamata ta fuskar tattala dabbobi.
"Idan na ga ana sayar da dabbobi domin a ci ko a ajiye a gida, ko domin yin maganin gargajiya ko tsafi, hakan na haddasa min fushi da ba zan iya kawar da kai ba," Mogbo ya ce.
Aikin ceto dabbobi a Nijeriya ba na masu raunin zuciya ba ne, Mogbo ya bayyana game da ƙalubalen da yake fuskanta.
Aikin ceton ya kai shi wurare daban-daban a ƙasarsa - a wani lokacin wurin dabbobin yawanci suke cikin hatsari sosai.
A gidan kula da dabbobi na Green Fingers Sanctuary, Mogbo na samar da dama ta biyu wa dabbobin da suka sha da ƙyar daga hannun mafarauta, da waɗanda suka rasa muhallansu saboda kutsen bil adama ko kuma suka rasa iyayensu.
"Muna ƙoƙarin samar da muhalli mai aminci da dabbobi za su yaɗu," ya jaddada, yayin da yake aiki ba ji ba gani domin kawo karshen tasirin rasa muhalli da kuma rikici tsakanin bil adama da dabbobin daji.
Mogbo ya yi nuni da mummunan sakamakon raguwar dabbobin dawa a Nijeriya, da ma wasu wuraren, yana bayar da misali da raguwar angulu a matsayin misali na zahiri.
Angulu, waɗanda sun taɓa zama masu muhimmanci wajen daidaita muhalli, an farauce su domin yin amfani da su wajen tsafin gargajiya da yin magunguna.
Raguwar yawansu ya taimaka wajen hatsarin kamuwa da cututtuka a cikin al'ummomi saboda aikin tsaftace muhalli da tsuntsaye ke yi.
Dogewar Mogbo kan tattala dabbobin daji ba ta tsaya kawai a kan ceto ɗaiɗaikun dabbobi ba.
Yana fatan ya zaburar da sabbin masu tattala dabbobi da masu kawo sauyi, waɗanda za su ci gaba da kare dabbobin dawan Nijeriya masu daraja.