Daga Kudra Maliro
A yankin Masarautar Dahomey da ke Yammacin Afirka, wato ƙasar Benin da Togo a yau, inda nan ne addinin gargajiya na voodoo ya samo asali, ana kallon lamarin a matsayin wata al'ada da ke nuna matsayin Afirka.
Kashi 12 cikin 100 na al'ummar Jamhuriyar Benin da ke da yawan mutum miliyan 13 ne suke gudanar da addinin Voodoo, a cewar wani ƙiyasi. Ƙungiyar tana da miliyoyin mabiya a wasu sassan duniya da suka haɗa da Brazil da Haiti da kuma Jihar Louisiana ta Amurka.
Ba a faye gaya wa mutanen waje labarin addinin Voodoo da ababen bautarsu ba, kuma a kan hana mabiya addinin ba da labaran tafarkin da suke kai.
"Addu'o'in addinin Voodoo ana yin su ne kai tsaye zuwa ga Ubangiji ta hanyar kakannin al'ummomin. Duk shekara muna shirya bukukuwan addini na Voodoo don kamun kafa da kakanninsu wajen nemar musu gafara," in ji Togbe Gnagblondro III, shugaban malaman addinan gargajiya na Togo, a hirarsa da TRT.
An fara sanin Voodoo ne a duniya tun a zamanin Cinikin Bayi a lokacin da ake tursasa wa bayin Afirka ta wajen fitar da su daga nahiyar. Sai dai kuma, an hana su damar gudanar da addinin.
Don kauce wa takunkuman, sai bayin suka fara daidaita allolinsu da malaman Cocin Katolika. Har ma suka fara gudanar da al'adun addinansu ta hanyar amfani da wasu alamu na Cocin Katolika.
Duk ran 10 ga watan Janairu, wasu al'ummar Jamhuriyar Benin kan kai gaisuwar ban girma ga allolin Voodoo a Ouidah, wani ƙaramin gari a gaɓar Tekun Atalantika wanda tsohuwar cibiyar cinikin bayi ce.
"Addinin gargajiya na Voodoo ya kasance wani bangare na al'adarmu ta Afirka a ko yaushe, tun daga lokacin kakanninmu har zuwa lokacin da Kiristanci da Musulunci suka shigo.
A tsawon shekaru, ƴan ƙasar Togo da dama sun fara komawa kan turbar addinin gargajiya na Voodoo,"Alphonse Logo, wani ɗan jarida ɗan ƙasar Togo, wanda ya sha ɗaukar rahoranni a lokutan bukukuwan addinin Voodoo, ya shaida wa TRT Afrika.
Ya ce mafi yawan mabiya Voodoo suna alfahari da yin addinin, inda suke bayyana shi a matsayin addinin gargajiya na Afirka.
"Ina tsoron wannan addinin, saboda idan ka yi alkawarin yin wani yanka don zubar da jinin dabba, kuma ba ka yi ba, to wani mugun abu zai faru da kai a rayuwa," Mr Logo ya ƙara da cewa.