Shahararren mawaƙin nan na ƙasar Tanzania Diamond Platnumz da mawaƙin nan kuma marubucin waƙa na ƙasar Maroko, Dystinct na daga cikin waɗanda ke kan gaba wajen nishaɗantarwa a taron bayar da kyaututtuka na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka CAF.
CAF ta ce bikin bayar da kyautar gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa na Afirka wanda za a gudanar a ranar Litinin da dare (16 ga Disamba), ba wai zai haska gwarazan 'yan wasa da koci-koci da ƙungiyoyi na nahiyar kawai ba, amma za a samu damar samun nishaɗi da jin sauti.
Diamond Platnumz wanda aka san shi da salon kiɗansa na Bongo Flava da Afrobeat, a ranar Lahadi ya sanar da cewa zai yi wasa a yayin bikin bayar da kyautar gwarzon ɗan ƙwallon na Afirka.
Diamond mai shekara 35, ya yi fice a faɗin duniya a matsayinsa na mawaƙi da marubucin waƙa da kuma ɗan kasuwa wanda kuma shi ne ya ƙirƙiro kuma yake shugabantar WCB Wasafi Record Label haka kuma yana daga cikin mawaƙan Afirka na farko-farko da suka samu masu kallo miliyan 900 a shafin YouTube.
CAF, a wata sanarwa a ranar Lahadi ta ce Diamond zai yi wasa a wurin taron tare da Dystinct, wanda aka sani da gauraya R&B da Afrobeat da Larabci a cikin waƙoƙinsa.
Dystinct ya samu kyaututtuka da dama daga kundin waƙoƙinsa da ya yi guda biyu waɗanda suka haɗa da Mon Yoyage (2021) da kuma Layali (2023), haka kuma ya haɗa kai da wasu manyan mawaƙa waɗanda suka haɗa da na Faransa Franglish.
Haka kuma ƙungiyar nan ta mawaƙa mata su uku na Women in Jazz, da kuma wata 'yar rawa wato Nakach.
Masu takara
A karshen taron, za a bayar da kyautuka 15 ga fitattun ‘yan wasa, masu horarwa, kungiyoyi, da kungiyoyin kwallon kafa na kasashen Afirka da suka yi fice a bana.
But who are the top contenders for the coveted male and female player awards?
Gwarzon Ɗan Wasan Shekara
Waɗanda ke takarar sun haɗa da Ronwen Williams (Afirka ta Kudu), Simon Adingra (Ivory Coast), Serhou Guirassy (Guinea), Achraf Hakimi (Morocco), da Ademola Lookman (Nijeriya). Wanda ya lashe kyauta a bara shi ne Victor Osimhen daga Nijeriya.
Gwarzuwar 'Yar Wasar Shekara
'Yan takara uku su ne Sanâa Mssoudy (Morocco), Chiamaka Nnadozie (Nijeriya), da Barbra Banda (Zambia). Asisat Oshoala daga Nijeriya ce ta lashe kyautar a 2023.
Bikin na wannan shekara zai gudana a Palais des Congrès a birnin Marrakech, Morocco, inda za a fara da ƙarfe 19:00, cewar CAF.
Kate Scott da Jamal Bouzrara ne za stari baƙi, kuma ana sa ran ganin ƙayataccen bikin da za a fitar da 'yan wasan Afirka mafiya ƙayatarwa a shekaran nan.