Dr. Masango ta kasance wacce aka sani a duniya kuma mace ta farko a Afirka da ta fara gudanar da gwaje-gwaje a dakin gwaje-gwajen kimiyyar fiziks mafi girma a duniya.

Yayin da duniya ke bikin Ranar Mata da 'Yan Mata a Fannin Kimiya ta Duniya ta 2025 a ranar 11 ga watan Fabrairu, Afirka ta Kudu ta yi alhinin rashin wata masaniyar kimiyya, Senamile Masango.

Masango, bakar fata mace ta farko a kasar mai ilimin kimiyyar nukiliya, ta rasu a asibiti tana da shekaru 37 a ranar Lahadi 9 ga watan Fabrairu. Har yanzu ba a bayyana musabbabin mutuwarta ba.

Ta kasance “babbar abar koyi ga matasa da yawa, musamman mata,” in ji mataimakin shugaban Afirka ta Kudu Paul Mashatile a cikin bayanin karramawar da ya yi mata.

An san manyan nasarorin da Masago ta samu a duk duniya, inda mataimakin shugaban kasar ya yaba mata kan "share hanya ga al'ummomi masu zuwa."

Ta kasance tana kararun digirin-digirgir, kuma masaniyar kimiyyar nukiliya, jagorar makamashi, sannan ƙwararriyar 'yar kasuwa.

Dakta Masango ita ce mace ta farko a Afirka da ta fara gudanar da gwaje-gwaje a CERN, Ƙungiyar Turai don Binciken Nukiliya. Ta lashe manyan kyaututtuka kamar lambar yabo ta Mata a Kimiyya a 2022.

"Za a samu babban giɓi kan sha'awarta ta haɓaka ƙwarewa mai muhimmanci a tsakanin jama'a da mata a kimiyya … muna so mu isar da ta'aziyyarmu ga dangin Masango, da jama'arta na kusa, da kuma fannin kimiyya gaba ɗaya. Allah ya sa ranta ya huta cikin aminci na har abada,” in ji mataimakin shugaban kasar Mashatile.

Masango ta kuma kasance 'yar kasuwa wadda ta kafa kamfanin tuntuɓar makamashi na Mphatisithele Consulting, kuma ta yi aiki a ƙungiyoyin kimiyya daban-daban na jama'a, gami da Kamfanin Makamashin Nukiliya na Afirka ta Kudu (NECSA) da Majalisar Raya Albarkatu.

Har ila yau, Ministan Kimiyya da Fasaha, da Ƙirƙira, Farfesa Blade Nzimande, ya yabi Masango, yana bayyana ta a matsayin "matashiya mai basira, kuma mai kishin ilimin kimiyyar nukiliya wadda ta yi wa ƙasarmu hidima da yin zarra."

“Rasuwarta wani babban rashi ne da ba wai kawai ya shafi ‘yan'uwanta ba ne, har ma ya haifar da gurbi mai zurfi a cikin al’ummar kimiyya da al’ummarmu baki daya,” in ji Sarkin Zulu, Misuzulu Sinqobile kaZwelithini, a cikin karramawar da ya yi wa marigayiyar masaniyar kimiyya.

An haife ta a Nongoma, KwaZulu-Natal, kuma Dokta Masango tana sha'awar kimiyya tun tana karama.

"Saboda launin fatata, ba tare da la'akari da shekaru 20-da na 'yanci ba, dole ne ku fara tabbatarwa da kanku - cewa za ku iya yin shi (aikin) kuma ku kasance a nan," kamar yadda ta taɓa faɗa.

Duk da cewa ana fuskantar wariya, Masango, a hirar da aka yi da ita, ta ce ta ci gaba da jajircewa wajen ƙarfafa wa mata da ‘yan mata a fannin kimiyya.

"Ina da shekara 11, malamina na darasin labarin kasa (geography) ya yi magana game da 'yan sama jannati, wanda hakan ya haifar da sha'awar kimiyya a tsawon rayuwa," ta tuna abin da ta taɓa faɗa a wata hira da Global Citizen. "A lokacin ne na kamu da son kimiyya."

Ta kaddamar da kungiyar Mata a Kimiyya a Afirka ta Kudu a cikin 2014 kuma ta kasance jagora a shirin Mata a Kimiyya da Injiniya a Afirka (WISE Africa).

TRT Afrika