Ana ta aika saƙon ta'aziyya dangane da rasuwar mawaƙin gambarar nan na Afirka ta Kudu, Malome Vector wanda ya rasu sakamakon hatsarin mota a ranar Laraba da rana.
Malome, wanda sunansa na asali shi ne Bokang Moleli, na kan hanyarsa ta zuwa Lesotho a lokacin da motar da yake ciki ta ci karo da wata babbar motar, kamar yadda iyalinsa suka tabbatar.
An sanar da rasuwar Malome da wasu mutum biyu a wurin da hatsarin motar ya faru.
"Ya kasance ɗa mai son mutane. Ya gudanar da duka rayuwarsa a masana'antar nishaɗi tare da yi mana waƙoƙin da muke so sosai," kamar yadda iyalinsa suka bayyana a wata sanarwa da suka fitar.
Akwai sauran masu ruwa da tsaki a harkar nishaɗantarwa da su ma suka yi ta'aziyya game da rasuwar mawaƙin.
"Yanayin yadda kake waƙa da tasirinka zai kasance tsawon lokaci. Ka kwanta cikin aminci," kamar yadda Spotify Africa ya rubuta a shafin X.
"Cikin rashin jin daɗi, muna ta'aziyya game da rasuwar wata fitila mai haskakawa, Zakin Lesotho ya kwanta dama. Muna miƙa ta'aziyyarmu ga masoyansa da abokan kamfaninsa na Ambitiouz Entertainment ya bayyana a shafinsa na X.
Malome ɗan shekara 32, ya yi suna bayan ya yi wata waƙa shi kaɗai mai suna "Dumelang" wadda ya saki a 2019, wadda ta yi suna a Afirka ta Kudu.
Sunan da ya yi a ƙasar ya ƙaru bayan da ya ci kyautar mawaƙa ta Afirka ta Kudu a rukunin wanda bidiyon waƙarsa ya fi kyau a 2021, inda ya yi waƙar tare da Miss Pru da Blaq Diamond.