Daga Firmain Eric Mbadinga
Daga garin Lome na Yammacin Afirka, zuwa Ouagadougou, daga Ouga zuwa Abidjan da Mali, sunan Karim la Joie sananne ne ga kowa a 'yan watannin nan.
Matashin dan kasar Burkina Faso na yada farin ciki da sanya dariya a kasashen Yammacin Afirka da ke magana da yaren Faransanci, madalla ga C'est qui lui? (Waye wannan) jerin bidiyo da zuwa da sabbin zango da ake yada su a shafukan sada zumunta.
Jarumin bidiyon da Karim yake wakilta, wani dan aksar Burkina Faso ne wanda ya manta dukkan wani abu game da Afirka, makonni biyu kawai bayan dawo wa daga Faransa.
Dawowar Karim ta sanya shi fara kokarin sake saba wa da jama'arsa, ya na tambayar: Waye wannan? a duk lokacinda ya wuce ta wani waje da iyayensa ko abokansa.
Kari kan abinda wasu ke wa kallon na rashin girmama talakawa, hali da dabi'ar Karim tun bayan dawowarsa daga kasar waje ya sauya sosai ta yadda mutum guda d abai manta da shi ba ne yake yi masa rakiya, wato Raoul Kara.
Karim kwararren jarumi, bari da mu yi tambayar da ta zama dabi'arsa; "Waye Karim?"
Sunansa na asali shi ne Karim Ouedraogo. Bidiyon da yake yi na zolaya ne ko nuna halayyar "Mbenguiste" - sunan da ake fada wa 'yan Afirka da suka dawo daga Faransa - wadanda suke jin su wasu ne bayan yin rayuwa a kasar waje.
"Ni ne Karim la hoie, matashin mai wasan barkwanci. tsohon dalibi mai sha'awar wasan ban dariya, barkwanci da sana'ar shirya fina-finai, da ma kaunar kida da waka. A takaice dai, Ni mai kaunar harkokin nan ne." in ji Karim la joie yayin dayake tattaunawa da TRT Afirka.
Matashin mai sha'awar kwallon kafa, wanda a koyaushe yake da sha'awar zurfafa karatu, ya amince cewar tun yana karamin yaro ya kasance mai iya bayyana kansa a koyaushe.
Yada farin ciki da samar da yanayi na jin dadi ba abu ne sabo gare shi ba, abu ne da ya saba da shi.
Bayan kammala jami'a, matashin dan kasar Burkina Faso ya rungumi baiwarsa ta barkwanci da kakaci. Sai a karshen 2023 ne basirar Karim a matsayinsa na mai rubuta labari da bayar da umarni ta fito fili karara a fagen barkwanci da kakaci.
Daga wani bidiyon zuwa wani, wasannin nasa na kara inganta sosai, kuma yana samun mutane miliyoyi da ke kallon sa a kowacce rana.
A watan Mayun 2024 ne ya samu bunkasa a shafukan sada zumunta, bayan ya saki wani bidiyo mai taken ''C'est qui lui?/Quand tu fais deux semaines en France''.
Tare da wani takalminsa kafa waje da faffadan kirjinsa yana kwambo, Karim la joie ya zama kalubalen matasa a shafukan sada zumunta, har ta kai ga wasu ma sun fara kwaikwayon tafiyarsa.
A daya daga cikin bidiyon d aya fitar, inda Karim la joie na tafiya yana kwambo hannayensa a bude, sai wani matashi ya tambaye shi ko ba shi da lafiya ne shi ya sa yake bokarewa haka.
Karim ya bayar da amsa ta hanyar da ya saba: "Waye wannan? ... Ni ba na musu da 'yan kwadago."
Wani mai bibiyarsa Nene Yousouf Sow daga Guinea ya yi kwamen da cewa: "Na kalli bidiyon sama da sau goma".
Ya ce "Mun san mutanen da ke da halayya irin wannan na cikin bidiyon. Wasun su ba sa son ganin tsaffin abokansu ko danginsu ko su koma unguwanninsu na asali. Komai ya sauya a wajensu."
A takaice dai, dubunnan mutane ne ke bayyana ra'ayoyinsu mau kyau da karfafa gwiwa game da ayyukan Karim.
"Komai ya koma zinare ga wadannan 'Mbenguists' din. Sakon da barkwanci na ke kokarin aike wa shi ne kar ka manta da asalinka (Duk irin sauyin arzikin da ka samu)," in ji Karim.
Mutum mai ibada, Karim ya bayyana godiyarsa ga Allah kan yadda jama'a suka karbi sakon da yake yada wa, kuma ya kudiri aniyar yin bidiyo da dama a nan gaba.
"A baya, ba a san ni sosai a shafukan sada zumunta ba. Hakan sai ya zama kamar a nuwa muke zaune. Na yi bidiyo daban-daban masu dauke da sakonni mabambanta, amma a lokacinda na fara sakin su a yanar gizo, sai na kara samun kwarewa." in ji Karim.
Ga masu aikin daukar bidiyon, wannan ne lokacin yaba wa da kyautata musu. Baya da Raoul Kaya da Trong Boy, abokan Karim sun hada da Safi Safi, Kama Kama da Rebeca.
Domin samun damar dawwamar da nasarar da suke samu, tare da girmama gayyatar da ake yi masa na yin wasa, Karim ya san yadda yake amfani da basirarsa da hada kai da abokansa.
"Za a ce na kasnace ina aiki tare da jaruman na tsawon lokaci. Mun san juna tuntuni, kuma tare da mai karsashi iri na, sai muka zama iyali guda."
"Da dogaro kan rubutaccen bayanin bidiyo, ina iya ba wa kowa rawar da zai taka, a kungiyance, muna kokarin samar da bidiyo d amutane ke yaba musu. Muna kara samun kware wa da ci gaba kuma a kan wannan turbar muke ci gaba da tafiya." in ji Karim.
Game da nauyin da ke kan sana'ar tasa, Karim ya ce zai ci gaba da samar da bidiyo da zia dinga faranta wa masu kallon sa.
"Ko da nasara da shuhura za su dinga amo, har yanzu muna bukatar gamsar da masu bibiyar mu tare da faranta musu da sabbin bidiyon da za su zo a nan gaba, wannan na da muhimmanci." Karim ya fada wa TRT Afirka.
A wannan lokaci, Karim da 'yan tawagarsa sun je kasashen Afirkada suka hada da Cote dIvoire da Togo, da ma wasu wuraren da dama.